Bincike: 'Yan Bindiga ne Suka Mika Gawar Janar Rabe Hannu da Hannu? Gaskiya Ta Fito
A karshen watan Mayu, 2026 ne wasu miyagun 'yan bindiga suka yi garkuwa da tsohon mai magana da yawun babbar hedkwatar sojojin Najeriya, Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya tare da matarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lamarin ya faru ne bayan yan bindiga sun farmake su a hanyar Marabar Musawa zuwa Kafinsoli da ke ƙaramar hukumar Matazu ta jihar Katsina, sai dai direbansu ya tsira da raunin harbi.

Source: Facebook
Tsohon babban jami'in sojin ya rasa ransa a hannun yan bindigar da suka yi garkuwa da shi bayan shafe fiye da kwanaki 10 a hannunsu, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
'Hoton' mika gawar Janar Rabe Abubakar
Bayan tabbatar da mutuwarsa, an fara yada wani hoto a kafafen safa zumunta fa ke nuna yadda 'yan bindiga suka mika wa wakilan da aka tura gawar marigayin hannu da hannu.

Kara karanta wannan
Yadda aka karbo gawar Manjo Janar Rabe Abubakar bayan ya rasu a hannun 'yan Bindiga
Hoton, wanda ya bazu a shafukan sada zumunta tare xa ikirarin nuna lokacin da ’yan bindiga suka miƙa gawar marigayi Manjo Janar Rabe ya janyo muhawara a tsakanin masu amfani da intanet.
An fara yaɗa hoton ne bayan Gwamnatin jihar Katsina ta sanar da mutuwar tsohon hafsan sojin a ranar 13 ga Yuni, 2026.

Source: Twitter
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na Katsina, Dr. Mu'azu Aliyu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamna, Ibrahima Kaulaha Mohmmed ya wallafa a Facebook.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an gudanar da jana’izar Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya) a Katsina bisa tsarin addinin Musulunci.
Abin da masu yaɗa hoton suka yi ikirari
Wasu shafuka da masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi iƙirarin cewa hoton ya nuna lokacin da ’yan bindiga suka kawo gawar marigayin sannan suka koma daji ba tare da an masu komai ba.
Wani shafin Facebook mai suna Native Reporters ya wallafa cewa:
”'Yan fashin daji dauke da manyan makamai sun mika gawar Janar Rabe a jiyan nan da safe a Katsina, kuma suka juya zuwa dajin Matazu ba tare da kowa ya kalubalance su ba! Har yanzu matar sa tana hannunsu.”
Haka zalika, wani mai amfani da dandalin X (wanda da aka fi sani da Twitter), @Tutsy22 (Adetutu Balogun), ya wallafa hoton tare da rubuta cewa:
”A cikin kasa mai cin gashin kanta, 'yan ta'adda sun yi garkuwa da Manjo Janar na soja, sun kashe shi, sun mika gawarsa sannan suka tafi abinsu ba tare da kowa ya masu komai ba.”
Haka kuma, @Laurestar (Lauretta Onochie) ma ta wallafa wannan hoto, inda ta rubuta:
”Madalla da aiki, Tinubu. 'Yan bindiga dauke da manyan makamai sun mika gawar Janar Rabe a jiyan nan da safe a Katsina, kuma suka juya zuwa dajin Matazu ba tare da kowa ya kalubalance su ba! Babu wani hukunci da aka dauka. Wace irin kasa ce wannan?"
Bincike ya gano alamun AI a hoton
Sai dai rahoton Daily Trust ya nuna cewa binciken da aka gudanar ta amfani da fasahar Open Source Intelligence (OSINT) ya nuna cewa babu wata hujja da ke tabbatar da cewa hoton na gaske ne.
Binciken gano hotunan da aka ƙirƙira ta hanyar fasahar AI ya nuna cewa akwai yiwuwar kashi 46.6 cikin 100 na cewa an samar da hoton ne da na’urar kirkirar hoto ta AI.
An kuma gano matsaloli a fuska, siffar jiki, makamai da tufafin mutanen da ke cikin hoton, abubuwan da ake yawan gani a hotunan da AI ke ƙirƙira.
Shin hukumomin sun fitar da hoton?
Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoto, babu wata hukuma ta gwamnati, jami'an tsaro ko kafar yada labarai mai sahihanci da ta wallafa hoton a matsayin hoton gaske daga wurin da lamarin ya faru.
Rahotannin hukumomi sun kuma nuna cewa wasu bayanan da aka haɗa da hoton ba su dace da bayanan da aka tabbatar ba.
Binciken ya tabbatar da cewa hoton da ake yaɗawa ba sahihin hoto ba ne daga lamarin mutuwar Janar Rabe Abubakar.

Source: Facebook
Hukuncin karshe da aka yanke
Duk da cewa wasu masu yaɗa hoton sun bayyana cewa AI ce ta ƙirƙire shi, rashin sanya wannan bayani kai tsaye a jikin hoton ya sa yana iya ruɗar mutane su ɗauka cewa hoto ne na ainihin abin da ya faru.
Don haka, hoton da ake ikirarin yana nuna lokacin da ’yan bindiga suka miƙa gawar Janar Rabe Abubakar ba gaskiya ba ne, kuma yaudara ce da za ta iya rikitar da masu kallo da bibiya.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun kutsa fadar sarki da dare, sun bindige matarsa bayan garkuwa da shi
An sako matar Manjo Janar Rabe?
Kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa har yanzu Hajiya Amina Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, tana hannun ’yan bindiga.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin kubutar da Hajiya Amina, amma sun ƙi bayyana cikakken bayani ko lokacin da ake sa ran samun nasara a aikin.
Hakan dai na zuwa ne bayan an tabbatar da mutuwar mijinta, wanda suka shiga hannun masu garkuwa da mutane tare a jihar Katsina.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

