Tinubu Ya Yi Tanadi domin Rage Tsadar Abinci, Zai Raba Miliyoyin Buhunan Taki

Tinubu Ya Yi Tanadi domin Rage Tsadar Abinci, Zai Raba Miliyoyin Buhunan Taki

  • Gwamnatin tarayya ta ce za ta saki buhunan takin zamani miliyan uku da hatsi da ta tanada domin rage farashin abinci a Najeriya
  • Ministan noma, Abubakar Kyari, ya ce za a fitar da takin cikin wata guda, yayin da za a saki hatsin da aka ajiye nan ba da jimawa ba
  • Gwamnati ta kuma ce za ta fara rabon taraktoci 2,000, yayin da ake sa ran amfanin gona 13 cikin 17 zai samu karuwar yawan amfanin gona

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Gwamnatin tarayya karkashin Bola Tinubu ta shirya kawo hanyar sauki ga yan Najeriya kan tsadar abinci.

Gwamnatin ta bayyana shirinta na sakin buhunan takin zamani miliyan uku da hatsi da ta tanada domin rage farashin kayan abinci da bunkasa harkokin noma a Najeriya.

Kara karanta wannan

Matakai 5 da za a bi a samu rancen N100m na Tinubu domin sayen gida

Tinubu zai fitar da abinci da buhunan takin zamani
Shugaba Bola Tinubu da wani matashin manomi a gonarsa. Hoto: Bayo Onanuga|Getty Images.
Source: Getty Images

Ministan noma da samar da abinci, Abubakar Kyari, ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja, yayin gabatar da rahoton binciken ayyukan noma na daminar shekarar 2026, cewar TheCable.

Shirin da Tinubu ya yi ga manoma

Kyari ya ce shirin shugaban kasa na samar da takin zamani na shirin fitar da buhunan takin cikin wata guda domin rage kudin da manoma ke kashewa wajen sayen kayan aikin gona.

Ya kara da cewa gwamnatin za ta kuma saki hatsin da aka saya aka adana karkashin shirin Bankin Noma na tabbatar da mafi karancin farashin amfanin gona.

Ministan ya ce za a fitar da hatsin ne domin daidaita farashin kayayyakin abinci a kasuwanni, yayin da gwamnati za ta sanar da tsarin rabon kayayyakin nan gaba.

Tinubu zai raba wa manoma taki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya a fadar shugaban kasa. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

Gwamnati za ta kara tallafa wa manoma

Kyari ya bayyana cewa karuwar yawan amfanin gona da fadada filayen noma za su taimaka wajen kara wadatar abinci da rage farashin wasu kayayyaki.

Kara karanta wannan

Ana neman yafe wa 'yan Najeriya bashin gwamnati har Naira tiriliyan 1

Ya ce kwatanta farashin abinci na shekarar 2025 da 2026 ya nuna an samu raguwar farashin wasu kayayyaki, musamman madara da masara, duk da cewa bai bayyana takamaiman alkaluman raguwar ba.

Ministan ya danganta fadada filayen noma da inganta tsaro a wasu yankuna, yana mai cewa jami'an tsaro sun taimaka wa manoma wajen komawa wuraren da a baya ba sa iya zuwa saboda matsalar tsaro, cewar Punch.

A bangaren samar da kayan aikin noma, Kyari ya ce gwamnati ta riga ta raba taraktoci 2,000, yayin da ake sa ran fara isar da wasu a kashi na biyu cikin watanni biyu zuwa uku masu zuwa.

Ya kuma ce asusun bunkasa noma na kasa da sake fasalin Bankin Noma na daga cikin matakan da gwamnati ke dauka domin saukaka wa manoma samun kudaden gudanar da ayyukansu.

Farashin kayan abinci ya fadi a kasuwanni

A baya, an ji cewa Ministan Noma da Samar da Abinci, Abubakar Kyari, ya ce farashin wasu muhimman kayan abinci ya ragu da kashi 50 a faɗin Najeriya.

Kyari ya ce an samu raguwar farashin ne idan aka kwatanta da matakan farashin da aka samu kafin shekarar 2023.

Ya ce gwamnati ta ƙara samar da kayan noma tare da zuba jari a ababen more rayuwa na karkara da tallafa wa ƙananan manoma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.