"Na Fi Tinubu": Amaechi Ya Fadi Rawar da Ya Taka wajen Nasarar Buhari

"Na Fi Tinubu": Amaechi Ya Fadi Rawar da Ya Taka wajen Nasarar Buhari

  • Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya tuna baya kan nasarar da marigayi Muhammadu Buhari ya samu ta zama shugaban kasa
  • Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ba Shugaba Bola Tinubu ba ne ya sanya Buhari ya zama shugaban kasa ba a wancan lokacin
  • Tsohon Ministan ya nuna cewa ya yi fafatuka wadda ta kai ga samun nasarar da marigayi Buhari ya yi a zabe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Rivers kuma tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana rawar da ya taka wajen nasarar marigayi Muhammadu Buhari.

Amaechi ya bayyana cewa shi ne, ba Shugaba Bola Tinubu ba, ya taka muhimmiyar rawa wajen sanya marigayi Muhammadu Buhari zama shugaban ƙasa a shekarar 2015.

Amaechi ya ce ya taka rawa kan nasarar Buhari
Rotimi Amaechi, marigayi Muhammadu Buhari da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @ChibuikeAmaechi, @MBuhari, @aonanuga1956
Source: Twitter

Tsohon Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Juma'a, 22 ga watan Mayun 2026 a shirin Prime Time na tashar Arise News.

Kara karanta wannan

Amaechi: Fastocin takarar shugaban kasa na 'dan amanar Daura sun mamaye Katsina

Amaechi ya yi martani ga Tinubu

Amaechi, wanda a yanzu yake neman takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam'iyyar ADC ya maida martani ga iƙirarin da Tinubu ya daɗe yana yi.

A lokacin yakin neman zaɓensa na gabanin 2023, Tinubu ya ce Buhari ba zai zama shugaban ƙasa ba, ba tare da shi ba, kuma lokacinsa ne shi ma ya zama shugaban ƙasar.

Amaechi ya ce ya fi Tinubu aiki kan Buhari

Sai dai Amaechi ya bayyana cewa a matsayinsa na Minista mai ci a ƙarƙashin Buhari, ba zai iya ƙalubalantar iƙirarin Tinubu a bainar jama'a ba domin kada ya jefa muƙaminsa cikin haɗari.

“Lokacin da muka yanke shawarar kafa APC, lokacin da nake Minista, (Tinubu) yana iƙirarin cewa shi ya sanya Buhari zama shugaban ƙasa, kuma ba zan iya mayar da martani ba saboda ina minista a ƙarƙashin Shugaba Buhari. Yin hakan zai zama babbar wauta ne domin Buhari na iya korarka."
"Don haka ba zan iya cewa, ‘Kayi kuskure’ ba. Shi bai sanya Shugaba Buhari zama shugaban ƙasa ba. Ba wai kawai na kasance Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen ba, amma kowa zai shaida cewa na yi dukkan fafutukar."

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Kwankwaso ya yi martani kan zargin yana yi wa Tinubu aiki

“Na jagoranci kungiyar gwamnoni, na zagaya ƙasar nan ina fafutuka a nan da can domin nuna wa ’yan Najeriya cewa wannan shi ne lokacin sauyi.”

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya yi magana kan Tinubu
Rotimi Amaechi da shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @ChibuikeAmaechi, @aonanuga1956
Source: Twitter

Rotimi Amaechi ya yi aiki a matsayin Darakta Janar na yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Buhari a shekarun 2015 da 2019.

Amaechi bai son zama mataimakin Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rotimi Amaechi ya bayyana cewa bai sayi fam domin neman kujerar mataimakin shugaban kasa ba a zaben 2027.

Amaechi ya nuna rashin jin dadinsa kan rade-radin cewa zai iya zama abokin takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a karkashin inuwar jam’iyyar ADC.

Tsohon Ministan sufurin a gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari, ya yi martani mai zafi kan batun cewa zai iya zama mataimakin shugaban kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng