Zaben 2027: Manyan Sarakuna 7 a Najeriya da Suka Fito Fili Suka Goyi bayan Bola Tinubu
Yayin da harkokin siyasa ke kara daukar zafi gabanin babban zaben Najeriya na 2027, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya samu goyon bayan wasu sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na kasar nan.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Manyan sarakuna da kungiyoyin masu rike da sarautun gargajiya daga sassa daban-daban na kasar sun fito sun nuna goyon baya ga tazarcen Bola Tinubu a zabe mai zuwa.

Source: Twitter
Rahoton Punch ya nuna cewa goyon bayan da wasu daga cikin sarakunan suka yi ta jawo hankali, musamman ganin yadda ake girmama su da kuma alakarsu da al'umma.
Wasu sarakunan sun bayyana goyon bayansu ne da kansu, yayin da wasu suka yi hakan a madadin kungiyoyin sarakuna.
Galibi dai suna bayyana ayyukan raya kasa, gine-ginen hanyoyi, manufofi, da kuma kyakkyawar alakar da ke tsakanin gwamnatin Tinubu da al'ummominsu a matsayin dalilinasu.
Legit Hausa ta tattaro muku wasu fitattun sarakunan gargajiya da aka ruwaito sun bayyana goyon bayansu ga neman wa'adin mulki na biyu na Shugaba Tinubu.
1. Sarkin Daura, Umar Faruq Umar
Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar, na daga cikin fitattun sarakuna na Arewa da suka bayyana goyon bayansu ga Shugaba Tinubu domin gabanin zaben 2027.
A watan Yulin 2025, rahotanni sun bayyana cewa Sarkin Daura ya nuna goyon bayansa ga Tinubu yayin da yake karbar wata tawaga karkashin jagorancin Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, a fadarsa da ke Daura, Jihar Katsina.
A cewar jaridar Premium Times, Sarkin ya nuna godiyarsa ga yadda Tinubu ya girmama marigayi tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, musamman yadda aka gudanar da jana'izarsa.

Source: Facebook
Bayan haka, Sarkin Daura ya ci gaba ada fitowa fili yana nuna goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a lokuta daban-daban.
2. Oba Rilwan Akiolu, Sarkin Legas
Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, na daga cikin manyan sarakunan da suka nuna goyon bayansu ga neman wa'adin mulki na biyu na Tinubu.

Kara karanta wannan
Tinubu na ganin ƴan adawa suka jefa ƙasa a halin ƙunci duk da matakan da ya ɗauka
A watan Satumban 2026, an ruwaito cewa Oba Akiolu ya bayyana goyon bayansa ga Shugaban Kasar yayin wata ziyara da tawagar masu yakin neman zaben Tinubu ta kai masa a fadarsa.
Rahoton The Cable ya bayyana cewa Sarkin ya nuna kwarin gwiwar Tinubu zai samu nasara a zaben 2027, inda ya bayyana cewa babu wanda zai maye gurbinsa a fadar shugaban kasa.

Source: Facebook
3. Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi
Oluwo na Iwo, Oba Abdulrosheed Akanbi, shi ma yana cikin fitattun sarakunan Kudu maso Yammacin Najeriya da suka bayyana goyon bayansu ga Tinubu.
A watan Mayun 2026, Akanbi ya jagoranci wasu sarakunan daga Osun ta Yamma wajen bayyana goyon bayansu ga shugaban kasar a wani taron manema labarai da aka gudanar a fadarsa da ke Iwo, Jihar Osun.
A cewar jaridar Vanguard, sarakunan sun ambaci ayyukan raya kasa da gwamnatin tarayya ke yi, musamman shirin sake gina hanyar Osogbo–Iwo–Ibadan, a matsayin daya daga cikin manyan dalilan goyon bayansu.

Source: Facebook
4. Shugaban Majalisar Sarakunan Akwa Ibom
A watan Janairun 2026, sarakunan gargajiya daga mazabar Ikot Ekpene sun taru a filin wasa na Ikot Ekpene, inda suka bayyana goyon bayansu ga Tinubu, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Gwamnan Akwa Ibom, Umo Eno.

