‘Yan Najeriya Na Kaunar Tinubu ba Kamar yadda Ake Gani a Kafafen Sadarwa ba’
- Ministan Yaɗa Labarai, Mohammed Idris, ya ce ’yan Najeriya na son Tinubu, yana mai kira gare su su yi watsi da labaran sada zumunta
- Idris ya bayyana yawan mutanen da suka halarci gangamin APC a Kaduna a matsayin alamar goyon bayan Tinubu da manufofinsa
- Ministan Ma’adanai, Dele Alake, ya ce ’yan Najeriya sun fara ganin amfanin sauye-sauyen gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Mohammed Idris, ya yaba da gangamin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓe a Kaduna.
Idris ya ce hakan ya nuna tasirin shugaban ƙasa a zukatan yan Najeriya yayin da 2027 ke karatowa.

Source: Facebook
Idris ya bayyana hakan ne ranar Asabar a filin gangamin da ke Kaduna, inda ya nuna kwarin gwiwarsa kan farin jinin Tinubu da goyon bayan manufofin gyaran tattalin arzikin gwamnatinsa, cewar Punch.
Minista ya ce ana kaunar Tinubu a Najeriya
Ya bayyana yawan mutanen da suka halarci gangamin a matsayin alamar karɓuwar shugaban ƙasa a tsakanin ’yan Najeriya, musamman magoya bayan da suka yi imani da manufofinsa.
Idris ya buƙaci ’yan Najeriya su wuce labaran da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta da sukar ’yan adawa, yana mai cewa yawan mutanen da suka halarci gangamin ya nuna goyon bayan da ake bai wa Tinubu.
Ya ce:
“Mun daɗe muna faɗin haka: ku yi watsi da duk labaran da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta, ku yi watsi da duk maganganun ’yan adawa. ’Yan Najeriya na son Asiwaju.”
Ya bayyana Kaduna a matsayin muhimmiyar cibiyar ƙaddamar da kamfen ɗin, yana mai cewa birnin na da muhimmanci a tarihi saboda kasancewarsa tsohuwar babban birnin Arewacin Najeriya.

Source: Facebook
Yan Najeriya na fahimtar manufofin Tinubu
A cewarsa, kasancewar magoya baya daga mabambantan ɓangarorin siyasa ya nuna shirye-shiryen haɗa kai domin goyon bayan Tinubu da manufofin gyaran tattalin arzikin gwamnatinsa.
Idris ya ce ’yan Najeriya na ƙara fahimtar amfanin da manufofin gwamnati za su iya samarwa da kuma damar farfaɗowar tattalin arziki, cewar Vanguard.
Ya amince cewa ƙasar na fuskantar ƙalubale, amma ya nuna kyakkyawan fata cewa sauye-sauyen gwamnatin za su inganta yanayin tattalin arzikin ƙasar nan a nan gaba.
“Akwai ƙalubale a wannan lokaci, amma muna barin wannan hali a baya. Muna ƙarfafa ci gaban da aka samu, kuma Najeriya za ta samu ci gaba.”
- in ji ministan.
Ya ce gwamnati na ci gaba da ƙoƙarin kai ƙasar ga bunƙasar tattalin arziki, inganta rayuwar jama’a da samun ci gaba mai ɗorewa.
Idris ya bayyana yanayin da aka samu a gangamin a matsayin abin ƙarfafa gwiwa ga kamfen ɗin neman wa’adi na biyu na shugaban ƙasa.
Uba Sani ya yi wa Tinubu alkawari
Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya ce al’ummar Arewa za su saka wa Shugaba Bola Tinubu da ƙuri’unsu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Uba Sani ya ce gwamnatin Tinubu ta samu nasarori wajen gine-gine, tsaro, ilimi da noma, ciki har da ayyukan hanyoyi da sake buɗe makarantu.
Gwamnan ya buƙaci ’yan Arewa su auna Tinubu bisa ayyukansa, ba ƙabilanci ko yankin da ya fito ba, tare da gargaɗin APC kan amfani da AI.
Asali: Legit.ng

