Bayan Kai Ruwa Rana, Jam'iyyar APC Ta Tsaida 'Dan Takarar Gwamnan Yobe a Zaben 2027
- Jam'iyyar APC ta ayyana tsohon sakataren gwamnatin jihar Yobe, Baba Malam Wali a matsayin dan takarar gwamna a zaben 2027
- Hakan ya biyo bayan nasarar da ya samu a zaman sulhun da kuma zaben fitar da gwani da APC ta gudanar a jihar Yobe
- Jihar Yobe na daya daga cikin jihohin da aka kai ruwa rana tsakanin masu neman takarar gwamna bayan zaman sulhun da aka gudanar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yobe, Nigeria - Tsohon Sakataren Gwamnatin Jihar Yobe (SSG), Alhaji Baba Malam Wali, ya lashe tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC gabanin zaɓen 2027.
An ayyana Malam Wali mai shekaru 68 a matsayin wanda ya lashe zaɓen fitar da gwani na gwamna da aka gudanar a fadin kananan hukumomin Yobe.

Source: Facebook
Sakamakon zaben fitar da gwanin APC

Kara karanta wannan
Gwanna Alia ya tika mutum 2 da kasa, ya lashe tikitin takarar gwamnan APC a zaben 2027
Rahoton Daily Trust ya tattaro cewa shugaban kwamitin zaben, Injiniya Muttaqah Rabe ne ya sanar da sakamakon kuri'un da aka kada Banquet Hall na gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu.
Ya ce an gudanar da zaɓen ne bisa tsarin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, ƙa’idojinta da kuma tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026.
Ya ce Malam Wali ya samu ƙuri’u 236,711 inda ya doke sauran masu neman takarar ciki har da Dr. Abubakar Bukar Kagu wanda ya samu ƙuri’u 9,748.
A cewarsa, Hon. Bashir Sheriff Machina ya samu ƙuri’u 1,894, yayin da Injiniya Mustapha Yunusa Maihaja ya samu ƙuri’u 1,178.
Darma ya ƙara da cewa Hamidu Alhaji Muhammad ya samu ƙuri’u 1,722, Inusa Muhammad ya samu 1,148, yayin da Ma’aji Modu ya samu ƙuri’u 1,371, kamar yadda Ounch ta kawo.
APC ta tsaida dan takarar gwamnan Yobe
Ya ce:
“Saboda haka ina ayyana Baba Malam Wali, bayan cika sharuddan kundin tsarin mulkin APC da ƙa’idojinta tare da samun mafi yawan ƙuri’u, a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Jihar Yobe.”
Wali, wanda ya fito daga Ƙaramar Hukumar Nguru a Yobe ta Arewa, ya zama ɗan takarar masala na APC bayan wani taron masu ruwa da tsaki, amma lamarin ya haifar da rikici a jam'iyya.

Source: Facebook
Masu bibiyar harkokin siyasa na ganin tsaida shi takara zai share hawayen masu buƙatar mika mulki zuwa Yobe ta Arewa, yankin da bai taɓa samar da gwamna ko mataimakin gwamna ba tun bayan ƙirƙirar jihar a 1991.
An haifi Wali a shekarar 1958, kuma ya yi karatu a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria (ABUl, inda ya samu digirin farko da na biyu.
Gwamna Alia ya lashe tikitin APC
An ji cewa APC ta bayyana Gwamna Hyacinth Alia a matsayin wanda ya lashe zaben fitar da dan takarar gwamnan jihar Benuwai a zaben 2027.
Sakamakon zaɓen kato bayan kato da aka sanar a Makurdi ranar Alhamis da ta gabata ya nuna cewa Alia ya samu ƙuri’u 367,786.
Da yake magana bayan samun nasarar, Alia ya gode wa ‘ya’yan jam’iyyar APC, masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar bisa goyon bayan da suka nuna masa.
Asali: Legit.ng
