Matsalar Tsaro: An Yi Hasashen Abin da Mutanen Jihohi 22 Za Su Yi Wa Tinubu a Zaben 2027

Matsalar Tsaro: An Yi Hasashen Abin da Mutanen Jihohi 22 Za Su Yi Wa Tinubu a Zaben 2027

  • Kungiyar ’yan Najeriya mazauna kasashen waje (NDMG), reshen Birtaniya, ta yaba wa gwamnatin Tinubu kan kokarin yaki da matsalar tsaro
  • Kungiyar ta yi hasashen cewa jam'iyyar APC da Shugaba Tinubu za su lashe zabe a jihohi 22 a babban zaben 2027
  • NDMG ta ce nasarorin da sojoji suka samu wajen ceto mutane da tarwatsa sansanonin ’yan ta’adda sun taimaka wajen hasashen nata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kungiyar ’Yan Najeriya Mazauna Kasashen Waje (NDMG), reshen Birtaniya, ta yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan kokarin inganta tsaro a Najeriya.

Kungiyar ta yi hasashen cewa jam’iyyar APC za ta lashe zabe a jihohi 22 a babban zaben 2027 saboda kokarin jami'an tsaro a fagen yaki da ta'addanci.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a wurin yakin neman zaben APC Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

A rahoton Leadershi, NDMG ta ce hasashen nata ya biyo bayan nazari mai kyau kan halin da kasar ke ciki, musamman yadda rundunar sojin Najeriya ke yaki da ta’addanci, garkuwa da mutane da sauran barazanar tsaro.

Kara karanta wannan

APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu

A cikin wata sanarwa da ta fitar yau Alhamis, NDMG karkashin jagorancin Dr Philip Idaewor, ta yaba wa babban hafsan tsaron kasa, Janar Olufemi Oluyede, da shugabannin rundunar soji bisa gagarumin ci gaba a yaki da rashin tsaro.

Kungiyar ta ce nasarorin da sojoji suka samu a baya-bayan nan sun nuna sabunta kudurin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Ta kara da cewa gwamnatin Tinubu ta cancanci yabo bisa ci gaban da aka samu a karkashin jagorancinta.

“Idan za a yi nazari na gaskiya kan gwamnatin Tinubu, dole ne a yi la’akari da ci gaban da ake samu a bangaren tsaro. Rundunar soji ta ci gaba da nuna jarumtaka, kwarewa da jajircewa wajen fuskantar barazanar tsaron kasarmu.

"Muna yabawa babban hafsan tsaron kasa, Janar Olufemi Oluyede, da daukacin shugabannin soji bisa sadaukarwar da suke yi da kuma sakamakon da ake samu.

"Kokarinsu na da matukar muhimmanci wajen dawo da amincewar jama’a da tabbatar da cewa ’yan Najeriya za su iya rayuwa da gudanar da sana’o’insu ba tare da tsoro ba,” in ji kungiyar.

Kara karanta wannan

"Alamu da lissafin siyasa sun nuna wanda zai lashe zaɓen shugaban ƙasa a 2027"

NDMG ta yi nuni da wasu hare-haren soji na baya-bayan nan da suka kai ga kubutar da mutane 125 da aka yi garkuwa da su, rusa sansanonin ’yan ta’adda, kwato makamai da kuma gano tare da kakkabe bama-bamai.

A cewar rundunar soji, ayyukan da aka gudanar tsakanin 6 zuwa 12 ga Nuwamba sun kuma sa ’yan ta’adda 12 da iyalansu suka mika wuya.

Hukumar kula da harkokin Afirka ta ma’aikatar harkokin wajen Amurka (US Bureau of African Affairs) ita ma ta yaba wa sojojin Najeriya kan wadannan ayyuka, inda ta bayyana ceto mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma rusa sansanonin ’yan ta’adda a matsayin manyan nasarori.

Kungiyar ta ce irin wannan bajinta da sojoji suka nuna na daga cikin muhimman abubuwan da suka yi la’akari da su wajen hasashen cewa APC za ta lashe zabe a jihohi 22 a shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262