Gwanna Alia Ya Tika Mutum 2 da Kasa, Ya Lashe Tikitin Takarar Gwamnan APC a Zaben 2027
- APC ta bayyana Gwamna Hyacinth Alia a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da dan takarar gwamnan jihar Benuwai a zaben 2027
- Gwamna Alia ya samu nasara da gagarumin rinjaye a sakamakon a kwamitin zaben ya sanar bayan kammala kada kuri'u ranar Alhamis
- Da yake jawabi bayan samun nasarar, Alia ya gode wa ‘ya’yan jam’iyyar APC, masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar bisa abin da ya kira gagarumin goyon baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Benue, Nigeria - Gwamnan Jihar Benuwai, Hyacinth Alia, ya zama ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen 2027 da ke tafe.
Hakan ya biyo bayan gagarumar nasarar da Gwamna Alia ya samu a zaben fitar da gwanin da jam'iyyar APC ta gudanar a jihar Benuwai.

Source: Facebook
Gwamna Alia ya samu tikitin APC
Sakamakon zaɓen kato bayan kato da aka sanar a Makurdi ranar Alhamis ya nuna cewa Alia ya samu ƙuri’u 367,786, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Hakan ya ba shi damar doke abokan takararsa mafi kusa, Jeffrey Kuranun da Terwase Orbunde, waɗanda suka samu ƙuri’u 2,923 da 3,247 bi da bi.
Shugaban kwamitin zaɓen fitar da gwani na gwamna da Majalisar Dokokin Jiha na APC a Benuwai, Kabir Isah, ya bayyana zaɓen a matsayin wanda aka gudanar cikin lumana da gaskiya.
Ya ayyana Gwamna Alia a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan samun mafi yawan ƙuri’un da aka kaɗa.
Gwamna Alia ya yi jawabin godiya
Da yake magana bayan samun nasarar, Alia ya gode wa ‘ya’yan jam’iyyar APC, masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar bisa abin da ya kira gagarumin goyon baya, amincewa da haɗin kai.
Ya ce:
“Ina kara gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa ba mu damar yi wa al’ummar Jihar Benuwai hidima.”
Alia ya kuma yabawa sauran ‘yan takarar da suka shiga zaɓen, yana mai cewa hakan ya nuna yadda ‘ya’yan jam’iyyar APC ke da ƙwarin gwiwa ga gwamnatinsa da kuma buƙatar ci gaba.
Gwamnan Benuwai ya yabi Shugaba Tinubu
Hakazalika, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, shugabannin APC na ƙasa bisa amincewa da tsarin zaɓen kai tsaye, yana mai cewa tsarin ya bai wa ‘ya’yan jam’iyya damar zaɓar ‘yan takararsu cikin ‘yanci.
Gwamnan ya danganta amincewar da aka nuna masa da zuba jari da gwamnatinsa ta yi a fannonin lafiya, ilimi, hanyoyi da kuma ɗaukar malamai aiki, cewar tashar Channels tv.

Source: Facebook
Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da fifita jin daɗin talakawa tare da kira ga ‘ya’yan jam’iyyar su ci gaba da haɗa kai gabanin babban zaɓen 2027.
APC ta tsaida dan takara a Gombe
A wani rahoton, kun ji cewa jam’iyyar APC ta bayyana Jamilu Ishiaku Gwamna a matsayin wanda ya lashe tikitin takarar gwamna a jihar Gombe.
APC ta sanar da hakan ne bayan kammala zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a faɗin ƙananan hukumomi 11 na jihar.
Jamilu Gwamna ya samu nasara ne bayan tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Pantami da Sanata Sa’idu Ahmed Alkali sun sanar da janyewa daga neman takara.
Asali: Legit.ng

