Shugaba Tinubu Ya Garzaya Fadar Babban Sarki a Najeriya, an Masa Addu'o'i

Shugaba Tinubu Ya Garzaya Fadar Babban Sarki a Najeriya, an Masa Addu'o'i

  • Rahoto ya nuna cewa shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, a fadarsa da ke Iga Idunganran a Legas
  • A yayin ziyarar, Sarkin ya yi wa Tinubu da gwamnatinsa addu'a tare da ba shi shawarwari kan al'amuran ƙasa da jin daɗin ’yan Najeriya
  • Tinubu ya samu tarba daga iyalan masarautar da kuma dimbin mazauna Legas da suka fito kan tituna domin tarbarsa yayin da ayarin motocinsa ke isa fadar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Legas – Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci Sarkin Legas, Oba Rilwan Akiolu, a fadarsa da ke Iga Idunganran, tsibirin Legas, ranar Lahadi.

Ziyarar ta ba shugaban damar karɓar addu'a da shawarwari daga basaraken gargajiyar kan tafiyar da gwamnatinsa da kuma al'amuran ƙasar.

Kara karanta wannan

Duk da matsalar da ake ciki da Wike, APC ta bayyana shirin da ta yi saboda Tinubu

Tinubu da sarkin Legas
Shugaba Bola Tinubu a fadar Sarkin Legas. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Tashar TVC ta wallafa bidiyon ziyarar shugaban kasar zuwa fadar Oba na Legas a wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Lahadi.

Sarki ya yi wa Tinubu addu'a

A yayin ziyarar, Oba Akiolu ya yi wa Tinubu, gwamnatinsa da Najeriya addu'a, yana roƙon Allah Ya ba su basira wajen tafiyar da mulki tare da tabbatar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.

Sarkin ya kuma ba shugaban shawara kan wasu batutuwan da suka shafi Najeriya da jin daɗin ’yan ƙasar domin jama'a su samu saukin rayuwa.

Jama'a sun fito tarbar Tinubu

Rahotanni sun ce lokacin da ayarin motocin shugaban ke dosar fadar, magoya bayan jam'iyyar APC da sauran masu fatan alheri sun yi cincirindo a yankunan Marina da Isale Eko.

Rahoton Vanguard ya nuna cewa mazauna yankin sun yi ta murna tare da nuna farin ciki da zuwan shugaban zuwa tsibirin Legas, lamarin da ya sanya wurin ya kasance cikin yanayi na shagali.

Kara karanta wannan

Tsohon ɗan Majalisa ya bukaci Atiku da Peter Obi su janyewa Tinubu, ya kawo hujja

Tinubu ya tafi da manyan jami'ai

Tinubu ya samu rakiyar Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, da shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

Haka kuma, wasu jiga-jigan APC, abokan siyasar shugaban da sauran manyan baki sun kasance cikin waɗanda suka raka shi zuwa fadar Sarkin Legas.

Motocin tallata Bola Tinubu
Wasu motocin tallata shugaba Bola Tinubu a Nasarawa. Hoto: Gov Abdullahi A. Sule
Source: Facebook

Ziyarar ta kasance wani ɓangare na ci gaba da ganawar Tinubu da manyan ’yan Najeriya, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki tun bayan dawowarsa Legas daga hutun aiki.

Ga bidiyon ziyarar shugaban kasar a kasa:

'Tinubu zai iya nasara'

A wani labarin, mun ruwaito cewa mujallar The Economist ta bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya samun damar sake lashe zaɓen 2027 duk da matsalolin da ake fuskanta da kuma rashin gamsuwar wasu ’yan Najeriya da gwamnatinsa.

Mujallar ta danganta matsayar da wasu abubuwa da suka shafi tsarin siyasar Najeriya, ciki har da ƙarfin jam'iyyar da ke kan mulki da kuma rabuwar kan ’yan adawa.

Sai dai wannan matsaya ta haifar da martani daga wasu ’yan siyasa da kungiyoyin adawa, waɗanda suka ƙalubalanci ra'ayin mujallar kan yiwuwar sake zaɓen Tinubu a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng