Amaechi: Fastocin Takarar Shugaban Kasa na 'Dan Amanar Daura Sun Mamaye Katsina
- Magoya bayan tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi su fara tallata takarar shugaban kasar da yake nema a jam'iyyar ADC
- Rahotanni sun nuna cewa an lika fastocin Amaechi, wanda ke rike da sarautar Dan Amanar Daura a wurare daban-daban a cikin birnin Katsina
- Wani mamban ADC a Katsina, Kabir Abdullahi Dogo ya shaidawa Legit Hausa cewa a shirye yake ya zabi Amaechi idan jam'iyyarsu ta ba shi takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Katsina, Nigeria - Tsohon ministan sufuri kuma tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi na ci gaba da samun goyon baya a sassa daban-daban na kasar nan gabanin zaben 2027.
Faatocin takarar shugaban kasa da Amaechi ke nema a jam'iyyar hadaka ta ADC sun fara karade jihohin kasar nan, musamman a Arewa maso Yamma.

Source: Facebook
An lika fastocin Amaechi a cikin Katsina
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an wayi gari da fastocin Amaechi a unguwanni daban-daban a cikin birnin jihar Katsina.
Amaechi, na rike da sarautar 'Dan Amanar Daura, wanda Mai Martaba Sarkin Daura, Farouq Umar Farouq ya ba shi tun a lokacin mulkin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Rahotanni sun nuna cewa fastocin yakin neman shugaban ƙasa na jigon jam’iyyar ADC kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, sun bayyana a manyan sassan Jihar Katsina.
Amaechi na neman takara a ADC
Idan zaku iya tunawa tsohon ministan ya bayyana a gaban kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa na ADC kwanaki biyu da suka gabata.
Amaechi na neman tikitin takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar tare da ɗan kasuwa Mohammed Hayatudeen da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
An ga fastocin “Amaechi for President” a manyan titunan cikin birnin Katsina, ciki har da mahadar GRA roundabout, WTC roundabout, Kiddies roundabout da Gadar Sama ta Kofar Kaura da sauran wurare.
Majiyoyi sun bayyana cewa wata ƙungiyar magoya baya mai suna “Amaechi Ambassadors” ce ke da alhakin liƙa fastocin a jihar.

Kara karanta wannan
"Ana rasa abinci a gidana": Ministan Buhari, Amaechi ya magantu kan mulki a Najeriya

Source: Facebook
Amaechi na kara samun goyon baya
Wani mamban ADC a jihar Katsina, Kabir Abdullahi Dogo ya shaida wa Legit Hausa cewa yana yi wa Amaechi fatan alheri a zaben fitar da gwanin da za a yi nan kusa.
Ya ce dama Peter Obi ne kadai yake tunanin ba zai iya zaba ba a ADC, to amma yanzu tsohon gwamnan na jihar Anambra ya koma NDC.
Dogo ya ce:
"Amaechi dan gida ne a Katsina, kuma ni ina daga cikin wadanda za su zabi tsohon ministan idan ya sami tikicin ADC, mutum ne tsayayye kuma ina ganin zai iya mulkin Najeriya.
ADC ta shirya tsaida dan takara
A wani rahoton, kun ji cewa kwamitin tantance ‘yan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC ya tantance Atiku Abubakar, Rotimi Amaechi da Muhammed Hayatu-Deen.
Masu ruwa da tsaki na ci gaba da tattaunawa domin cimma matsaya tsakanin ‘yan takarar kafin zaben fitar da gwani na jam'iyyar da za a yi ranar 25 ga Mayu, 2026.
Manyan yan takara, Atiku da Amaechi sun amince da tsarin masalaha, to amma duk da haka idan ba a cikma matsaya ba, za a fita zaben fidda gwani.
Asali: Legit.ng
