Tinubu na Ganin Ƴan Adawa Suka Jefa Ƙasa a Halin Ƙunci duk da Matakan da Ya Ɗauka

Tinubu na Ganin Ƴan Adawa Suka Jefa Ƙasa a Halin Ƙunci duk da Matakan da Ya Ɗauka

  • Shugaba Bola Tinubu ya zargi jam’iyyun adawa da haddasa yunwa da talauci a Najeriya, yayin da ya kaddamar da yakin neman zabensa a Kaduna
  • Tinubu ya kare cire tallafin man fetur, yana mai cewa hakan ya kawo karshen cin hanci, karya takardun biyan kudi da safarar mai
  • Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya ce Tinubu ya dade yana goyon bayan ’yan siyasar Arewa, ciki har da Atiku Abubakar da Muhammadu Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Shugaba Bola Tinubu ya zargi jam’iyyun adawa da haddasa yunwa da talauci a Najeriya yayin da ake shirin zabe.

Tinubu ya fadi hakan ne yayin mayar da martani kan sukar da ake yi wa gwamnatinsa game da yadda take tafiyar da tattalin arzikin kasar, yayin da ya kaddamar da yakin neman zabensa na wa’adi na biyu a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Tinubu na Kaduna, El Rufai ya jefa masa tambayoyi 12, ya tuna masa hadisin Manzo

Tinubu ya zargi yan adawa da lalata Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Kokarin da Tinubu ke yi a Najeriya

Da yake jawabi a wajen kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC na shekarar 2027 a Kaduna, Tinubu ya ce gwamnatinsa na kokarin kawar da matsalolin tattalin arziki da ake dangantawa da jam’iyyun adawa, cewar Channels TV.

Ya kuma yi wa magoya bayansa alkawarin samun wadata idan aka sake zabensa, yana mai tabbatar musu cewa ba za su yi nadamar sake ba shi wa’adi na biyu ba.

Ya ce:.

“Ina da hujja, ina jin abokan hamayyata suna magana kan yunwa da talauci. Wa ya haddasa su? Su ne suka haddasa su! Su ne suka haddasa yunwa, su ne suka haddasa talauci, mu kuma muna kokarin kawar da su.
“Muna biyan albashi a kan lokaci, gwamnoninmu suna aiki, kuma ina alfahari da su saboda suna kawo ci gaba. A gare ku yaran kasarmu, alkawarin wa’adi na biyu shi ne wadata; ba za ku yi nadamar zuwa kada kuri’a ba.”

Kara karanta wannan

Duk da fargaba a Kaduna, APC ta yi alƙawari ga Tinubu yayin da zai fara kamfen

Tinubu ya kare cire tallafin man fetur

Cire tallafin man fetur ya zama daya daga cikin manyan batutuwan da ake tattaunawa a kansu gabanin zaben shekarar 2027, inda wasu ’yan adawa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, suka yi alkawarin dawo da tallafin idan aka zabe su.

Sai dai Tinubu ya kare wannan mataki a wajen gangamin yakin neman zabensa a Kaduna, inda ya bukaci magoya bayansa su yi hattara da abin da ya kira ikirarin yaudara daga abokan hamayyarsa.

“Ku yi hankali, ku sa ido a kansu. Kada ku bari su yaudare ku. Abin da ya wuce ya wuce. Tallafin man fetur ya zama tarihi a gare mu. Babu sauran cin hanci da rashawa, babu sake kirkirar takardun biyan kudi na karya, babu karya, babu safarar man fetur."

- In ji shi.

Tinubu ya soki yan adawa a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Shettima ya magantu kan goyon bayan Tinubu ga Arewa

Da yake jawabi a wajen kaddamar da yakin neman zaben, Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya ce Tinubu ya dade yana goyon bayan shugabannin siyasar Arewa tsawon shekaru.

Kara karanta wannan

Rokon da gwamnatin tarayya ta yi wa Atiku kan takararsa da Tinubu a zaben 2027

Shettima ya kawo misalan goyon bayan da Tinubu ya bai wa Atiku Abubakar a shekarar 2007, Nuhu Ribadu a shekarar 2011, da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a zabukan shekarun 2015 da 2019.

Ya ce:.

“A shekarar 2011, Asiwaju ya goyi bayan wani dan Arewa, Nuhu Ribadu, sannan a shekarun 2015 da 2019, ya goyi bayan marigayi Shugaban Kasa Muhammadu Buhari."

Uba Sani ya yi wa Tinubu alƙawari

Mun kawo muku rahoton cewa Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce al’ummar Arewa za su saka wa Shugaba Bola Tinubu da ƙuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Uba Sani ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori wajen gine-gine, tsaro, ilimi da noma, ciki har da ayyukan hanyoyi da sake buɗe makarantu.

Gwamnan ya buƙaci ’yan Arewa su auna Tinubu bisa ayyukansa, ba ƙabilanci ko yankin da ya fito ba, tare da gargaɗin APC kan amfani da AI.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.