Tirkashi: Tuggun da Amurka da Israila Ke Duba Yiwuwar Yi kan Iran
- Isra’ila na son ƙaddamar da sabon farmaki tare da Amurka saboda saurin da Iran ke bi wajen sake gina masana’antun kera makamai masu linzami
- Sojojin Isra’ila sun shirya fuskantar sabon zagaye na faɗa, yayin da Amurka ke da manyan jiragen yaƙi da rundunonin soji a yankin
- Ana fuskantar rashin tabbas kan matakin Donald Trump, yayin da Netanyahu ke fuskantar yiwuwar rasa kujerar firaminista bayan sakamakon zaɓen Isra’ila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Isra’ila da Amurka na nazarin yiwuwar ƙaddamar da sabon farmaki kan Iran nan ba da jimawa ba, kamar yadda wasu majiyoyi masu masaniya kan lamarin suka bayyana.
Majiyoyin sun bayyana cewa gwamnatin Firaminista Benjamin Netanyahu na nuna damuwa kan yadda Iran ke saurin sake gina ƙarfin masana’antunta na kera makamai masu linzami.

Source: UGC
Isra’ila da Amurka na nazarin sabon farmaki
Tashar CBS ta bayyana cewa majiyoyin ne suka sanar mata da hakan a cikin wani rahoto da ta fitar a ranar Juma'a, 20 ga watan Nuwamban 2026.
Haka kuma, Isra’ila na fargabar yadda Iran ke ƙoƙarin kare muhimman cibiyoyin sojojinta da na nukiliya daga hare-hare, ta hanyar mayar da su ƙarƙashin ƙasa.
A wannan makon, Shugaban Amurka Donald Trump ya kuma yi zargin cewa Iran na iya ƙoƙarin ƙera makamai masu hadari, duk da cewa bai gabatar da wata hujja da ke tabbatar da zargin ba.
Tattaunawar Amurka da Iran ta gaza cimma matsaya
Watanni da dama na tattaunawa a kaikaice tsakanin Amurka da Iran sun gaza samar da yarjejeniyar tsagaita wuta da za ta ba da damar sake buɗe mashigar ruwan Hormuz.
Iran ta ƙi tattauna batun shirinta na nukiliya, matuƙar Amurka ba ta ɗage takunkumin killace ta ta ruwa ba, tare da amincewa da wasu muhimman sharuɗɗa guda shida.
A cewar majiyoyin, sojojin Isra’ila sun kammala shirye-shiryen fuskantar sabon zagaye na faɗa da Iran. Haka kuma, sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana domin mayar da martani idan Iran ta fara kai hari.
Gwamnatin Netanyahu ta fi son ƙaddamar da sabon aikin soji tare da Amurka. Sai dai har yanzu ba a san ko Trump yana son ba da umarnin sake kai hari ba, ko kuma irin matakin da zai ɗauka.
Yaƙin Iran ya kasance ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da suka taimaka wajen kayar da jam’iyyar Republican a zaɓen tsakiyar wa’adin mulki na baya-bayan nan. Haka kuma, yaƙin bai samu karɓuwa sosai a tsakanin Amurkawa ba.
Amurka ta tanadi manyan kayan yaƙi a yankin
Amurka na da manyan kayan aikin soji a yankin, ciki har da dubban sojoji, jiragen yaƙi masu ɗaukar jiragen sama guda biyu da rundunonin da ke tare da su.
Wannan runduna ta ƙunshi jiragen ruwa na yaƙi da dama, tare da jiragen sama masu kai hare-hare.
Trump da Netanyahu ne suka haɗa kai wajen fara yaƙin Iran kusan watanni tara da suka gabata, inda suka ƙaddamar da manyan hare-hare kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Kara karanta wannan
Mazan fama: Amurka ta yabawa sojojin Najeriya bayan gudanar da wani gagarumin aiki
Sai dai akwai alamun cewa lokacin da shugabannin biyu za su iya haɗa kai wajen sake ƙaddamar da wani farmaki na iya ƙurewa.
Netanyahu na fuskantar barazanar rasa kujerarsa
Netanyahu na iya rasa kujerar firaminista a cikin makonni masu zuwa sakamakon yadda aka gudanar da zaɓen ƙasar Isra’ila a ƙarshen watan jiya.
A ɓangaren Amurka kuwa, jam’iyyar Republican ta Trump za ta rasa iko da majalisun dokokin ƙasar guda biyu a watan Janairu. Hakan zai bai wa abokan hamayyarsa damar yin tasiri sosai kan batun kuɗaɗen yaƙin.
Tashar ta ce ofishin Netanyahu da rundunar sojin Isra’ila ba su mayar da martani kan tambayoyinta game da shirin sake kai hare-hare kan Iran ba. Idan aka aiwatar da shirin, wannan zai zama karo na uku na manyan faɗace-faɗace tsakanin ɓangarorin.
Fadar White House da rundunar sojin Amurka ma sun ƙi yin tsokaci kan matakin da gwamnatin Trump ke nazari a kai.
Sai dai kwamandojin sojin Amurka sun daɗe suna bayyana cewa a shirye suke su aiwatar da duk wani umarni da Trump ya bayar.
Majiyoyin sun bayyana cewa kasancewar kayan aikin sojin Amurka a yankin, za a iya fara sabon farmaki cikin kwanaki biyu zuwa huɗu idan Trump ya ba da umarni.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu

Source: Getty Images
Amurka ta kafa sabuwar runduna kan Iran
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Amurka ta sanar da kafa sabuwar rundunar soji domin dakile safarar makamai da wasu kayayyakin da aka kakaba wa kasar Iran takunkumi ta kan iyakokinta da kuma tekun Caspian.
Rundunar mai suna Task Force Iron Gate za ta kasance ne a birnin Tampa da ke jihar Florida, inda za ta hada kai da sauran hukumomin gwamnatin Amurka wajen aiwatar da aikin.
Asali: Legit.ng

