Sarkin Benin ya nesanta kansa daga zagin Buhari da Oshiomhole

Sarkin Benin ya nesanta kansa daga zagin Buhari da Oshiomhole

- Oba Ewuare II, sarkin Benin ya karyata batun wakilta wani domin ya zagi shugaban kasa Muhammadu Buhari, Adams Oshiomhole da Kaftin Hosa Okunbor

- Ya alakanta bidiyon zagin shugabannin da ke yawo a shafukan zumunta ga aikin makiya

- An dai zargi sarkin da kunduma zagi ga shugaban kasa Muhammadu

Sarkin Benin, Oba Ewuare II ya musanta wakilta wani don zagin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Adams Oshiomhole da Kaftin Hosa Okunbor.

Basaraken ya ce zagin shugaban kasa da kuma wadannan 'ya'yan jihar Edo da ke yawo a kafafen sada zumuntar zamani aiki ne na makiya kuma masu son tada zaune tsaye.

Sarkin ya yi martanin ne a kan wani bidiyo da wani Eranomigho Edegbe da ke ikirarin zama hadinsa ya fitar.

A bidiyon an ji basaraken na kunduma zagi ga shugaban kasa Muhammadu.

Oban Benin ya nesanta kansa daga zagin Buhari da Oshiomhole
Oban Benin ya nesanta kansa daga zagin Buhari da Oshiomhole Hoto: Pulse
Asali: UGC

Amma kuma basaraken, a wata takarda da sakataren sa ya sa hannu, Frank Irabor, ya ce: "Mun yi Allah wadai da mummunan harin makiya a kan nagartar shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu mutane da ake dangantawa garemu.

"Domin karin bayani kai tsaye, Sarkin Benin na sanar da cewa daga bidiyon har abinda ya kunsa ba daga garesa bane kuma bashi da hannu a ciki," yace.

Ya yi bayanin cewa Oshiomhole da Okunbor wadanda tamkar 'ya'ya suke ga fadar, ba wai mutunta al'ada kadai suke ba, suna bada gudunawarsu wurin zaman lafiyar jihar.

KU KARANTA KUMA: PDP ta bai wa mataimakin Akeredolu muhimmiyar shawara

A yayin da yake bukatar ban hakuri daga Eranomigho don gujewa matakin da zai dauka, ya ja kunnen duk wani da ke fatan bata wa masarautar suna da ya guji tsinuwar magabata da kuma tsohuwar karagar masarautar Benin.

A wani labari na daban, mun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta shawo kan matsalar tsaro da ya addabi yankin arewa ta yadda noma zai dawo.

A wata takarda da Atiku ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce idan har ba a shawo kan matsalar tsaro ba, ta yuwu hakan ya zama babbar matsala ga kasar baki daya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng