Kwankwaso Ya Ce Kano da Jihohin Arewa 6 Za Su Sake Zaben Tinubu a 2027, Ya Fadi Dalili
- Ɗan kwamitin kamfen APC, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya ce yankin Arewa maso Yamma ya kuduri aniyar sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027
- Ya ce taron gangamin yaƙin neman zaɓen APC da aka gudanar a Kaduna ya nuna yadda yankin ke goyon bayan Tinubu domin ya sake yin wa’adi na biyu
- Kwankwaso ya ce goyon bayan yankin ya samo asali ne daga burin tabbatar da haɗin kan ƙasa, adalci wajen rabon arziki da ci gaba mai ɗorewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - Mamba a Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba na APC, Musa Illiyasu Kwankwaso, ya jaddda goyon bayan Arewa maso Yamma ga Shugaba Bola Tinubu.
Kwankwaso ya bayyana cewa al'ummar yankin Arewa maso Yamma sun kuduri aniyar sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Source: Facebook
The Nation ta ruwaito cewa Kwankwaso ya ce ɗumbin mutanen da suka halarci gangamin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC a Kaduna ranar Asabar, ya nuna ƙudurin yankin na goyon bayan Tinubu.
Da yake zantawa da manema labarai a gefen taron da aka gudanar a filin VIP Pavilion, Kwankwaso ya bayyana taron a matsayin wata alama bayyananniya da ke nuna matsayar siyasar Arewa maso Yamma gabanin babban zaɓen 2027.
Arewa masu Yamma na tare da Tinubu
Ya ce yadda aka tara dimbin mambobin jam’iyya da magoya baya ya kawar da shakku game da aniyar yankin na goyon bayan sake zaɓen Tinubu.
Ya jaddada cewa burin tabbatar da haɗin kan ƙasa, ci gaba cikin adalci da kuma samar da Najeriya mafi inganci ne ya sa suka amince da shi.
“Yau, mu al’ummar yankin siyasa na Arewa maso Yamma mun bayyana matsayarmu karara game da wanda muke goyon baya.

Kara karanta wannan
Jam'iyyun adawa 3 Sun haɗa kai da APC domin yallata Shugaba Tinubu, an jero sunayensu
“Zaɓinmu shi ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ya nuna jajircewarmu wajen samar da Najeriya mafi inganci da haɗin kan ƙasa,” in ji Kwankwaso.
Dalilin Arewa na goyon bayan Tinubu
Ya bayyana cewa sake zaɓen Tinubu zai ba da damar ƙarfafa ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da ci gaba cikin adalci da raba albarkatun ƙasa yadda ya kamata a tsakanin yankunan siyasa shida na ƙasar, cewar Vanguard.

Source: Facebook
Kwankwaso ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa goyon bayan Arewa ga Tinubu tamkar ciniki ne, inda ya dage cewa yankin ya kuduri aniyar cika alƙawarin siyasar da ya ɗauka ta hanyar tabbatar da nasarar shugaban ƙasar a 2027.
“Asiwaju ɗan takarar Arewa ne, kuma ba zai inganta wani abu da ya saɓa wa burinsa ba, domin mu mutane ne masu riƙon amana, kuma za mu tabbatar da nasararsa a 2027,” in ji shi.
Kwankwaso ya hango nasarar Tinubu
Kun ji cewa Musa Illiyasu Kwankwaso ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027,
Jigon APC ɗin ya lura cewa shigowar manyan ’yan siyasar adawa daga.sassa daban-daban na siyasa na nuna goyon baya na musamman ga shugabancin Tinubu.
Asali: Legit.ng