Kara karanta wannan
Raddin da Jalo Jalingo ya yi wa sarakuna ya sa ya ji babu daɗi hannun ƴan Facebook
An bayyana goyon bayan ne a wani babban taro da ya samu halartar manyan sarakuna, shugabannin kabilu, shugabannin kauyuka, shugabannin iyalai da matansu.
Sarkin Abak kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Akwa Ibom, mai kartaba Akuku Udofia, ya bayyana cewa matsayar sarakunan ta samo asali ne daga abin da suka kira ayyukan shugabannin da kuma yadda suke gudanar da mulkinsu.

Source: Facebook
Sarakunan sun ambaci ayyukan more rayuwa, manufofin tattalin arziki da ayyukan raya kasa a matsayin wasu daga cikin dalilan goyon bayansu, kamar yadda Leadership ta kawo.
5. Sarkin Benin
Sarkin Benin a jihar Edo, Mai martaba Omo N’ Oba N’ Edo, Uku Akpolokpolo, (Ewuare II) ya bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu domin ya yi tazarce zuwa wa’adi na biyu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Sarkin ya bayyana matsayinsa ne yayin da Daraktan- Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa (PCC), Sanat Abdulaziz Yari, ya jagoranci tawaga zuwa Fadar Benin domin neman albarka da goyon bayansa ga Tinubu.

Source: Facebook
Sarkin Benin ya gode wa Tinubu bisa kyakkyawar tarbar da ya samu a lokacin ziyararsa da ta gabata a Fadar Shugaban Ƙasa, sannan ya yi wa Shugaban addu’ar samun wa’adi na biyu.
Ya ce bai kamata a sauya gwamnati kawai saboda son sauyi ba, yana mai cewa ya kamata a bai wa gwamnatin damar ci gaba da shirye-shiryenta.
Sai dai ya jaddada cewa Masarautar Benin ba ta da alaƙa da kowace jam’iyyar siyasa, kuma bai kamata a fassara matsayinsa a matsayin shiga wata jam’iyya ba.
6. Esu Sa'Rubochi, Ibrahim Mohammed Pada
Esu Sa'Rubochi, Alhaji Ibrahim Mohammed Pada, shi ma yana cikin sarakunan gargajiya a Babban Birnin Tarayya Abuja.da suka bayyana goyon bayansu ga Tinubu.
Pada ya bayyana matsayarsa ne yayin da yake karbar wakilan kungiyar FCT Renewed Hope Ambassadors a Rubochi, da ke karamar hukumar Kuje.
A cewar Voice of Nigeria, Sarkin ya yaba da abin da ya bayyana a matsayin ayyukan gwamnatin tarayya da ake gani a yankinsa.
Ya kuma bayyana goyon bayansa ga Tinubu da Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, tare da yin alkawarin amfani da tasirinsa wajen karfafa goyon bayan jama'a ga APC.
7. Gomon Kuje, Alhaji Haruna Jibrin
Gomon Kuje, Alhaji Haruna Jibrin, wanda ke Abuja, ya shiga jerin sarakuna da suka bayyana goyon bayansu ga neman wa'adin mulki na biyu na Tinubu.
A watan Disamban 2025, Jibrin ya bayyana goyon bayansa yayin da yake karbar wakilan kungiyar FCT Renewed Hope Ambassadors a fadarsa.

Source: Facebook
A cewar rahoton The Nation, Sarkin ya yaba da ayyukan da gwamnatin tarayya ta gudanar a Kuje, musamman inganta hanyoyin mota a yankin.
Haka kuma, Jibrin ya yi alkawarin wayar da kan jama'a domin su goyi bayan jam'iyyar APC a zabukan da ke tafe, ciki har da neman wa'adin mulki na biyu na Tinubu.
Tinubu ya roki alfarmar yan Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya roƙi ’yan Najeriya su sake ba shi wa’adi na biyu a 2027 domin ci gaba da ayyukan alherin da ya fara.
Ya buƙaci magoya bayansa su zaɓi APC a dukkan matakai, ciki har da shugaban ƙasa, gwamnonin jihohi, Majalisar Tarayya da majalisun dokokin jihohi.
Tinubu ya kuma yaba wa gwamnonin APC bisa abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarinsu na samar da ci gaba a jihohinsu.
Asali: Legit.ng


