Yadda Za Ka Gane idan Kana Cikin Wadanda Gwamnati Za Ta Turawa Tallafin N100,000
- Gwamnatin tarayya ta bayyana yadda mutane za su gani suna cikin wadanda za a bai wa tallafin iyali na N100,000 a Najeriya
- Hukumar kula da shirin tallafin ta buƙaci waɗanda suka yi rajista su riƙa duba saƙonnin wayoyinsu domin sanin ko an zaɓe su
- Za a aika saƙonnin SMS ga waɗanda aka zaɓa a matakai daban-daban a shiyyoyin siyasa shida na ƙasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - An shawarci mutanen da suka yi rajista domin cin gajiyar shirin tallafin N100,000 na Gwamnatin Tarayya ga iyali masu fama da matsin rayuwa da su riƙa duba wayoyinsu domin ganin ko an turo masu saƙon SMS.
Hukumar kula da shirin ta ce za a aika wa waɗanda suka yi nasara saƙonnin SMS domin sanar da su cewa an zaɓe su, tare da bayyana musu ƙarin umarnin yadda za su karɓi kuɗin tallafin.

Source: Facebook
A cewar wata sanarwa da hukumar ta sanya wa hannu, wadda Punch ta samu ranar Juma’a, za a aika saƙonnin ne zuwa lambobin wayoyin da aka mutane suka shigar wajen zaɓen waɗanda za su ci gajiyar shirin.
Wannan na nufin masu neman tallafin su riƙa kula da layukan wayoyin da suka yi amfani da su wajen rajista, domin kamfanonin biyan kuɗin da aka zaɓa don tura kudin za su iya tuntubarsu.
Hukumar ta bayyana cewa ba za a kammala zaɓen waɗanda za su ci gajiyar shirin lokaci guda ba, domin za a gudanar da aikin ne a matakai daban-daban a shiyyoyin siyasa shida na ƙasar.
Sanarwar ta ce:
“Tsarin zaɓen mutanen da za ba tallafin ya ƙunshi gano gidajen da suka cancanta ta hanyar tsarin kula da walwalar al’umma.
"Za a yi amfani da ingantattun bayanan katin shaidar ɗan ƙasa, tantance gidaje bisa ƙa’idojin talauci da halin ƙuncin rayuwa, da kuma zaɓar waɗanda za su ci gajiyar shirin a matakai daban-daban a shiyyoyin siyasa shida.”
Saboda haka, masu neman tallafin da suka yi rajista a shafin yanar gizon nfsp.ng/signup na iya samun saƙonnin sanarwa a lokuta daban-daban, gwargwadon matakin da za a tantance gidajensu.
Wannan bayani na nufin cewa rashin samun saƙon SMS bai kamata ya zama dalilin ɗaukar cewa mutum ba zai samu tallafin ba, domin ana sa ran za a ci gaba da zaɓen waɗanda za su amfana a rukuni-rukuni.
Abin da za a yi bayan samun SMS
Hukumar kula da shirin ta ce waɗanda suka samu saƙon sanarwar an zaɓe su za su buƙaci bin umarnin da ke cikin saƙon kafin a aiwatar da biyan kuɗinsu.
Ta bayyana cewa za a tura wa waɗanda aka zaɓa tallafin N100,000 zuwa asusun bankunan da suka bayar lokacin yin rajista.
Asali: Legit.ng

