Fadan Manya: Bayan Karyata Shi, Sule Lamido Ya Sake Taso Kashim Shettima a Gaba

Fadan Manya: Bayan Karyata Shi, Sule Lamido Ya Sake Taso Kashim Shettima a Gaba

  • Sule Lamido ya buƙaci Kashim Shettima ya riƙa yin magana cikin natsuwa da sanin girman muƙaminsa na mataimakin shugaban ƙasa
  • Tsohon gwamnan ya ce Shettima na buƙatar amfani da matsayinsa wajen kare muradun Arewa maimakon shiga muhawarar da za ta rage darajar ofishinsa
  • Sule Lamido ya soki wasu kalaman da Shettima ya taɓa yi kan Yemi Osinbajo, Atiku Abubakar da Ahmad Lawan, yana mai cewa bai kamata a raina tsofaffin shugabanni ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dr Sule Lamido, ya shawarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da ya riƙa taka-tsantsan wajen furta kalamansa a bainar jama’a.

Sule Lamido ya buƙaci Shettima ya nuna natsuwa, sanin ya kamata da kuma girman da ake buƙata daga mutumin da ke riƙe da babban muƙami a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Jonathan ya fito da sabuwar magana kan dalilinsa na mika mulki ga Buhari cikin sauki

Sule Lamido ya soki Shettima
Sule Lamido da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima Hoto: Mustapha Sule Lamido, Stanley Kingsley Nkwocha
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da ’yan jarida jim kaɗan bayan ƙaddamar da kamfen ɗin PDP a Dutse, babban birnin jihar Jigawa, ranar Laraba, 18 ga watan Nuwamban 2026.

Lamido ya ce Shettima na buƙatar ƙarin natsuwa

Tsohon gwamnan ya amince da cewa Shettima mutum ne mai basira, iya magana da kuma kyawawan halaye. Sai dai ya ce waɗannan abubuwa kaɗai ba su wadatar ba wajen nuna ƙwarewar shugabanci.

A cewarsa, mataimakin shugaban ƙasar na buƙatar fahimtar girman muƙaminsa da nauyin da ke kansa a matsayinsa na mutum na biyu mafi girma a siyasar Najeriya, kuma ɗaya daga cikin manyan shugabannin Arewa.

“Ya kamata ya fahimci cewa shi ne mutum na farko a Arewa. Duk abin da ya faɗa, mutane za su ɗauke shi da muhimmanci.
“Ya kamata ya daina yawan barkwanci, domin ina ganin bai fahimci cikakken nauyin da ke tattare da muƙamin da yake riƙe da shi ba.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

Ya kuma buƙaci Shettima da ya yi amfani da matsayinsa wajen inganta muradun al’ummar Arewa, maimakon shiga musayar kalamai a bainar jama’a da ka iya rage darajar ofishinsa.

Ya soki kalaman Shettima kan Osinbajo da Atiku

Lamido ya kuma nuna rashin jin daɗinsa kan wasu kalaman da mataimakin shugaban ƙasar ya taɓa yi game da fitattun ’yan siyasa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Yemi Osinbajo, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan.

Ya tuna cewa Shettima ya taɓa kiran Osinbajo mai sayar da ƙanƙara, yayin da ya kira Atiku mai aikin duba tsafta watau dan duba gari.

Tsohon gwamnan ya bayyana irin waɗannan kalamai a matsayin rashin girmamawa ga mutanen da suka taɓa riƙe manyan muƙamai a Najeriya.

Ya ce ya kamata Shettima ya riƙa la’akari da yadda jama’a za su fahimci kalamansa da kuma ma’anar da za su ɗora musu.

“Ya kamata ya fi nuna natsuwa kuma ya wuce yawan barkwanci. Ya kamata ya yi tunani kan abin da zai faɗa, yadda mutane za su kallonsa da kuma ma’anar da za su fahimta daga kalamansa, maimakon yin magana ba tare da taka-tsantsan ba.”

Kara karanta wannan

Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya

Ya tunatar da Shettima girman muƙaminsa

Sule Lamido ya jaddada cewa muƙamin mataimakin shugaban ƙasa na buƙatar babban matakin ɗaukar nauyi da kuma mutunta darajar ofishin.

Ya buƙaci Shettima ya gyara yadda yake gudanar da kansa a bainar jama’a, tare da nuna girmamawa ga muƙamin da yake wakilta.

A cewarsa, akwai nauyi mai girma da ke tattare da wannan muƙami, don haka bai kamata a ɗauke shi da wasa ba.

Ya ƙara da cewa ya kamata mataimakin shugaban ƙasar ya tashi tsaye wajen cika abubuwan da ake sa ran zai yi bisa matsayinsa.

Sule Lamido ya ba Shettima shawara
Sule Lamido da Ahmed Makarfi a wajen kamfen din PDP a Jigawa Hoto: Mustapha Sule Lamido
Source: Facebook

Kashim Shettima ya soki Amaechi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kashim Shettima, ya soki Rotimi Amaechi, kan zargin cewa marigayi Muhammadu Buhari ya yi masa alƙawarin tikitin takarar shugaban ƙasa na APC a 2023, amma daga baya ya karya alƙawarin.

Shettima ya bayyana zargin na tsohon ministan sufurin a matsayin magana marar dacewa da rashin girmamawa ga marigayi Buhari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng