Najeriya Za Ta Shiga Tarihi a Duniya kan Yawan Al'umma Mabiya Musulunci
- Wani rahoto na ya nuna cewa Najeriya za ta kasance ƙasa ta uku mafi yawan Musulmi a duniya nan da shekaru kadan
- An yi hasashen cewa Musulmi za su wuce Kiristoci a yawan mabiya a duniya nan da shekarar 2070
- Pakistan ce za ta kasance ta farko, sai Indiya da Najeriya, yayin da Indonesia za ta koma ta huɗu a jerin ƙasashen
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Najeriya na shirin zama ƙasa ta uku mafi yawan al'ummar Musulmi a duniya nan da shekarar 2035, kamar yadda wani sabon rahoto ya nuna.
Rahoton ya kuma yi hasashen cewa addinin Musulunci zai zarce Kiristanci, wanda ya daɗe yana kan gaba a matsayin addini mafi yawan mabiya a duniya.

Source: Original
Cibiyar Bincike ta Pew (Pew Research Centre) da TheCable bibiya, ta fitar da wannan hasashe a cikin wani rahoto mai taken Future of World Religions, wanda aka wallafa ranar Laraba.

Kara karanta wannan
An ba 'yar Amurka Dala miliyan 4.5 bayan ta yi hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya ta bayyana
Najeriya za ta shiga sahun ƙasashen Musulmi
A cewar rahoton, Pakistan ce za ta kasance ƙasa mafi yawan Musulmi a duniya nan da shekarar 2035, sai Indiya a matsayi na biyu.
Najeriya ce za ta kasance ta uku, yayin da Indonesia, wadda a halin yanzu ita ce ƙasa mafi yawan Musulmi a duniya, za ta koma ta huɗu.
Majiyoyi sun bayyana cewa ƙaruwa a yawan haihuwa na daga cikin manyan abubuwan da suke taimaka wa wajen karuwar al'ummar Musulmi a duniya.
Dalilan ƙaruwa a yawan Musulmi
Binciken ya nuna cewa tsakanin shekarun 2020 zuwa 2025, matan Musulmi sun haifi matsakaicin yara 3.1, idan aka kwatanta da yara 2.5 ga matan Kirista.
Haka kuma, sauran matan da ba Musulmi ko Kiristoci ba sun haifi matsakaicin yara 1.6 a wannan lokaci.
Rahoton ya bayyana cewa ana buƙatar matsakaicin yara 2.1 ga kowace mace domin maye gurbin yawan al'ummar da ke mutuwa da waɗanda za a haifa.

Source: Twitter
Amurka za ta rasa rinjayen Kiristoci
Har ila yau, rahoton ya yi hasashen cewa Amurka za ta rasa matsayinta na ƙasa mai rinjayen Kiristoci, duk da cewa Kiristoci za su ci gaba da kasancewa mafi yawan mabiya addini a ƙasar.
Haka kuma, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC) za ta zarce Amurka wajen yawan Kiristoci, ta zama ƙasar da ta fi kowace ƙasa yawan mabiya addinin Kiristanci.
Sai dai cibiyar ta jaddada cewa hasashen ya dogara ne da ci gaba da yanayin haihuwa, mace-mace da sauya addini kamar yadda suke a halin yanzu.
Ta kuma yi gargaɗin cewa yaƙe-yaƙe, bala'o'i da sauye-sauyen tattalin arziki na iya sauya waɗannan hasashe, cewar Punch.
Musulunci zai zarce addinin Kiristanci a duniya
A baya, an ji cewa wani sabon bincike ya nuna cewa Musulunci na iya zama addini mafi yawan mabiya a duniya, inda zai zarce Kiristanci nan da shekarar 2035.
Cibiyar bincike ta Pew ta ce yawan Musulmi zai ci gaba da ƙaruwa cikin sauri fiye da na Kiristoci a shekaru masu zuwa.
Binciken ya yi nazari kan ƙasashe da yankuna 201, inda ya yi hasashen sauyin yawan mabiya addinai daban-daban daga 2020 zuwa 2070.
Asali: Legit.ng
