Tikitin Tinubu da Kashim: Malami Ya Gano Abin da Zai Kawo Karshen APC

Tikitin Tinubu da Kashim: Malami Ya Gano Abin da Zai Kawo Karshen APC

  • Fasto Elijah Ayodele ya yi gargadi ga Shugaba Bola Tinubu kan sake tsayawa takara da mataimakinsa, Kashim Shettima
  • Malamin ya ce tikitin Musulmi da Musulmi tsakanin Tinubu da Shettima a 2027 zai iya kawo ƙarshen jam’iyyar APC gaba ɗaya
  • Ayodele ya bayyana cewa sake tsayar da Shettima zai jawo adawa daga cikin gida da ƙasashen waje tare da rage wa APC damar lashe zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual, Primate Elijah Ayodele, ya yi hasashe kan abin da zai faru da APC a zaben 2027 da ake tunkara.

Ayodele ya bayyana cewa jam’iyyar APC za ta iya rugujewa idan Bola Tinubu da Kashim Shettima suka sake tsayawa tare a 2027.

Fasto ya gargadi tikitin Tinubu da Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima da Bola Tinubu. Hoto: Kashim Shettima, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa wajen yaɗa labarai, Osho Oluwatosin, ya fitar wanda Tribune ta samu.

Kara karanta wannan

'Mutumina ne': Peter Obi ya yi magana da ake zargin yana gujewa Atiku

'Adawar da tikitin Musulmi da Musulmi zai fuskanta'

Ayodele ya ce tikitin Musulmi da Musulmi zai fuskanci tsananin adawa daga gida da kuma wajen Najeriya.

Malamin ya bayyana cewa sake haɗa Tinubu da Shettima a tikiti ɗaya zai zama kuskuren siyasa mai girma wanda zai rage damar APC ta ci gaba da mulki.

Ya ce har wasu Musulmai da wasu masu ƙarfi a ƙasa za su yi adawa da wannan tikiti, lamarin da zai jawo matsin lamba daga gida da waje.

Matsalar da cire Shettima zai jawo wa Tinubu

Ayodele ya kuma bayyana cewa cire Shettima daga matsayin mataimakin shugaban ƙasa zai jawo wa Tinubu matsaloli masu yawa da bai yi tsammani ba.

Ya ce shugaban ƙasar zai shiga cikin ruɗani saboda duk matakin da zai ɗauka kan Shettima zai iya jawo masa babban ƙalubale a siyasance.

Faston ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta fara ne da kuskure tun lokacin da aka amince da tikitin Musulmi da Musulmi kafin zaɓen 2023, cewar Daily Post.

Kara karanta wannan

"Ta rasa alkibla," Tsohon gwamnan Ekiti ya hango rikici a APC gabanin zaben 2027

Fasto ya gargadi Tinubu kan daukar Shettima mataimaki
Babban Fasto a Najeriya, Elijah Ayodele. Hoto: Primate Elijah Ayodele.
Source: Facebook

Abin da zai taimaki shugaban kasa, Tinubu

Ayodele ya ce gyara wannan kuskure ba zai zama abu mai sauƙi ba, yana mai cewa Allah bai goyi bayan gwamnatin daga farko ba kafin ma a zo wannan lokaci.

Ya bayyana cewa matsalolin da gwamnatin ke fuskanta yanzu na daga cikin sakamakon wannan mataki, yana mai cewa shugaban ƙasa zai ci gaba da fuskantar ƙalubale.

A ƙarshe, Ayodele ya ce abin da kawai zai taimaki shugaban ƙasar shi ne rahamar Ubangiji saboda ƙalubalen siyasar da ke gabansa suna da yawa wanda sai ya dage kafin ya.fi ƙarfin haka.

Martanin wani dan APC kan zaben Tinubu, Shettima

Wani dan APC ya yi magana kan hasashen malamin inda ya ce ko a zaben 2023 ma an yi ta maganganu makamantan haka.

Sani Sabo ya bayyana cewa yana da karfin guiwar cewa gwamnatin Bola Tinubu za ta sake samun nasara a zaben 2027.

Fasto Ayodele ya shawarci Jonathan kan takara

Kara karanta wannan

An kawar da Fubara, na kusa da Wike ya samu tikitin takarar gwamna a Rivers

Mun ba ku labarin cewa Fasto Elijah Ayodele ya gargadi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan game da takarar zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Ayodele ya gargadi Jonathan da ya yi taka-tsantsan kan batun tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027 da ake tunkara a Najeriya.

Malamin cocin ya ce takarar Jonathan za ta girgiza APC tare da sauya tsarin siyasar Najeriya, amma ya nuna cewa tafiyar ba za ta kasance mai sauki ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.