Kano, Borno da Jihohi 5 da Za Su Iya Fin Kowane Zuba wa Tinubu Kuri’u a Arewa

Kano, Borno da Jihohi 5 da Za Su Iya Fin Kowane Zuba wa Tinubu Kuri’u a Arewa

  • Kano da Borno na cikin jihohin da ake ganin Shugaba Bola Tinubu zai iya samun kuri'u masu yawa
  • A zaben shugaban kasa na 2023, APC ta samu kuri'u sama da 500, 000 a Kano da 252,282 a jihar Borno
  • Zamfara za ta ja hankali saboda nadin Abdulaziz Yari, a matsayin daraktan yakin neman zaben Tinubu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kano - Abba Kabir Yusuf ya zaburar da mutanen Kano su yi kokari wajen ganin a jihar su ne Bola Ahmed Tinubu ya ga ruwan kuri'u.

Gwamnan Kano yana so jiharsa ta zama wanda ta fi kowace ba jam’iyyar APC kuri’u a zaben shugaban kasa da za a yi a 2027.

Bola Tinubu da Kashim Shettima
Bola Tinubu da Kashim Shettima wajen yakin zaben Najeriya Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Yadda muka yi hasashen kuri'un Bola Tinubu

Legit Hausa ta yi hasashen jihohin Arewa da ake ganin daga gare su ne shugaba Bola Tinubu zai samu kuri’u mafi yawa.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna kuma shugaba a PDP ya tsumbula kafa a APC babu wanda ya ji labari

Abin da muka yi la’akari da shi, shi ne kuri’un da APC ta samu a 2023 da ‘yan siyasa masu farin jini da ake da su a jihohin.

Wani abin dubawa kuma zai zama karfin da jam’iyyun hamayya suke da shi a yankin na Arewa.

Jihohin Arewa da Tinubu zai ga kuri'u

1. Kano

Ba abin mamaki ba ne kuri’un Bola Tinubu a Kano su zarce na ko ina a Arewacin Najeriya saboda karfin APC a jihar.

Na farko dai shugaban kasar ya samu kuri’u fiye da 500, 000 a zaben 2023 kuma a yanzu Abba Kabir Yusuf ya shigo APC.

Baya ga haka, mutane rututu daga jihar Kano sun samu mukamai a gwamnatin tarayya baya ga tsohon shugaban APC.

Kano tana da miliyoyin masu katin zabe, sai da za a iya ganin tasirin NDC saboda takarar Rabiu Kwankwaso da Peter Obi.

2. Katsina

Muna sa jihar Katsina cikin jihohin da mu ke ganin za a zabi Tinubu duk da goyon bayan da Atiku Abubakar ya samu a 2023.

Kara karanta wannan

G100: Atiku, Peter Obi suna daf da tsaida ‘dan takara 1 da zai tunkari Tinubu

APC tana iya tashi da kuri’u masu yawa a jihar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari musamman saboda irinsu Ibrahim Masari.

Baya ga gwamna da sauran masu rike da mukamai, Hadimin shugaban kasar ya motsa kasa a Katsina duk da akwai rikicin gida.

A 2023 kuwa, dama mutane 480, 000 suka ba Tinubu kuri’arsu a Katsina, sai dai watakila adadin ba zai kai haka a zaben badi ba.

3. Zamfara

Ba abin mamaki ba ne alkaluma su canza a Zamfara wannan karo saboda nadin Abdulaziz Yari a matsayin Darekta janar.

Tsohon gwamnan Zamfara kuma sanata mai-ci ne ya ke jagorantar yakin zaben Tinubu kuma an san shi da farin jini a yankin.

Ban da Yari, shi kan shi Gwamna Dauda Lawal ba zai so shugaban kasa ya kunyata a Zamfara ba bayan sauya-shekarsa daga PDP.

Ko da Atiku Abubakar yana tashe, APC ta tara jiga-jigai a jihar irinsu Ministan tsaro, Bello Matawalle da Ahmad Yariman Bakura.

4. Kaduna

Mun kawo Kaduna a cikin wuraren da za a fito da tulin kuri’un Bola Tinubu saboda alakarsa da Mai girma Gwamna Uba Sani.

Kara karanta wannan

Mutuwar uwa, fadan ‘ya ‘yansa da abubuwa 10 da suka faru da El Rufai da yake tsare

Atiku Abubakar ne ya yi nasara a Kaduna a zaben da ya wuce, amma labarin zai iya canza wa wannan karo saboda karfin APC.

Jam’iyya mai-ci ta samu shiga a wajen mutanen Kudancin Kaduna a dalilin ayyuka da mukamai da canjin tikiti a zaben gwamna.

Uba Sani ya tarwatsa tsofaffin ‘yan APC da suka shiga ADC kuma za a dage wajen ganin bayan tsohon gwamna Nasir El-Rufai.

5. Borno

A Borno, Tinubu ya samu 54.22% na kuri'un da aka kada a zaben da ya wuce, ya doke Atiku Abubakar na PDP mai kuri'u 190,921.

Kasancewar Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, dan jihar ne, ba za a yi mamaki ba idan aka ga hobbasa a wannan karo.

An ta rade-radin Tinubu zai canza abokin gaminsa amma daga baya ya rike tikitin shi, Shettima zai so ya nuna ba a yi kuskure ba.

Amma duk yadda tsohon gwamnan zai so, halin tattalin arziki, tsaro, fitowar masu zabe da kuma karfin ‘yan adawa za su yi tasiri.

Tinubu
Taron kungiyoyin magoya bayan Bola Tinubu a Kano Hoto: Ibrahim Adam
Source: Facebook

Tituna da wasu ayyukan Bola Tinubu a Arewa

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Yadda Tinubu, Atiku da Peter Obi ke fafatawar neman nasara a jihohin Arewa 5

An ji labari cewa Cif Bayo Onanuga ya fitar da jerin tituna da aikin jirgin kasa da Bola Tinubu yake yi wa yankin Arewacin Najeriya.

Ban da karasa titin Abuja-Kaduna-Kano, akwai hanya da za a yi tun daga Sokoto har Legas da wasu tituna da za su kai har Filato.

Hadimin shugaban kasa ya rufe bakin ‘yan adawa da suke cewa ba su ci moriyar komai ba a shekaru uku da rabi da aka yi ana mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng