Raddin da Jalo Jalingo Ya Yi wa Sarakuna Ya Sa Ya Ji Babu Daɗi annun Yan Facebook
- Sakataren Majalisar Malaman kungiyar Izala ya ce dukkan sarakunan gargajiya wakilan masu mulki ne kawai
- Ibrahim Jalo Jalingo ya yi rubutu yana cewa dokokin Shari’ar Musulunci kan talakawa sun shafi har da sarakunan
- Sheikh Jalingo ya nuna sarki zai iya rasa rasa rawaninsa idan ya yi fito-na-fito da masu mulkin da suka nada shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Taraba - Ibrahim Jalo Jalingo malamin addini ne da ya yi fice wajen goyon bayan gwamnatin APC ta Bola Tinubu.
Wannan karo malamin Musuluncin ya dura kan sarakunan gargajiya, ya tunatar da su cewa suna karkashin gwamnati.

Source: Facebook
A dandalin Facebook, Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo ya gargadi sarakuna game da yin fito-na-fito da masu mulki a Najeriya.
Malamin ya tuna wa sarakunan gargajiya cewa matsayinsu daya a yanzu da talakawa wajen biyayya ga shugabannin siyasa.
Jalo Jalingo ya yi magana bayan waki'ar Katsina
Babu mamaki ya yi wannan rubutu ne bayan Sarkin Katsina ya yi wasu maganganu da ‘yan APC suka kai masa ziyara.
Abdulmumin Kabir Usman ya fada wa ‘yan kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu cewa abubuwa ba su tafiya daidai a kasa.
Ba a dade da yin haka ba sai ya yi rubutu ranar Juma’a, yana jan sarakuna cewa idan aka tunbuke su, ba a saba wa doka ba.
Rubutun Jalo Jalingo da ya jawo magana
DUKKAN SARAKUNA A YANZU WAKILAI NE SU NA MASU MULKI:
1. Dukkan wani sarki a Nigeria a yanzu wakili ne kawai shi na masu mulkin Nigeria, kuma dukkan wasu ƙa'idojin Khuruuji da Shari'ar Musulunci ta zayyana su game da talakawan Nigeria to shi ma waɗannan Ƙa'idojin sun hau kansa, sam sam babu wani banbanci tsakaninsa da sauran al'ummar Ƙasa cikin waɗannan Ƙa'idojin, haka lamarin yake a Shari'ance da kuma Nigeriance.
2. Sannan a duk lokacin da masu mulkin Ƙasar suka sauƙe shi daga wannan wakilcin da suka ba shi, toh kuwa tabbas ya sauƙa ken nan a dai Shari'ance da kuma Nigeriance.

Kara karanta wannan
Tinubu: Nasir El Rufai ya daura bidiyon abin da Sarkin Katsina ya fada wa Abdulaziz Yari
- Ibrahim Jalo Jalingo
Martanin da aka maida wa malamin addinin
Masu bibiyar Facebook ba su kyale malamin haka ba, mafi yawansu sun fito suna masu Allah-wadai da matsayar da ya dauka.
Wani mai suna Jagora Maitsamiya ya ankarar da wani malamin addinin, Dr Magaji Zarewa game da wannan magana ta takwaransa.
A baya ya fito Facebook, yana tir da masu cin mutuncin malamai, Maitsamiya ya ce masa irinsu Jalingo suke bata wa shehunnan suna.
“Dr. Magaji Falalu Zarewa Ina ga iya wannan ya Isa uziri ga masu zagin malamai.
Saboda wallahi kwata-kwata Babu tausayi, jin-kai, rahama, a maganganun Malam”
Habib Dantagwarma ya ce:
Maganarka ta yi hannun riga da gaskiya; son zuciyarka ne kawai tsantsa
Engr Usman Baba Abubakar ya ce:
Hon Allah ya yaye maka wannan cuta ta son zuciya da ke damunka
Saƙon da ka ke son isarwa shi ne:
Sarkin Katsina yayi kuskure wajen tunatar da shugaban qasa halin rashin tsaro da al'ummar sa ke ciki ko?

