Tsohon Sanata Ya Yi Nadamar Goyon bayan Gwamna har Ya Hau Kujerar Mulki, Ya Nemi Afuwa

Tsohon Sanata Ya Yi Nadamar Goyon bayan Gwamna har Ya Hau Kujerar Mulki, Ya Nemi Afuwa

  • Tsohon shugaban APGA na ƙasa, Sanata Victor Umeh, ya nemi afuwar gudummuwar dmda ya bayar wajen zaɓen Gwamna Chukwuma Soludo
  • Umeh ya zargi Soludo da cin amanar amincewar da aka ba shi, yana mai cewa bai cika wasu alkawura ga waɗanda suka tallafa masa ba
  • Sanatan ya kuma soki gwamnan kan adawarsa da burin Peter Obi na tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra, Nigeria - Tsohon sanatan da ya wakilci mazabar Anambra ta Tsakiya a Majalisar Dattawa, kuma tsohon shugaban jam’iyyar APGA na ƙasa, Victor Umeh, ya yi nadamar goyon bayan Gwamna Charles Chukwuma Soludo.

Sanata Umeh ya nemi afuwar rawar da ya taka wajen taimaka wa Farfesa Chukwuma Soludo ya zama gwamnan jihar Anambra.

Victor Umeh.
Tsohon shugaban jam'iyyar APGA na kasa, Sanata Victor Umeh Hoto: Senator Victor Umeh
Source: Facebook

Umeh ya zargi Soludo da cin amana

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Jam'iyyar adawa ta yanke shawara, ta umarci mabiyanta su zaɓi Tinubu a 2027

Leadership ta rahoto cewa ya zargi Soludo da nuna ƙin al’ummar jihar Anambra da ma yankin Kudu maso Gabashin Najeriya baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) ya zama “mayaudari kuma ma ci amana,"

Umeh ya bayyana hakan ne a wajen bikin cika shekaru biyar da kafuwar kafar yaɗa labara8 a Jihar Anambra, The Razor Newspaper, da aka gudanar a Awka, babban birnin jihar, ranar Alhamis.

Ya bayyana cewa a matsayinsa na Darakta Janar na ƙungiyar kamfen ɗin da ta samar da Soludo a matsayin gwamnan Anambra, ya bata lokaci da kudadensa wajen tabbatar da nasarar APGA.

Tsohon sanata ya tuka wahalar da ya sha

Ya ce ya haɗa kai da jiga-jigai, musamman Cif Primus Odili, shugaban ma’aikatan gwamnan jihar a wancan lokacin, Cif Willie Obiano, wajen tara kuɗi daga masu hannu da shuni domin gudanar da kamfen ɗin zaɓen gwamna.

Sai dai ya ce yana nadamar yadda Soludo ya ci amanar amincewar da suka yi masa.

Umeh ya ce, alal misali, a lokacin kamfen ɗin, Soludo ya zo wurinsa ya roƙe shi da ya taimaka wajen samo kuɗi, yana mai cewa ba shi da kuɗin yakin neman zabe.

Kara karanta wannan

"Ba sai an yi magudi ba," Gwamna ya ce an kammala zaben shugaban kasa na 2027

Duk da haka, Umeh ya ce babban abin da ya fi ba shi takaici shi ne yadda Soludo ya dauri damarar hana ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC, Peter Obi, samun nasara a zaɓen 2027 mai zuwa.

Soludo.
Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo a gidan gwamnatinsa da ke Awka Hoto: Charles Chukwuma Soludo
Source: Facebook

Mutanen Anambra na tare da Obi

“Al’ummar Jihar Anambra suna goyon bayan Peter Obi na zama shugaban ƙasa. Kuma Peter Obi shi ne mafi cancanta a cikin duk waɗanda ke neman zama shugaban ƙasa.
“Ina daga cikin masu ƙarfi wajen goyon bayan a samu shugaban Najeriya daga Kudu maso Gabas domin tabbatar da adalci da daidaito. Abin da Soludo yake koyar da ’yan Igbo ba shi da ma’ana; wannan ba siyasa ba ce,” in ji Umeh.

Umeh ya kuma ƙalubalanci ikirarin Soludo na cewa manufar APGA a zaɓen shugaban ƙasa ita ce ta goyi bayan sake zaɓen shugaban ƙasa mai ci domin jam’iyyar ta samu damar kasancewa cikin gwamnatin tarayya.

Gwamna Soludo ya hango nasarar Tinubu

Kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Chukwuma Soludo, ya ce Shugaba Bola Tinubu ba ya bukatar maguɗin zaɓe domin samun wa’adi na biyu a zaɓen 2027.

Gwamna Soludo ya ce alamu sun nuna cewa APC ta yi wa yan adawa fintinkau, kuma za ta sake lashe zabe cikin sauki a shekara mai kamawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262