Tinubu Ya Bayyana Muhimman Darussan da Ya Koya daga Rayuwar Buhari
- Shugaba Bola Tinubu ya ce ya koyi darussa masu muhimmanci daga marigayi Muhammadu Buhari, musamman kan shugabanci, kishin ƙasa da kyawawan halaye
- Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin mai ba shi shawara, Aliyu Moddibo, yayin ƙaddamar da littafin tarihin Buhari
- Ya ce Buhari ya nuna cewa mutuncin muƙamin gwamnati yana dogara ne da halayen wanda ke riƙe da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya bayyana cewa ya koyi darussa masu muhimmanci daga marigayi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana a matsayin shugaba, ɗan kishin ƙasa kuma mutum mai nagartattun halaye.
Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamban 2026 yayin ƙaddamar da littafin tarihin rayuwar Buhari mai juzu’i uku.

Source: Twitter
An shirya taron ƙaddamar da littafin ne ta kwamitin shirya taron tare da haɗin gwiwar kamfanin buga littattafai na May Publishing Limited, cewar rahoton jaridar TheCable.
Tinubu ya bayyana darussan da ya koya daga Buhari
Shugaban ƙasar, wanda mai ba shi shawara na musamman kan harkokin gudanarwa, Aliyu Moddibo, ya wakilta, ya ce rayuwar Buhari ta kasance abin koyi wajen hidimar jama’a, kyawawan halaye da kishin ƙasa.
Ya bayyana cewa mutane kan tuna da ma’aikatan gwamnati bayan rasuwarsu saboda irin ayyukan da suka gudanar da gudummawar da suka bayar ga al’umma.
Tinubu ya ce:
“A duk lokacin da muka fara rayuwa bayan mun rasu, abin da za mu bari a baya shi ne tarihin rayuwarmu.
“Hakan ya fi muhimmanci idan muka sadaukar da rayuwarmu wajen yi wa jama’a hidima.
“Muna barin tarihin ayyukan da muka gudanar da abubuwan tunawa da za su iya zaburar da waɗanda za su zo bayanmu. Wannan shi ne dalilin da ya sa muke da ƙarfin gwiwar ba da labarin rayuwarmu.”
Ya bukaci shugabanni su ba da tarihin rayuwarsu
Tinubu ya ce mutanen da suka riƙe manyan muƙaman gwamnati ba za su iya yin shiru su ƙi bayyana tarihin rayuwarsu ba.
Ya yi gargaɗin cewa idan mutum bai ba da labarin rayuwarsa ba, wasu za su yi hakan a madadinsa, kuma za su iya gabatar da shi ta hanyar da ba ta dace da yadda yake ganin kansa ba.
“Idan kuka ƙi ba da labarin rayuwarku, wasu za su yi hakan a madadinku. Wataƙila ba za ku ma gane kanku a cikin labarin da za su bayar ba.
“Wasu za su rubuta ne domin ɓata mana suna, yayin da wasu za su yi hakan domin ciyar da wani muradinsu gaba.” In ji shi
Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba na musamman
Shugaban ƙasar ya bayyana marigayi Buhari a matsayin mutum na musamman wanda ya karya tsarin siyasar da aka saba gani a Najeriya.
Ya ce Buhari ya ba waɗanda suke ganin sun fahimci salon siyasarsa mamaki, tare da zama abin koyi ga tsararrakin shugabanni da za su biyo baya.
Tinubu ya ce:
"A matsayinsa na shugaba mai ƙa’ida, tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja kuma shugaban ƙasa da aka zaɓa ta hanyar dimokuraɗiyya, dimbin mabiyansa sun nuna wani abu da masu sukarsa suka sha kasa fahimta.
“Wato yadda jama’a suka fahimci cewa mutum ne da ya gudanar da rayuwarsa ta wata hanya ta musamman.”
Sauƙin kan Buhari ya burge Tinubu
Tinubu ya ce yana sha’awar sauƙin kan Buhari, kishin ƙasarsa da jajircewarsa wajen yi wa Najeriya hidima.
“Na koyi abubuwa da dama daga Shugaba Muhammadu Buhari, a matsayinsa na shugaba kuma ɗan Adam wanda bai damu da tara dukiyar duniya ba, da kuma ɗan kishin ƙasa wanda ƙaunarsa ga Najeriya ta wuce muƙaman da ya riƙe.
“Ya koya mini cewa mutuncin muƙamin gwamnati yana dogara ne da halayen wanda ke riƙe da shi. Ya kuma koya min cewa kyakkyawan misalin shugaba yana ci gaba da magana ko bayan ya bar muƙaminsa.” In ji shi.

Source: Facebook
Shettima ya kwatanta farin jinin Obi da Buhari
A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya kawatanta farin jin marigayi Muhammadu Buhari da Peter Obi.
Shettima ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ba zai kai farin jinin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba.
Asali: Legit.ng