Yadda Amaechi Yake Fuskantar Matsin Lamba kan Zama Abokin Takarar Atiku a ADC

Yadda Amaechi Yake Fuskantar Matsin Lamba kan Zama Abokin Takarar Atiku a ADC

  • Jam’iyyar ADC na duba Rotimi Amaechi a matsayin wanda zai zama abokin takarar Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
  • Majiyoyi sun ce yankin Kudu maso Kudu, inda Amaechi ya fito ne ake ganin zai fi kawo ƙuri’u ga tikitin haɗakar adawa a zaben mai zuwa
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ana jiran dawowar Atiku Abubakar daga ƙasashen waje kafin a sanar da abokin takarar tasa a hukumance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar ADC na dab da yanke shawarar zaɓen tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi, a matsayin wanda zai zama abokin takarar Atiku Abubakar a 2027.

Bayan kammala zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar, ana rahoto cewa manyan masu ruwa da tsaki sun amince cewa haɗa Atiku da Amaechi shi ne mafi dacewa da muradin ADC a fafatawar siyasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

Amaechi: Jam'iyyar ADC ta sanar da abokin takarar Atiku a zaben 2027

Jam'iyyar ADC ta nace cewa Rotimi Amaechi ne take so ya zama abokin takarar Atiku Abubakar.
Atiku Abubakar yana daga hannu ga masoyansa (hagu) da tambarin ADC (tsakiya) da Rotimi Amaechi (dama). Hoto: @atiku, @ADCNig
Source: Twitter

Ana so Amaechi ya zama mataimakin Atiku

Rahoton jaridar Daily Trust ya nuna cewa Atiku ya kai wa Amaechi ziyara jim kaɗan bayan zaɓen fitar da gwanin, inda aka ce ya nemi goyon bayansa don ci gaba da aiki tare a cikin jam’iyyar.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa ba za a sanar da wanda zai zama abokin takarar ba har sai Atiku ya dawo daga tafiyar da ya yi ƙasashen waje.

Cikin waɗanda ake so a ba matsayin akwai tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha, Sanata Austin Akobundu da kuma Cif Emeka Nwajuba.

Wata majiya ta ce Amaechi ne ke kan gaba, kuma shi ne ake ci gaba da tuntuba don ya amince da hakan saboda tasirinsa a siyasar Kudu maso Kudu da kuma gogewarsa a matakin ƙasa.

Majiyar ta ce kai tikitin mataimakin zuwa Kudu maso Kudu ne zai iya bai wa ADC dama mai kyau a zaɓen, musamman ganin cewa APC na da ɗan takara daga Kudu maso Yamma yayin da ADC na da ɗan takara daga Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Rahoto: Dalilin da ya sa Atiku ya 'zabi' Amaechi a matsayin abokin takararsa a 2027

Tasirin Amaechi a siyasar Najeriya

Rahotanni sun kuma danganta zaɓar Amaechi da rawar da ya taka a baya a matsayin shugaban yaƙin neman zaɓen Muhammadu Buhari a lokacin da yake APC.

Masu sharhi sun ce wannan tarihin na iya taimaka wa ADC wajen jawo wasu ‘yan siyasa da ke da saɓani da APC zuwa cikin haɗakar su.

An kuma bayyana cewa Amaechi yana da alaƙa mai ƙarfi da manyan ‘yan siyasa a sassa daban-daban na Najeriya, wanda ake ganin zai iya taimaka wa tikitin a zaɓe.

Rahoto ya nuna cewa jam'iyyar ADC ta yi kokari matuka wajen dinke barakar da ta taso mata bayan zaben fitar da gwani.
Jiga-jigan Adawa, ciki har da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Rotimi Amaechi, David Mark a wajen kaddamar da shugabannin ADC. Hoto: @atiku
Source: Facebook

Takaddama a cikin jam’iyyar ADC

A baya, bayan taron ‘yan adawa da aka yi a Ibadan, an ruwaito cewa Atiku ya fara duba yiwuwar zaɓen Gwamna Seyi Makinde a matsayin abokin takararsa.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa wannan shiri bai yi nasara ba, domin kuwa Makinde ya bayyana cewa zai tsaya takara a wata jam’iyya daban in ji rahoton Leadership.

Haka kuma, Amaechi da Muhammed Hayatu-Deen sun fafata da Atiku a zaɓen fitar da gwani na ADC, inda Atiku ya samu nasara.

Kara karanta wannan

1959 zuwa 2026: Lokuta 5 da Hausawa da Ibo suka haɗu a siyasance kafin tafiyar OK a NDC

Duk da cewa an samu rashin jituwa bayan sakamakon zaɓen fitar da gwani, rahotanni sun nuna cewa shugabannin jam’iyyar sun warware matsalolin cikin gida domin ci gaba da shirin zaɓen 2027.

Atiku ya 'amince' da zaben Amaechi

Tun da fari, mun ruwaito cewa, majiyoyi sun ce Atiku Abubakar ya amince da Rotimi Amaechi a matsayin abokin takararsa a jam’iyyar ADC kafin zaben 2027.

Majiyoyin sun bayyana cewa ADC ta zabi Amaechi saboda tasirinsa a siyasar Kudu maso Kudu da gogewarsa a gwamnatin tarayya.

Jam’iyyar ADC ta ce tana kokarin ganin cewa ta kauce wa rikicin cikin gida, irin wanda ya dabaibaye PDP dab da babban zaben 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com