"Ta Rasa Alkibla," Tsohon Gwamnan Ekiti Ya Hango Rikici a APC gabanin Zaben 2027

"Ta Rasa Alkibla," Tsohon Gwamnan Ekiti Ya Hango Rikici a APC gabanin Zaben 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya ce jam'iyyar APC ta kauce daga manufofin da aka kafa ta akai tun farko
  • Kayode Fayemi ya gargadi jam’iyyar cewa tsarin maslaha wajen fitar da ‘yan takara na iya haddasa rikici da rabuwar kai a APC
  • Dan siyasar ya ce hana ‘yan jam’iyya yin zabe cikin ‘yanci ne babbar barazana ce ga dimokuradiyya, wadda APC ke fama da ita

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya fito ya yi maganganu masu zafi game da jam'iyyar APC mai mulki yayin da ake tunkarar zabukan 2027.

Kayode Fayemi ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta kauce daga manufofi da akidojin da aka kafa ta a kai.

Tsohon gwamnan Ekiti ya ce APC na iya fuskantar rikici saboda zabukan fitar da gwani.
Kayode Fayemi, tsohon gwamnan Ekiti da ya hango rikici a jam'iyyar APC. Hoto: @kfayemi
Source: Twitter

“Jam’iyyar APC ta rasa alkiblarta” - Fayemi

Kara karanta wannan

"Har da talauci a ciki," Ministan Yar'Adua ya fadi dalilin shiga takarar gwamna a Akwa Ibom

Fayemi ya bayyana haka yayin wata hira a shirin State Affairs, wanda Edmund Obilo ke gabatarwa, inda ya nuna damuwa kan yadda ake gudanar da harkokin cikin gida na jam’iyyar.

Ya ce rashin tattaunawa da bin tsarin dimokuradiyya a APC na kara haddasa matsaloli cikin jam'iyyar musamman a lokacin zabukan fitar da gwani.

A cewar Fayemi, tsarin maslaha wajen zabar ‘yan takara ba matsala ba ne idan dukkan bangarori sun amince da shi.

Sai dai ya ce matsala tana tasowa ne idan tsarin ya hana ‘yan jam’iyya damar zabar wanda suke so cikin ‘yanci.

“Na fada karara cewa wannan ba ita ce turbar da aka dora jam’iyyar tun asali ba. Mun rasa alkiblarmu kuma mun kauce daga hangen nesan wadanda suka kafa APC,” in ji Fayemi.

Fayemi ne ya kakaba magajinsa a Ekiti?

Tsohon gwamnan ya kuma musanta zargin cewa ya tilasta wa wani zama gwamnan Ekiti bayan karewar wa’adinsa, in ji rahoton Daily Trust.

Ya ce gwamnan jihar na yanzu ya fito ne ta hanyar sahihin zaben fitar da gwani da wasu ‘yan takara shida suka fafata a ciki.

Kara karanta wannan

Tsohon dan acaba da ya zama ɗan majalisa ya rasa takara bayan ya koma APC

A cewar tsohon gwamnan:

“Ban dora kowa ba. An gudanar da zaben fitar da gwani a jihata kuma gwamnan yanzu ya fafata da akalla mutum shida ya yi nasara a kan su."

Fayemi ya ce nuna goyon baya ga wanda mutum yake so a siyasa ba laifi ba ne muddin ba a hana sauran mutane hakkinsu na dimokuradiyya ba.

Kayode Fayemi ya ce jam'iyyar APC ta kauce daga manufofin da aka gina ta a kai.
Kayode Fayemi, tsohon gwamnan jihar Ekiti. Hoto: @kfayemi
Source: Twitter

Tsohon gwamna ya hango rikici a APC

Da aka tambaye shi kan yadda wasu manyan mutane ke yanke muhimman shawara a APC su kadai, Fayemi ya yarda cewa wannan babban abu ne da zai haddasa rikici a APC.

Tsohon gwamnan ya jaddada cewa dukkanin wadanda suka nemi takara a APC, amma aka ware aka nada wani da sunan maslaha, za su kullaci jam'iyyar ne kawai.

Fayemi ya jefa tambaya:

“Ka san hatsarin daukar maganar mutum daya kawai? Me kake tunanin zai faru da masu neman takarar da aka ki ba su damar fafata wa a kato bayan kato? Kana tunanin za su yi farin ciki?”

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu Alkali ya bi sahun Pantami, ya janye daga takarar gwamna a Gombe

Lokacin da aka tambaye shi ko hakan na iya haddasa rarrabuwar kai a APC, Fayemi ya amsa da cewa, “Eh, hakan za ta iya faruwa, lokaci ne kawai zai nuna”

Shugaban APC ya gana da Tinubu

A wani labari, mun ruwaito cewa, APC ta bayyana yakinin cewa za ta warware duk wasu matsaloli da rikice-rikicen da suka biyo bayan zabukan fitar da gwani.

Shugaban APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ne ya bayyana hakan jim kadan bayan ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a Legas.

Ana ci gaba da samun sabani da rigingimun tsakanin masu neman takara a inuwar APC, inda wasu ke nuna fushinsu a fili kan tsarin masalaha.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com