Buba Galadima Ya Fito da 'Son Kan' Tinubu, Ya Ce Babu Mai Zaben Shi sai Mahaukaci
- Buba Galadima bai ji dadin yadda aka ceto daliban makaranta a Oyo, amma aka manta da takwarorinsa a Borno ba
- Babban jigon na NDC ya ce gwamnatin Bola Tinubu ta tura dukkan jami'an tsaro domin ceto yaran da aka sace a jihar Oyo
- Amma da hakan ta faru a Borno har yau ba a kubutar da yaran ba, a kan haka Buba ya ce bai dace a ba APC kuri’un jihar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Borno - Fitaccen ɗan adawa, Buba Galadima, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana mai zarginta da nuna bambanci.
Injiniya Buba Galadima yana ganin Gwamnatin tarayya ta yi watsi da yaran makaranta da aka sace a jihar Borno tun Mayu da Yunin 2026.

Source: Twitter
Buba Galadima ya tuno zancen daliban Borno
Daily Trust ta ce Buba Galadima ya bayyana haka ne a wajen taron tattaunawa da jama'a da NDC ta shirya a Maiduguri, a jihar Borno.

Kara karanta wannan
Ana zargin ‘dan takaran gwamnan ADC da shiga yarjejeniya a asirce da jam’iyyar APC
Ya ce halin da yaran da aka sace daga Mussa da Lassa a Borno suke ciki ya nuna irin yadda gwamnatin Tinubu ta yi watsi da su.
Buba Galadima ya kwatanta yadda Gwamnatin tarayya ta dauki mataki game da abin da ya faru a jihar Oyo lokacin da aka sace dalibai.
An rahoto shi yana cewa gwamnati ta tashi tsaye da gaggawa wajen ceto yaran da aka sace a Oriire, amma har yau daliban Borno na tsare.
Ya ce:
"An sace yaran Mussa kusan a daidai lokacin da aka sace wasu yara a jihar Oyo, ranar 15 ga Mayun 2026.
Shugaban ƙasa ya tura dukkan shugabannin hukumomin tsaro zuwa wurin, tare da ba su umarnin tabbatar da an kuɓutar da yaran.
Amma game da yaranmu a nan Borno, shiru kawai aka yi. Ana mu'amala da mu kamar baƙi daga Chadi, Kamaru da Nijar.
Kamar ana gaya mana ne cewa ba mu cancanci a ba mu kariya a Najeriya ba. Mahaukaci ne kawai zai zaɓi Tinubu."

Kara karanta wannan
Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu
Ana zargin gwamnati ta manta da Borno
Buba Galadima ya ce abin takaici ne yadda duk da kasancewar Borno na da mataimakin shugaban ƙasa, amma ta yi watsi da dalibansu.
Ya ce irin wannan hali ba shugabanci na gari ba ne, illa nuna wariya ga wasu 'yan Najeriya.
A ƙarshe, ‘dan siyasar ya yi kira ga gwamnati da ta gaggauta ba da fifiko wajen ceto yaran da aka sace watanni shida da suka wuce.
An ji Buba yana gargadi cewa ci gaba da yin shiru kan lamarin zai ƙara mayar da jihar da yankin Arewa maso Gabas saniyar ware.
An gudanar da taron ne domin wayar da kan jama'a da kuma neman goyon mutane su bi bayan Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso.

Source: Getty Images
Kwaratsi wajen taron yakin zaben APC
Labarin nan ya nuna an samu raunuka yayin da aka kai farmaki a wurin gangamin APC har ana tunanin an rasa rai a jihar Delta.
An yi arangama tsakanin matasan Ijaw da Itsekiri a lokacin gangamin jam’iyyar APC a Makarantar Nana Model College da ke Warri.
Rikicin ya samo asali ne daga rashin jituwa a dalilin sake fasalin rumfunan zaɓe da INEC ta yi a ƙaramar hukumar Warri ta Kudu.
Asali: Legit.ng