Kara karanta wannan
An ba Kwankwaso shawarar hada kai da Tinubu a sakon taya shi murnar cika shekara 70
Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya kare mu fitintunun zamani...
- Khidir Muazu
Yusuf Alhassan Abbaty kuwa cewa ya yi:
Allah ya kyauta.
Yanzu kai so kake ya zama ɗan amshin shata kamar yadda ku ka lalace ku ka zubar da mutuncinku, Sarkin mai Katsinan Dikko ya fi ka gaskiya.
Ahmadu Tijjani Umara kuwa sai dai ya rubuta:
Ajabba! Lallai Naira shegiya ce!
Sai kuma:
Allah ya shirye ka Data Sheikh Rararan Izala idan kai mai shiryuwa ne, in kuma ba mai shiryuwa bane kai Allah yai mana maganinka da kai da azzuluman shugabbanin da ka ke karewa
- In ji Yahaya YK
Abdulhamid Dauda Sulaiman ya ce:
Innalillahi wa inna alaihi rajiun
Malamai da ake tsammanin zasu fada wa shugabanni Gaskiya
Amma wai yau su ne masu yin hannun ka mai sanda ga shugabannin cewa duk wanda ya fada musu gaskiyar, su cire shi daga mukaminsa.
To ai malam in dai Sarkin Katsina ya rasa muƙaminsa na sarauta a kan fadin gaskiya ai y aci riba domin muna masa kyakkyawan zaton Allah zai ba shi sarautar da ta fi wannan a Aljanna insha Allah.
Allah ya shirya mana shugabannin da malamammu.
Muhammad Kodomi ya ce:
Wane sako ka ke son isarwa? Sheikh ina maka nasiha tare da ni cewa mu ji tsoron Allah
Zakariya Mohammed Abubakar ya rubuta:
"Masu tallata Tinubu da sunan malanta suna zaluntar mabiyarsu"
Muawiya Yahaya Muazu Sabuwa ya yi addu'a:
"Allah wadaran naka ya lalace"
Ibrahim A. El-Caleel ya rubuta masa cewa:
Akramakallah,
Wannan dai ba ka isa ba gaskiya. Sarkin Katsina ya fi ka kusa da gaskiya a wannan babin.
Kai dai tunda amshin shata ya fi maka a wannan lokacin, to sai mu maka uzuri da fatan Allah Ya fadakar da kai.
Amma kwakwalwarmu ba ta lalace ba da har za mu yi tunanin cewa abinda kake yi ya fi dacewa da addini fiye da na Sarkin Katsina.
Allah Ya taimaki Sarkin Katsina akan daidai, Ya tsare shi.
Kai ma Allah Ya taimake ka domin ka samu tsayawa gaskiya.
Ameen
Wasu sun goyi bayan Sheikh Jalingo
Shi Abubakar NTA wani ‘dan Izala mazaunin Jalingo, yana goyon bayansa, ya ce:
"Gaskiya ne, su sarakuna karkashin Local Government Chairman ma suke, kuma tun a tashin farko mafi yawan su an zarge su wajen daurewa barayin daji gindi, musammam sarakunan yankin Zamfara, Kebbi, Katsina. Wasu ma sai da Gomnati ta dakatar dasu kai tsaye saboda zargi ya yi yawa a kansu.
Allah ya kara taimakon Shugaban kasar mu ya ba shi nasara cikin sauki."
Nasir Muaz ya soki lokacin da aka yi wannan magana:
"Mallam wallahi ka kusa kai mutane wuya.
Abin da ka fada haka ne amma ba lokacin da mutane suke cikin fushin mulkin nan ba ne ya kamata ka yi wannan magana.
Allah wargaza mulkin Azzalumai, mayaudara da son zuciya"
Nasir El-Rufai ya ji dadin kalaman Sarkin Katsina
A baya aka ji labari cewa Malam Nasir El-Rufai ya wallafa bidiyon abin da Sarkin Katsina ya faɗa wa Sanata Abdulaziz Yari.
Bidiyon ya nuna tattaunawar Abdulmumin Kabir da Yari yayin ziyarar tawagar yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu. a fadar sarkin.
Ziyarar na cikin shirye-shiryen APC na neman goyon bayan sarakunan gargajiya gabanin zaɓen 2027 da kuma sa albarkarsu.
Asali: Legit.ng


