Matasa Sun Far Wa Mawakin Siyasa, Dauda Rarara da Duka a Masallacin Juma'a

Matasa Sun Far Wa Mawakin Siyasa, Dauda Rarara da Duka a Masallacin Juma'a

  • An kai wa fitaccen mawakin siyasar Hausa, Dauda Kahutu Rarara, hari a Masallacin Ƙasa da ke Abuja ranar Juma’a
  • Rarara ya shahara wajen rera waƙoƙin yabon ’yan siyasa na jam’iyyar APC, ciki har da Shugaba Bola Tinubu
  • Maharan sun far masa yayin da yake shiga masallacin, duk da ƙoƙarin jami’an tsaro na hana su kai masa hari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wasu fusatattun matasa sun far wa fitaccen mawakin siyasar Hausa, Dauda Kahutu, wanda aka fi sani da Rarara, hari a Masallacin Ƙasa da ke Abuja ranar Juma’a.

Mawakin, wanda ya shahara wajen rera waƙoƙin yabon ’yan siyasar jam’iyyar APC ya fitar da waƙar Shugaba Bola Tinubu wadda ake kunnawa a gangamin kamfen ɗin shugaban ƙasar, musamman a Arewa.

Daily Trust ta rahoto cewa waƙar mai taken Omologo ta samu damar rerawa kai tsaye a gaban Shugaba Tinubu a lokacin ziyarar aiki da ya kai jihar Katsina a bara.

Kara karanta wannan

Magana ta kare: Jam'iyyar adawa ta yanke shawara, ta umarci mabiyanta su zaɓi Tinubu a 2027

Wakar tana daga cikin wakokin da suka kara daga darajar mawakin, wanda ya dade tauraruwarsa na harkawa a fagen wakokin siyasa a Najeriya.

Abin da ya faru da Rarara

Rahotanni sun nuna cewa Rarara ya gamu da fushin dandazon matasa lokacin da ya tunkari babban masallacin kasa da ke Abuja yau Juma'a, 20 ga watan Nuwamba, 2026.

Yayin da mawakin ke dosar masallacin, wasu jami’an tsaro sanye da kayan farar hula da kuma waɗanda ke cikin kakin aiki na rakiyarsa, sai ga wasu fusatattun mutane sun nufi inda yake cikin hanzari.

Jami’an tsaron sun yi ƙoƙarin hana mutanen kai masa hari, amma sun ci gaba da dukan mawakin ta ɓangarori daban-daban, inda aka ce sun lakada masa dukan tsira.

A ruwaito cewa a lokacin da lamarin ke faruwa, Dauda Rarara, wanda ke sanye da hula mai tambarin Tinubu, ya cire hularsa.

Karin bayani na nan tafe...

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262