Mutane Sama da 30 da Suka Taba Samun Lambar Yabon GCON a Tarihin Najeriya

Mutane Sama da 30 da Suka Taba Samun Lambar Yabon GCON a Tarihin Najeriya

  • Daga shekarar 1963 zuwa yau, Gwamnatin Najeriya ta raba babbar lambar karramawa ta GCON ga mutane sama da 30
  • Gwamnonin yankunan da aka yi a jamhuriyya ta farko suka fara samun lambar girmar a hannun shugaba Nnmadi Azikiwe
  • Ban da ‘yan Najeriya akwai mutane daga kasar waje da Shugaba Bola Tinubu da Ibrahim Babangida suka ba GCON

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lambar Grand Commander of the Order of the Niger (GCON), ita ce mafi girmar karramawa da mutum zai samu bayan GCFR a Najeriya.

Ita GCFR kuwa lamba ce da Mai girma shugaban kasa kuma shugaban dakarun Najeriya ko wani wanda ya yi zarra kadai yake amfani da ita.

Tarihin lambar GCON a Najeriya

Bayan Bola Ahmed Tinubu ya ba Wole Olanipekun lambar GCON, Legit Hausa ta tattaro sauran wadanda suka taba samun wannan karramawa.

A tarihi mutane fiye da 30 mu ka san cewa Mai girma shugaban kasa ya taba ba su lamba ta GCON.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba gawurtaccen lauya lambar yabo ta 2 a daraja da mutum zai iya samu

Daga shafin Wikipedia aka fahimci cewa kafin babban lauyan, akwai mutanen Najeriya da na kasar waje da suka taba samun wannan babbar lamba.

Takardun da aka samu daga shafin gwamnatin Najeriya sun nuna a shekarar 1963, Nnamdi Azikiwe ya fara bada lambar GCON a tarihin kasar.

Azikiwe ya bada lambobin ne ga tsofaffin gwamnonin yankuna da aka yi kafin a kifar da gwamnati.

Mutanen kasar waje da suke da lambar GCON

Business Day ta ce akwai mutane daga waje kamar Nelson Mandele, Muammar Gaddafi da Sarauniya Elizabeth da duk an taba ba su GCFR.

Ban da GCFR da gwamnatin Ibrahin Badamasi Babangida ta ba ta a 1989, tun a shekarar 1969 Sarauniya Elizabeth ta taba samun shaidar GCON.

A jerin akwai shugaban kasar Indiya da ‘dan kasuwa daga kasashen ketare da wasu ‘yan siyasa da suka taba rike shugabancin Majalisar tarayya.

Sai dai duk da Bukola Saraki ya shugabanci Majalisar dattawa daga 2015 zuwa 2019, Gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta ba shi lambar GCON ba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi hira da fitacciyar 'yar Amurka, za a saki bidiyon tattaunawar

Har ila yau akwai wasu fitattun ‘yan kasuwa da kimarsu ta kai sun tashi da lambar karramawar a baya, a cikinsu har da mai kudin nahiyar Afrika.

Shugabanni da manyan alkalai suna cikin jerin

Atiku Abubakar, Namadi Sambo, Yemi Osinbajo da Kashim Shettima suna da GCON a matsayinsu na mataimakan shugaban kasa daga 1999 zuwa yau.

Alkalan alkalan da suka samu su ne Adetokunbo Ademola, Olukayode Ariwoola, Dahiru Musdapher, Idris Kutigi da Ibrahim Tanko Muhammad.

Cikakken jerin masu lambar GCON a Najeriya

  1. Sir Francis Akanu Ibiam
  2. Alhaji Kasim Ibrahim
  3. Chief Joseph Odeleye Fadahunsi
  4. Queen Elizabeth
  5. Adetokunbo Ademola
  6. Amina J. Mohammed
  7. Anyim Pius Anyim
  8. Olukayode Ariwoola
  9. Atiku Abubakar
  10. Bello Maitama Yusuf
  11. Dahiru Musdapher
  12. Emeka Anyaoku
  13. Alex Ekwueme
  14. Aliko Dangote
  15. Godswill Akpabio
  16. Goodluck Jonathan
  17. Idris Legbo Kutigi
  18. Joseph Wayas
  19. Ibrahim Tanko Muhammad
  20. Kashim Shettima
  21. Mike Adenuga
  22. Mike Akhigbe
  23. Murtala Nyako
  24. Namadi Sambo
  25. Narendra Modi
  26. Ngozi Okonjo-Iweala
  27. Oba (Dr.) Sikiru Kayode Adetona
  28. Ahmad Lawan
  29. Siddiq Abubakar III
  30. Yemi Osinbajo
  31. Tajudeen Abbas
  32. Gilbert Chagoury
  33. Wole Olanipekun

Wole Olanipekun ya samu GCON a sunan shi

Labari ya zo cewa Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya ba Wole Olanipekun lambar yabo ta GCON da ake murnar cikarsa shekaru 50 yana aikin lauya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng