Matsala Ta Kunno Kai kan Ficewar Sheikh Pantami daga Jam'iyyar APC a Gombe
- An fara takaddama kan ficewar tsohon ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami daga APC kafin komawa jam'iyyar PDP
- Shugaban APC na mazabar Pantami ya ce ya karbi takardar ficewar Pantami daga jam'iyya mai mulki tun ranar 19 ga Mayu, 2026
- Jam'iyyar APC ta yi ikirarin cewa har yanzu babban malamin na cikin jerin mambobinta a tsarin hukumar INEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Rikici ya kunno kai a jam'iyyar APC ta jihar Gombe kan batun ficewar tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, daga jam'iyyar kafin komawarsa PDP.
Yayin da bangaren Pantami ke cewa ya mika takardar fita zaga APC kafin ya shiga PDP, wasu shugabannin APC daga mazabarsa a karamar hukumar Gombe sun ce bai bi ka'idar sauya sheka ba.

Source: Facebook
Isa Pantami ya mika takardar barin APC
Shugaban APC na mazabar Pantami, Alhaji Bala Galda, ya bayyana cewa shi da kansa ya karbi takardar murabus din Pantami, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.
A cewarsa, takardar na dauke da kwanan watan 19 ga Mayu, kuma ya sanya hannu da dangwala hannun amincewa a kanta tare da Mai ba APC shawara kan harkokin shari'a, Malam Babangida Gololo.
“Lokacin da Farfesa Pantami ya shiga PDP ya kuma samun tikitin takarar gwamna, APC ta karamar hukuma ta kira duka shugabannin mazabar Pantami, ta umarce mu da kada mu karɓi ko sanya hannu kan takardar ficewarsa daga jam'iyya.
"Na shaida musu cewa na riga na karbi takardar kuma na sanya hannu da yatsa tun ranar 19 ga Mayu, saboda babu wata doka da ta tilasta mani sanar da shugabannin jam'iyya idan wani memba ya yanke shawarar ficewa," in ji Galda.
Makircin da aka shiryawa Pantami

Kara karanta wannan
"Duk shiri ne," Babachir Lawal ya sake tabo yadda ADC ta tsaida Atiku takara a zaben 2027
A rahoton Leadership, Bala Galda ya kuma yi zargin cewa shugabannin jam'iyyar sun bukace shi da ya musanta cewa ya karbi takardar murabus din tsohon ministan amma ya ki amincewa da hakan.
"Na gaya musu ba zan iya musanta abin da na san gaskiya ne ba, musamman ma da yake yatsana na kan takardar da ke hannun Farfesa Pantami."
Mai ba APC shawara kan harkokin shari'a a mazabar Pantami, Malam Babangida Gololo, ya ce babu wani tanadi a kundin tsarin APC da ya wajabta wa memba ya rubuta takardar murabus kafin shiga wata jam'iyya.
A cewarsa, shiga sabuwar jam'iyya shi kadai na nuna mutum ya fice daga tsohuwar jam'iyyarsa.
APC ta ce Pantami mambanta ne
Sai dai sakataren yada labarai na APC a jihar Gombe, Moses Kyari, ya ce jam'iyyar ta bukaci shugaban mazabar ya gabatar da kwafin takardar murabus din da aka amince da ita amma ya kasa yin hakan.
"Mun gayyace shi ya zo ya gabatar mana da ainihin takardar murabus din da Pantami ya bayar, amma ya ki amsa gayyata kuma ya daina amsa kiran jam'iyyar," in ji shi.

Source: Facebook
A cewar APC, har yanzu sunan Pantami na cikin jerin mambobin jam'iyyar a tsarin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC).
Kyari ya ce jam'iyyar ba ta hana Pantami ficewa ba, amma tana ganin dole ne ya bi hanyoyin da suka dace wajen yin murabus.
Farfesa Pantami ya samu karin goyon baya
A wani labarin, kun ji cewa tsohon ɗan takarar majalisar jihar Gombe, Hon. Mubarak Musa Dantori ya sauya sheka daga ADC zuwa PDP mai adawa.
'Dan siyasar ya bayyana cewa ya dauki wannan matakin ne domin komawa gidan siyasar dan takarar gwamnan Gombe na jam'iyyar PDP, Farfesa Isa Pantami.
Mutane da dama na ganin komawar Dantori zuwa layin Pantami za ta karawa tafiyar karfi duba da tasirin da ya ke da shi musamman a yankin mazabar Gombe ta Kudu.
Asali: Legit.ng

