Kwankwaso Ya Ziyarci Yari da Labaran Karya da Suka Yi Ta Yawo a Makon da Ya Wuce
- Labaran karya marasa tushe suna ta kara yawo musamman a fagen siyasa yanzu da aka buga gangar kamfe
- An samu labaran karya da aka kirkiro domin rudar da magoya baya da kuma na bata wasu ‘yan siyasa a kasar
- Akwai tsofaffin bidiyoyi da yanzu suke yawo a shafukan sada zumunta matsayin sababbi saboda muguwar manufa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Nigeria - Har kullum mukan bibiyi labarai na karya marasa tushe da mutane suka rika yada wa da gangan ko da rashin sani.
Wannan karo ma mun tattaro labaran bogi da suka shahara, sai dai bincike ya nuna sam babu wani kanshin gaskiya a cikinsu.

Source: Facebook
Wasu labaran bogi da suka yi yawo
Labaran bogin da Legit Hausa ta samu a kwanakin nan sun kunshi furofagandar yakar APC inda aka fake da sunan tsohon minista.
1. INEC da batun 'yan takara a wasu jihohi
Hotunan karya sun rika yawo ana cewa hukumar zabe ta INEC ta ce za ta dawo da sunayen mwasu masu neman takarar gwamna.
Bayanan bogin da aka samu sun nuna lamarin zai shafi jihohi shida da aka taba takaran jam’iyyun hamayya irinsu PDP da NDC.
Da farko musamman magoya bayan irinsu Isa Ali Pantami sun rika murna kafin INEC ta karyata labarin a wata sanarwa a X.
Jihohin da ake magana a kai su ne Zamfara, Gombe, Delta, Plateau, Yobe da kuma Kano.
2. Haduwar Rabiu Kwankwaso da Abdulaziz Yari
Wasu a shafukan sada zumunta sun dawo da wani hoton ganawar Abdulaziz Yari da Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa a Abuja.
Daga shafukan Sanata Kwankwaso a Facebook muka gano an yi ganawar ne a Mayun 2023 lokacin da Yari yake harin shugabancin majalisa.
Masu yada hoton sun yi ikirarin kwanan nan aka yi zaman, suna cewa hakan ya tabbatar da tsohon gwamnan yana tare da APC a boye.
3. Adawar APC wajen Adebayo Adelabu
Wani bidiyo da Legit Hausa ta gani a shafin X ya yi ikirarin Adebayo Adelabu ya fito yana fada wa jama’a su kaurace wa jam’iyyar APC.
Tsohon ministan na makamashi ya ce ba a yi haka ba, an dawo da bidiyon wata hira da aka yi da shi ne tun yana jam’iyyar Accord a 2022.
Punch ta ce ofishin yada labaran Adelabu mai harin zama gwamnan Oyo ya karyata labarin da aka samu daga wajen @dangbanamanager a X.
4. Atiku Abubakar zai yaki ‘yan shi’a
A irin wadannan labarai na kanzon kurege ne aka zargi Atiku Abubakar da shirin ganin bayan ‘yan shi’a da zarar ya samu mulkin Najeriya.
Mun ga labarin ne a wani hoto da tambarin wata kafa mai suna Jaridar Najeriyaa da wani Jabir T. Usman ya wallafa a dandalin Facebook.
Bincike a shafukan tantance labaran karya kamar https://www.polihive.org/verify sun nuna babu inda Atiku ya yi makamanciyar maganar nan.
5. Ihun ‘yan Majalisar tarayya
Anthony Chigozie ya daura bidiyo a Facebook da sunan an ji ‘yan adawa a Majalisar wakilan Najeriya suna ihu da caccakar Bola Tinubu.
Labaran da ba gaskiya ba ne ya ce ‘yan majalisar sun rika ihun “APC Ole! APC Ole!” domin yakar soke aika sakamako a tsarin dokar zabe.
Rahoton FactCheck Hub ya nuna a nan ma tsohon bidiyo aka dawo da shi domin yaudarar jam’a, abin ya faru ne tun a watan Fabrairun 2026.
Marigayi Buhari ya so takarar Yemi Osinbajo?
Laolu Akande, tsohon hadimin Yemi Osinbajo, ya musanta ikirarin cewa marigayi Muhammadu Buhari bai goyi bayan takarar Yemi Osinbajo ba
Hadimin ya bayyana cewa marigayi tsohon shugaban kasar ya nuna wa farfesan goyon baya da kansa sannan ya karfafa masa gwiwa a lokacin.
Wannan martani ya biyo bayan kalaman tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal, wanda ya ce Buhari bai tare da takarar mataimakinsa.
Asali: Legit.ng


