Sarkin Daura Ya Karrama 'Yar Tinubu, Ya ba Ta Babbar Sarauta a Jihar Katsina

Sarkin Daura Ya Karrama 'Yar Tinubu, Ya ba Ta Babbar Sarauta a Jihar Katsina

  • Sarkin Daura ya karrama Folashade Tinubu-Ojo, ’yar Shugaba Tinubu, saboda gudunmawarta wajen ci gaban al’umma da mata baki daya
  • Sarkin Daura ya kuma nada Minista Hannatu Musa Musawa sarautar Mairamar Kasar Hausa, yayin bikin Hawan Magajiya da aka gudanar a fadar masarautar
  • Bikin ya samu halartar Gwamna Dikko Umaru Radda da manyan jami’an gwamnati, sarakuna da masu rike da sarautun gargajiya daban-daban daga sassa daban-daban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Daura, Katsina - Sarkin Daura, Mai Martaba Alhaji Umar Faruk Umar, ya ba Hajiya Folashade Tinubu-Ojo, Iyaloja-Janar ta Najeriya da Lagos sarauta.

Basaraken ya ba Folashade sarautar Jakadiyar Kasar Hausa a bikin da aka gudanar a fadar masarautar da ke jihar Katsina.

Sarkin Daura ya bayar Tinubu sarauta
Folashade Tinubu-Ojo yayin da take karbar sandar sarautar Jakadiyar Kasar Hausa daga Sarkin Daura. Hoto: @MSIngawa.
Source: Twitter

Hakan na cikin wani rubutu da wakilin Legit Hausa ya gano a shafin @MSIngawa na X a daren yau Labara 26 ga watan Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu ya yi wa Yar'Adua, Buhari da sauran shugabannin Najeriya fintinkau

Tinubu ya yi magana kan ranar Hausa

An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya bayyana Hausawa a matsayin manyan ginshikai da ke taka muhimmiyar rawa wajen hadin kai da ci gaban Najeriya.

Tinubu ya ce harshen Hausa ya bunkasa sosai, inda ya zama daya daga cikin manyan harsunan hadin kai da kasuwanci a duniya.

Shugaban kasar ya taya al'ummar Hausawa murnar Ranar Hausa ta Duniya, wadda ake gudanarwa a ranar 26 ga watan Agusta Read more:

An ba Hannatu Musawa sarauta a Daura

Hajiya Folashade Tinubu-Ojo ’yar Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ce, kuma nadin nata ya kasance wani muhimmin lamari a masarautar Daura.

Sarkin ya kuma nada Ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Bude Ido da Tattalin Arzikin Kirkire-kirkire, Hannatu Musa Musawa, sarautar Mairamar Kasar Hausa.

An gudanar da bikin mai kayatarwa a fadar Sarkin Daura, jim kadan bayan kammala Hawan Magajiya, wanda aka fi sani da Sallar Gani.

Kara karanta wannan

Ko Tinubu na da abubuwan da zai shawo kan 'yan Najeriya su zaɓi APC a 2027? An samu bayani

Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya halarci bikin tare da Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, da sauran manyan jami’ai.

Haka kuma, Babban Sakataren Musamman na Gwamna, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, da wasu mata masu sarautun gargajiya sun halarci bikin a fadar.

An nada sarautun ne domin karrama gudunmawar wadanda aka ba su, musamman wajen bunkasa al’adu, karfafa mata da taimakawa ci gaban al’umma.

Nadin sarautar ya kara nuna muhimmancin al’adun gargajiya na Masarautar Daura da kuma bukatar karrama masu taimakawa wajen kare al’adun Hausawa da kuma karfafa masu guiwa.

Bikin ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya, manyan baki da masu rike da sarautu, wadanda suka taru domin shaida wannan tarihi.

Jonathan ya samu sarauta daga jihar Bauchi

Mun ba ku labarin cewa Masarautar Bauchi ta ba tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, sarautar gargajiya ta Jigon Bauchi.

Mai martaba Sarkin Bauchi, Rilwanu Adamu, ne ya naɗa Jonathan sarautar yayin wani biki da aka gudanar a fadar masarautar a Bauchi.

Gwamna Bala Mohammed ya yaba wa masarautar kan karrama Jonathan, yayin da tsohon shugaban ya gode, tare da alkawarin mutunta dokoki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.