"Sabuwar Kungiyar Ta'addanci Za Ta Fara Aiki a Najeriya," An Gargadi Bola Tinubu

"Sabuwar Kungiyar Ta'addanci Za Ta Fara Aiki a Najeriya," An Gargadi Bola Tinubu

  • Primate Elijah Ayodele ya yi ikirarin cewa nan da wata hudu masu zuwa wata sabuwar kungiyar ta’addanci na shirin fara aiki a Najeriya
  • Malamin cocin ya gargadi gwamnatin Bola Tinubu da ta dauki matakin gaggawa domin dakile matsalar tsaro da garkuwa da mutane
  • Ayodele ya ce matsalar rashin tsaro na iya kara haddasa zanga-zanga da matsin lamba kan Gwamnatin tarayya idan ba a dauki mataki ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya gargadi Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu kan yiwuwar sake samun sabuwar barazanar tsaro a Najeriya.

Babban malamin addinin Kiristan ya yi wannan gargadin ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar.

Primate Ayodele ya gargadi Tinubu kan bullar sabuwar kungiyar ta'addanci.
Primate Ayodele, shugaban cocin INRI Evengelical Spiritual (hagu) da Shugaba Bola Tinubu (dama). Hoto: @primate_ayodele, @officialABAT
Source: Facebook

Primate Ayodele ya hango matsalar tsaro

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi martani da Janar Rabe Abubakar ya mutu a hannun 'yan bindiga

A cikin sanarwar, Ayodele ya yi ikirarin cewa akwai wata kungiyar ta’addanci da ke shirin fara aiki domin haddasa matsala ga gwamnatin Tinubu, in ji rahoton Tribune.

Ya bayyana cewa sabuwar kungiyar na iya fara ayyukanta cikin watanni uku zuwa hudu masu zuwa idan ba a dauki matakin gaggawa ba.

“Akwai wasu da ke shirin sake tada rikici domin raunana gwamnatin shugaban kasa. Dole ne gwamnati ta dauki wannan batu da muhimmanci,” in ji Ayodele.

Ya bukaci shugaban kasar da ya duba duk wata kafa da masu aikata laifi za su iya amfani da ita domin hana faruwar matsala a gaba.

Ayodele ya yi magana kan masu garkuwa

Malamin cocin ya kuma nuna damuwa kan yadda matsalar garkuwa da mutane da hare-haren tsaro ke ci gaba da karuwa a Najeriya.

A cewarsa, tun a bara ya yi gargadin cewa rashin tsaro zai zama daya daga cikin manyan kalubalen gwamnatin Tinubu, amma ba a dauki gargadin da muhimmanci ba.

Ya ce idan har matsalar ta ci gaba musamman batun sace dalibai a jihar Oyo, akwai yiwuwar kungiyoyi daban-daban su fara zanga-zanga.

Kara karanta wannan

Rana ta 3: Masu zanga zanga sun toshe titi mai muhimmanci a Abuja kan matsalar tsaro

“Mutane da dama sun fara gajiya da matsalar rashin tsaro. Akwai kungiyoyi da ke shirin yin zanga-zanga idan ba a ceto wadanda aka sace ba,” in ji Ayodele.
Primate Ayodele ya ce matsalar tsaro ta shafi kowa don haka akwai bukatar a dauki matakin gaggawa.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele na jawabi daga ofishinsa. Hoto: @primate_ayodele
Source: Facebook

‘Kowa na iya fadawa hannun masu garkuwa’

Ayodele ya kara da cewa matsalar rashin tsaro ba ta ware kowa ba, yana mai cewa hatta ‘yan siyasa da jami’an tsaro na iya fadawa hannun masu aikata laifi.

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa, faston ya a bukaci ‘yan Najeriya su kasance masu lura tare da bai wa hukumomin tsaro hadin kai domin dakile matsalar.

A cewarsa, akwai yiwuwar masu aikata laifi su fara amfani da hanyoyin ruwa wajen gudanar da hare-hare nan gaba.

Ya kuma bayyana cewa kafa ‘yan sandan jihohi kadai ba zai wadatar ba wajen kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya.

Ayodele ya hango matsala a zaben 2027

A wani labari, mun ruwaito cewa, Primate Elijah Babatunde Ayodele ya gargaɗi Bola Tinubu ya tashi tsaye domin daƙile rikicin siyasa.

Malamin ya yi wannan gargaɗin ne a lokacin da yake hasashen abin da zai iya faruwa a zaben shugaban ƙasa mai zuwa a 2027.

A wani faifan bidiyo, Ayodele ya ce matukar Tinubu da muƙarrabansa suka gaza yin abin da ya dace, za su fuskanci ƙalubale a zaɓe.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com