Sarkin Legas, Oba Rilwanu, ya ziyarci Sanusi har gida a Legas (Hotuna)

Sarkin Legas, Oba Rilwanu, ya ziyarci Sanusi har gida a Legas (Hotuna)

Oba na jihar Legas, Rilwan Akiolu ya kai ziyarar kara ga tubabben Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi a gidansa da ke Legas a daren Lahadi, 15 ga watan Maris.

Sanusi ya isa jihar Legas ne a ranar Juma'a 14 watan Maris bayan kotu ta bada umarnin sakinsa daga tsarewar da aka yi masa a jihar Nasarawa.

Sarkin Legas, Oba Rilwanu, ya ziyarci Sanusi har gida a Legas (Hotuna)
Sarkin Legas, Oba Rilwanu, ya ziyarci Sanusi har gida a Legas (Hotuna)
Asali: Twitter

A wani labari na daban, majalisar jihar Kano ta dakatar da 'yan majalisa biyar na watanni shida dangane da hargitsin da aka samu a zauren majalisar a ranar Litinin din makon jiya. Wannan hargitsin kuwa yayi sanadin kwace sandar majalisar.

Sarkin Legas, Oba Rilwanu, ya ziyarci Sanusi har gida a Legas (Hotuna)
Sarkin Legas, Oba Rilwanu, ya ziyarci Sanusi har gida a Legas (Hotuna)
Asali: Twitter

A dawowa zaman zauren da aka yi a yau Litinin, Abdulazeez Gafasa, kakakin majalisar ya ce, an dakatar da 'yan majalisar ne sakamakon take dokar da suka yi, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.

Sarkin Legas, Oba Rilwanu, ya ziyarci Sanusi har gida a Legas (Hotuna)
Sarkin Legas, Oba Rilwanu, ya ziyarci Sanusi har gida a Legas (Hotuna)
Asali: Twitter

'Yan majalisar da aka dakatar sun hada da: Garba Yau Gwarmai mai wakiltar mazabar Kunchi/Tsanyawa, Labaran Abdul Madari mai wakiltar mazabar Warawa, Isyaku Ali Danja mai wakiltar mazabar Gezawa, Mohammed Bello mai wakiltar mazabar Rimingado/Tofa da Salisu Ahmed Gwamgwazo mai wakiltar mazabar birnin Kano.

Kamar yadda kakakin majalisar ya sanar, "Yan majalisar biyar an dakatar dasu ne sakamakon karantsaye da suka yi ga dokokin majalisar ta hudu wacce ta haramta kawo tsaiko da hana zaman majalisar.

"Sun kawo rashin hankali da yunkurin kwace sandar majalisar don zagon kasa ga zaman majalisar na wannan lokacin," Gafasa yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng