Nadin Sarauta
Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya yi zaman fada a Kano duk da jibge jami'an tsaro. Yan sanda sun cika fadar Kano da Bichi yayin da ake shirin raka sarkin Bichi.
Shugaba Bola Tinubu ya jawo aikin sama da Naira triliyan 4 a masarautar Borgu da ta ba shi Jagaba. Kamfanin Brazil zai zuba hannub jarin $2.1bn a Borgu.
Yayin da rigimar sarauta ta kara kamari, mazauna yankin Kajola a karamar hukumar Ero sun maka gwamnatin jihar a kotu kan kakaba masu wani basarake.
Olubadan na jihar Oyo, Oba Owolabi Akinloye Olakulehin ya dakatar da nadin sarauta da aka shirya yi a yau Alhamis 28 ga watan Nuwambar 2024 a birnin Ibadan.
Ciroman Kano, Aminu Muhammadu Sanusi II ya ziyarci jihar Jigawa. Ya gana da gwamna Umar Namadi da sarkin Dutse, Hamim Nuhu Muhammad Sanusi a Garu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya roki alfarmar sarakunan gargajiya kan wayar da kan al'umma inda ya bayyana muhimmancinsu a tsare-tsaren gwamnati.
Sarkin Beni da ke ƙaramar hukumar Shira a Bauchi, basarake mafi daɗewa a kan sarauta, Muhammadu Inuwa ya riga mu gidan gaskiya a asibitin FMC a Azare.
Gwamna Monday Okpebholo na Edo ya rushe wasu sababbin masarautu da tsohon gwamna, Godwin Obaseki ya samar inda ya dawowa Oba na Benin, Oba Ewuare II martabarsa.
Mai alfarma sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III ya gwangwaje gwamnan jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris da sarautar gwarzon daular Usmanuyya saboda taimakon jama'a.
Nadin Sarauta
Samu kari