"Har da Talauci a ciki," Ministan Yar'Adua Ya Fadi Dalilin Shiga Takarar Gwamna a Akwa Ibom

"Har da Talauci a ciki," Ministan Yar'Adua Ya Fadi Dalilin Shiga Takarar Gwamna a Akwa Ibom

  • Tsohon ministan Abuja, John James Udoedehe, ya ce talauci da rashin aikin yi ne suka sa yake neman takarar gwamnan Akwa Ibom
  • Udoedehe ya zargi gwamnati mai ci a Akwa Ibom da kasa rage radadin rayuwa duk da dumbin kudaden da jihar ke samu daga tarayya
  • Dan takarar na jam'iyyar ADC ya bayyana cewa yana da kwarin gwiwar lashe zaben 2027 duk da cewa ya taba faduwa a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Akwa Ibom - Tsohon karamin ministan babban birnin tarayya Abuja, John James Udoedehe, ya ce karuwar talauci, rashin aikin yi a Akwa Ibom ne suka sa ya yanke shawarar neman kujerar gwamnan jihar a zaben 2027.

Udoedehe, wanda ke neman tikitin takara a jam’iyyar ADC, ya bayyana haka yayin wata tattaunawa da manema labarai a gidansa da ke Uyo ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

"Ka guji tarko": Sule Lamido ya shawarci Jonathan game da takarar shugaban kasa

Tsohon ministan Abuja ya bayyana dalilin shiga takarar gwamnan Akwa Ibom.
John James Udoedehe, tsohon ministan Abuja da yake takarar gwamnan Akwa Ibom. Hoto: Sitippe
Source: Facebook

“Talauci ya yi yawa a Akwa Ibom” - Udoedehe

Tsohon sakataren jam’iyyar APC na kasa ya nuna damuwa kan yadda matsin rayuwa ke kara tsananta a jihar duk da dimbin kudaden da gwamnati ke samu, in ji rahoton Punch.

A cewarsa, irin wahalar da jama’a ke ciki ce ke kara masa kwarin gwiwar shiga takara.

“Abin da yake bani karfin gwiwa shi ne idan na ga irin talauci, rashin daidaito da rashin aikin yi da ke addabar mutanen jihar nan. Na san dole ne a yi wani abu,” In ji Udoedehe.

Ya kara da cewa duk gwamnatin da ta kasa magance matsalolin talauci da rashin aikin yi ba ta fara aiki yadda ya kamata ba.

“Talauci ya yi yawa a Akwa Ibom. Za ka ga mutum mai shekaru 35 amma gashin kansa ya yi furfura saboda wahalar rayuwa."

- John James Udoedehe.

Udoedehe ya soki tsarin kashe kudin gwamnati

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya hakura da takara, ya janye daga zaben fitar da gwanin APC

Jaridar Leadership ta ruwaito Udoedehe ya ce ci gaban da ake gani a jihar bai dace da dumbin kudaden da gwamnati ke samu ba.

Ya bukaci a duba kasafin kudin jihar cikin shekaru biyu da suka gabata domin tantance ko kudaden suna amfanar jama’a yadda ya kamata.

A cewarsa, kudaden da tsoffin gwamnoni Godswill Akpabio da Udom Emmanuel suka samu cikin shekaru 16 ba su kai abin da Gwamna Umo Eno ya samu cikin shekaru uku ba.

John James Udoedehe ya ce Akwa Ibom na fama da talauci.
Jihar Akwa Ibom, inda tsohon minista, John James Udoedehe yake takarar gwamna. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'ADC za ta yi nasara' - Udoedehe

Mai neman takarar gwamnan ya bayyana cewa yana da yakinin jam’iyyar ADC za ta iya samun nasara a Akwa Ibom a zaben 2027.

Udoedehe, wanda ya yi minista daga 2007 zuwa 2008 ya kuma tunatar da jama’a cewa yana daga cikin wadanda suka kafa tsarin APC a jihar.

Udoedehe ya karyata zargin cewa ya shiga takara ne domin samun kudade daga wasu ‘yan siyasa. Ya bayyana irin wadannan zarge-zarge a matsayin bata suna da farfaganda.

Ana so gwamnan Akwa Ibom ya yi murabus

A wani labari, mun ruwaito cewa, jigon ADC a jihar Akwa Ibom, Sanata John Akpanudoedehe ya yi kira ga Gwamna Umo Eno ya yi murabus daga kujerarsa.

Kara karanta wannan

"Ku tashi tsaye ku kare kan ku daga ƴan bindiga," Hadimin Tinubu ga ƴan Najeriya

Tsohon sanatan ya yi wannan kira ne saboda yadda gwamnan ke nuna karfa-karfa a rikicin da ya barke kam mallakin wani daji a yankin Ekid.

Rahoto ya nuna cewa mazauna yankin sun yi zanga-zanga ranar Litinin, inda suka nuna adawa da yunkurin gwamnatin jihar Akwa Ibom.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com