Rundunar Sojin Najeriya Ta Dauki Matakin Farko bayan Mutuwar Janar Rabe a Katsina

Rundunar Sojin Najeriya Ta Dauki Matakin Farko bayan Mutuwar Janar Rabe a Katsina

  • Rundunar sojoji ta kaddamar da 'Operation Clean Sweep III' domin fatattakar ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a Matazu da wasu yankunan Katsina
  • Sabon samamen ya biyo bayan mutuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya a hannun ‘yan bindiga bayan sace shi da aka yi da matarsa
  • Hedikwatar tsaro ta ce sojoji sun lalata maboyar ‘yan ta’adda da cibiyoyin ajiyar kayan aikinsu a yankunan Dikkawa, Adua da Karaduwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Katsina - Rundunar sojojin hadin gwiwa a Arewa maso Yamma karkashin Operation Fansan Yamma ta kaddamar da wani sabon farmaki mai suna Operation Clean Sweep III domin yaki da ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda a Katsina.

A wata sanarwa da jami’in yada labarai na rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar ranar Litinin, ya bayyana cewa an fara wannan farmakin ne tun ranar 14 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Abubuwan sani game da Manjo Janar Rabe Abubakar da ya mutu a hannun 'yan bindiga

Sojoji sun kaddamar da farmakin Operation Clean Sweep III a Katsina.
Sojojin Najeriya a bakin aiki. Hoto: @ZagazOlaMakama
Source: Twitter

Farmakin soji bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar

Sanarwar ta ce manufar sabon samamen ita ce gano da kuma fatattakar wadanda ke da hannu a hare-hare da ta’addanci a karamar hukumar Matazu da sauran yankunan da ke makwabtaka da ita, in ji rahoton Channels TV.

Sabon matakin ya biyo bayan mutuwar Janar Rabe Abubakar wanda aka sace tare da matarsa a hannun ‘yan bindiga a Katsina.

Gwamnatin jihar Katsina ta sanar a ranar Asabar cewa tsohon babban jami’in sojan ya rasu ne yayin da yake tsare a hannun maharan sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka hada da ciwon sukari da hawan jini.

An yi jana’izarsa ranar Lahadi da yamma a makabartar Gidan Dawa da ke kusa da gidansa a cikin birnin Katsina, inda jama’a da dama suka halarta.

Sojoji sun lalata maboyar ‘yan bindiga

Rundunar ta ce tun bayan fara Operation Clean Sweep III, jami’anta suka gudanar da samame bisa bayanan sirri da kuma bincike a wuraren da ake zargin maboyar ‘yan ta’adda ne.

Kara karanta wannan

Bincike: 'Yan bindiga ne suka mika gawar Janar Rabe hannu da hannu? Gaskiya ta fito

A cewar sanarwar, an samu nasarori musamman a yankunan tsaunukan Dikkawa da sauran ƙauyukan da ke kusa.

“Samamen da aka kai yankunan Adua, Nasarawa da Karaduwa ya kai ga gano da lalata maboyar ‘yan ta’adda, wuraren ajiye kayayyaki da sauran cibiyoyin da suke amfani da su,” in ji sanarwar.

Rundunar ta bayyana cewa hakan ya rage karfin ayyukan ‘yan bindigar a yankin.

Sojoji sun gano tare da lalata maboya da sansanonin 'yan ta'adda a Katsina.
Taswirar jihar Katsina, inda sojoji suka gudanar da samame kan 'yan bindiga. Hoto: Legit.ng
Source: Original

An nemi hadin kan jama’a

Punch ta ruwaito cewa sojojin sun ce suna gudanar da aikin tare da sauran hukumomin tsaro da kuma shugabannin al’umma domin tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Sun tabbatar wa mazauna Matazu da sauran yankuna cewa za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi tare da hana ‘yan bindiga samun damar gudanar da ayyukansu.

Rundunar ta kuma bukaci jama’a su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano maboyar masu aikata laifuka.

Janar Rabe ya mutu a hannun 'yan bindiga

Tun da fari, mun ruwaito cewa, Gwamnatin Katsina ta tabbatar da rasuwar tsohon Manjo Janar na rundunar sojojin Najeriya, Rabe Abubakar.

Kara karanta wannan

Atiku ya yi martani kan rasuwar Manjo Janar Rabe a hannun 'yan bindiga

Tsohon babban jami'in sojan ya rasu ne yayin da yake tsare hannun ‘yan bindiga sakamakon matsalolin ciwon sukari da hawan jini da yake fama da su.

Mai girma Gwamna Dikko Radda ya bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga jihar Katsina da Najeriya baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com