Ciyaman a Kano Ya Ballo Ruwa, Ya Yi Barazana ga Jama’a kan Zaben APC a 2027
- Ƙungiyar Amnesty International ta soki shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Abubakar Ma’azu Mojo, bisa wasu kalamansa
- An zargi shugaban ƙaramar hukumar da ƙarfafa amfani da barazana, tashin hankali da daba domin karɓe rumfunan zaɓe daga yan adawa
- Amnesty ta buƙaci hukumomin tsaro su ɗauki mataki, tana gargadin cewa irin waɗannan kalamai na iya tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano — Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta yi Allah-wadai da kalaman da ake zargin shugaban ƙaramar hukumar Gwale da yi.
An gano Abubakar Ma’azu Mojo, ya yi kan yadda magoya bayan jam'iyyar APC za su tabbatar da nasarar jam'iyyar a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Ƙungiyar ta bayyana damuwarta ne bayan wani bidiyo ya bazu a kafafen sada zumunta, inda aka ga Mojo yana magana kan yadda za su tabbatar da APC ta samu nasara a rumfunan zaɓe.
A cewar Amnesty, Mojo ya umarci magoya bayan jam'iyyar da su yi amfani da duk wata hanya, ciki har da tsoratarwa da tashin hankali, domin ganin sun cimma burinsu.
Abin da shugaban karamar hukumar ya ce
A cikin kalaman da aka jingina masa, shugaban ƙaramar hukumar ya yi maganganu da ke cike da barazana da ya tayar da hankula.
Ya ce:
"Ko ta hanyar tsoratarwa, tashin hankali, daba ko wata hanya, ku tabbatar kun samar wa APC nasara a rumfunan zaɓenku."
Amnesty ta bayyana kalaman a matsayin barazana ga zaman lafiyar jama'a, tana mai cewa irin wannan furuci na iya haifar da fargaba tare da tauye haƙƙin 'yan ƙasa na shiga zaɓe cikin lumana.

Source: Original
Amnesty ta buƙaci a ɗauki mataki
Ƙungiyar ta yi kira da a tabbatar da ɗaukar matakin da ya dace kan duk wanda aka samu da hannu wajen yin barazanar tayar da tarzoma a lokacin zaɓe.
Ta kuma yi gargaɗin cewa bai kamata a ɗauki zaɓe a matsayin yaƙin dole sai an ci ba, domin hakan na iya ƙarfafa tashin hankali da hana masu zaɓe bayyana ra'ayinsu cikin 'yanci.
Bugu da ƙari, Amnesty ta soki hukumomin tsaro a Najeriya, tana zarginsu da rashin ɗaukar isassun matakai kan barazanar tashin hankalin zaɓe da wasu 'yan siyasa ke yi gabanin zaɓen 2027.
Ƙungiyar ta jaddada cewa dole ne a mutunta zaɓin siyasar kowane ɗan ƙasa, tare da tabbatar da cewa kowa na iya shiga harkokin zaɓe ba tare da fuskantar barazana ko tilastawa ba.
Wannan kira na Amnesty ya zo ne a daidai lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan kalaman siyasa da shirye-shiryen tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.
Rikicin APC ya yi kamari a Kano
Mun ba ku labarin cewa jigon APC a Jihar Kano, Aminu Shehu Sharada, ya roƙi Shugaba Bola Tinubu da Sanata Abdulaziz Yari su shiga tsakani don yin sukhuba jam’iyyar.
Ya yi gargaɗin cewa rikicin cikin gida na iya rage wa APC damar samun nasara a zaɓen 2027 idan ba a gaggauta shawo kansa ba.
Sharada ya ce shugabannin jam’iyyar a Kano na buƙatar tattaunawa da sulhu domin gina haɗin kai kafin babban zaɓen ƙasar.
Asali: Legit.ng