2027: Tinubu Ya Sake Neman Alfarmar Yan Najeriya yayin Kamfen a Kaduna
- Shugaba Bola Tinubu ya roƙi ’yan Najeriya su sake ba shi wa’adi na biyu a 2027 domin ci gaba da ayyukan alheri
- Gwamnan Kaduna, Uba Sani, da Sanata Abdulaziz Yari sun ce Arewa za ta mara wa Tinubu baya, bisa ayyukan gwamnati a tsaro, ilimi da gine-gine
- Sai dai Atiku Abubakar ya zargi Tinubu da ƙoƙarin ɗora wa ’yan adawa alhakin yunwa da talauci, yayin da ADC ta soki gangamin APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya roƙi ’yan Najeriya da su sake ba shi dama domin ya ci gaba da ayyukan da ya fara.
Shugaba Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa ta samar da wadata, ci gaba, farfaɗowar tattalin arziki da damarmaki.

Source: Facebook
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyar APC a Kaduna ranar Asabar, cewar rahoton Tribune.
Zargin yan adawa da Tinubu ya yi
Shugaban ya zargi abokan hamayyarsa da dogaro da ƙiyayya maimakon gabatar da ingantattun hanyoyin magance matsalolin ƙasar.
Ya buƙaci magoya bayansa su zaɓi APC a dukkan matakai, ciki har da shugaban ƙasa, gwamnonin jihohi, Majalisar Tarayya da majalisun dokokin jihohi.
Tinubu ya kuma yaba wa gwamnonin APC bisa abin da ya bayyana a matsayin ƙoƙarinsu na samar da ci gaba a jihohinsu.
Haka kuma, ya zargi ’yan adawa da haddasa yunwa da talauci a ƙasar, sannan suna sukar gwamnatinsa a kan matsalolin. Ya dage cewa gwamnatinsa na ƙoƙarin magance ƙalubalen tattalin arzikin da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Ya ce:
“Ina jin abokan hamayyata suna magana kan yunwa da talauci. Wa ya haddasa su? Su ne. Sun haddasa yunwa, sun haddasa talauci. Muna ƙoƙarin kawar da su."
Ya buƙaci ’yan Najeriya su goyi bayan manufofin gwamnatinsa, yana mai cewa tana ƙoƙarin tabbatar da biyan albashi a kai a kai da samar da damarmaki ga jama’a.
Tinubu ya kuma kira ga masu cancantar kaɗa ƙuri’a da su tabbatar suna da katin zaɓensu na dindindin (PVC), tare da shiga zaɓe mai zuwa, cewar Punch.

Source: Twitter
'Za mu sakawa Tinubu' - Uba Sani
Tun da farko, a jawabinsa na maraba, gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce al’ummar Arewacin Najeriya za su saka wa Tinubu saboda ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a yankin.
Gwamnan ya tuna da ziyarar Tinubu zuwa Birnin Gwari a lokacin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na 2023, lokacin da yankin ke fama da rashin tsaro. Ya ce shugaban ƙasar ya cika alƙawuran da ya ɗauka na gina hanya da inganta tsaro.
Shettima ya nemi alfarmar yan Najeriya
Mun ba ku labarin cewa mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya buƙaci masu zaɓe a Arewa su haɗa kai domin ganin Bola Tinubu ya sake lashe zaɓe.
Shettima ya tuna yadda Tinubu ya goyi bayan Atiku Abubakar a 2007 da marigayi Muhammadu Buhari a zaɓen 2015 da 2019.
Ya bayyana jami’o’i, ayyukan tituna da hanyoyin jirgin ƙasa da bututun iskar gas a matsayin wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa.
Asali: Legit.ng

