Kai Tsaye: Sakamakon Zaben Fitar da Gwanin APC tsakanin Tinubu da Osifor Ya Fara Fitowa
Delta ya fado hannun Tinubu
Rahoton Punch ya bayyana cewa Bola Tinubu ya samu nasara mai rinjaye sosai a Delta a zaben tsaida 'dan takarar shugaban kasa.
Mai girma gwamnan Delta, Rt. Hon. Sheriff Oborevwori ya sanar da cewa cikin 'yan APC 407,815 da ake da su a, 407,646 sun kada kuri'a.
Oborevwori ya ce Mr Stanley Osifo bai da kuri'a ko daya a mazabu 270 da aka yi zabe a jihar.
Tinubu ya lallasa Osifo a Gombe
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu nasarar lashe zaben fitar da gwani na shugaban kasa a jihar Gombe.
@Imranmuhdz ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya samu kuri'u 450,517 yayin da abokin hamayyarsa Stanley Osifo, bai samu kuri'a ko daya ba.
Tinubu ya samu nasara a Delta
Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, wanda ya yi aiki a matsayin jami'an tattara sakamako na zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a jihar, ya sanar da cewa Shugaba Tinubu ne ya lashe zaɓen.
Ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya samu mafi yawan kuri'u a zaben fitar da gwanin, kamar yadda @imranmuhdz ya sanya a shafin X.
Shugaba Tinubu: Kuri'u 407,646
Stanley Osifo: 0
Tinubu ya samu gagarumar nasara a Kwara
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu gagarumar nasara a zaben fidda gwani na takarar shugaban kasar APC da aka gudanar a Jihar Kwara.
Ya samu kuri'u 310,990 inda ya doke babban mai kalubalantarss guda daya tilo, Stanley Osifo, wanda bai sami ko kuri'a daya ba.
Gwamna AbdulRahman AbdulRazaq, wanda ya kasance jami'in tattara sakamakon zabe na jiha, ne ya bayyana sakamakon a Ilorin, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
AbdulRazaq ya bayyana cewa jimillar mambobin APC 457,374 ne aka yi wa rajista, yayin da mambobi 310,990 aka tantance kuma suka shiga cikin tsarin kada kuri'a a fadin jihar.
Tinubu ya tika Osifor da kasa a Bayelsa
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar APC da aka gudanar a jihar Bayelsa yau Asabar, 23 ga watan Mayu, 2026.
Shugaban kwamitin zabe na Bayelsa kuma gwamna mai ci, Doye Diri ne ya sanar da hakan bayan kammala tattara sakamako, kamar yadda Nigerian Affairs ta wallafa.
Sakamakon Bayelsa
Bola Ahmed Tinubu - 277,192
Stanley Osifo - 5
Tinubu Ya Samu Kuri’a 131,096 a Jihar Edo
Shugaba Bola Tinubu ya samu kuri'u 131,096 a zaben fitar da gwani na shugaban kasa na jam'iyyar APC da aka gudanar a fadin mazabu 192 na jihar Edo a ranar Asabar.
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, wanda shi ne babban jami'in tattara sakamakon zaben, ya bayyana cewa zaben ya gudana cikin lumana, inda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi rinjaye da tazarar kuri'u masu yawa.
A cewar Okpebholo, Tinubu ya samu kuri'u 131,096, yayin da mai kalubalantarsa, Stanley Osifo, ya samu kuri'a 1 kacal a daukacin mazabu na Jihar Edo.
Tinubu ya yi nasara a mazabar Stanley Osifo
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu gagarumar nasara a kan Stanley Osifo a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da ya gudana a mazaɓa ta 9 ta Ute-Okpu, da ke Ƙaramar Hukumar Ika ta Arewa-Maso-Gabas a Jihar Delta.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa mambobin jam'iyyar APC sun fito kwansu da kwarkwata sun yi zabe a mazabar a yau Asabar.
Zaben APC: Tinubu ya yi nasara a jihar Zamfara
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya bayyana shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a matsyain wanda ya lashe zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa.
Gwamnan, wanda shi ne shugaban kwamitin tattara sakamako ya sanar da hakan ne a wani faifan bidiyo da Imran Muhammad ya wallafa a X
Sakamakon da aka bayyana ya nuna cewa Tinubu ya samu ƙuri’u 321,579, yayin da abokin takararsa, Stanley Osifo, ya samu ƙuri’u 42 kacal.
Sakamakon zaben fitar da gwanin APC a Zamfara
Shugaba Bola Ahmed Tinubu - 321,579
Stanley Osifo - 42