"Tinubu Bai Fi Ya Lashe Jihohi 2 ba"; An Yi Sabon Hasashe kan Zaben Shugaban Kasa
- Hakeem Baba-Ahmed ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai sha kaye a zaɓen 2027 idan aka gudanar da zaɓen cikin ’yanci da adalci
- Shugaban na PRP ya ce rashin gamsuwar ’yan Najeriya kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da sauran matsaloli na iya janyo wa APC rasa mulki
- Ya bayyana cewa hasashensa ya samo asali ne daga hulɗar jam’iyyarsa da talakawa da kuma sauraron ra’ayoyinsu, ba wai zato kawai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar People’s Redemption Party (PRP) na ƙasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Tinubu zai sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 idan aka gudanar da zaɓen cikin ’yanci da adalci.
Baba-Ahmed ya ce rashin gamsuwar da jama’a ke nunawa kan gwamnatin Tinubu na iya jawo wa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) rasa ikon mulki.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu

Source: Facebook
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a wata hira da gidan talabijin na Arise News a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamban 2026.
Ya kuma zargi gwamnatin Tinubu da mayar da hankali kan yadda za ta ci gaba da riƙe mulki, maimakon magance matsalolin tattalin arziki da tsaro da ke addabar ƙasar.
A cewarsa, ’yan Najeriya na ƙara nuna takaici kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da sauran matsalolin da iyalai ke fuskanta.
Dalilin da ya sa yake ganin Tinubu zai sha kaye
Shugaban PRP ya ce ra’ayinsa ya samo asali ne daga hulɗar da jam’iyyarsa ke yi da talakawa da kuma irin halin da suke ciki a ƙarƙashin gwamnatin yanzu.
“Idan aka gudanar da zaɓe cikin ’yanci da adalci, Shugaba Tinubu, ina sake nanatawa, ba zai lashe wannan zaɓe ba.
“’Yan Najeriya baki ɗaya, ba Arewa maso Yamma kaɗai ba, za su ƙi shi saboda bai yi wani aiki da ya kai kusa da abin da suke tsammani daga gare shi ba.
“Gwamnatin Tinubu ta fi mayar da hankali kan yadda za ta ci gaba da kasancewa a kan mulki, maimakon magance matsalolin ƙasar nan.” In ji shi.
PRP ta ce tana sauraron ra’ayin talakawa
Shugaban na PRP ya jaddada cewa matsayar jam’iyyarsa ta samo asali ne daga hulɗa kai tsaye da ’yan ƙasa, ba wai hasashe kan ra’ayinsu ba.
Ya ce jam’iyyar tana hulɗa da jama’a, tana bibiyar rayuwarsu da sauraron ra’ayoyinsu domin fahimtar halin da suke ciki.
“Ba ma yin zato kawai. Muna hulɗa da su. Ba ma ba su kuɗi. Ba mu da kuɗin da APC take da shi na bai wa mutane.
“Saboda haka, muna tattaunawa da su, muna bibiyar rayuwarsu da ra’ayoyinsu, kuma muna fahimtar yadda suke kallon abubuwan da ke faruwa.” In ji shi.
Ya yi hasashen jihohin da Tinubu zai iya lashewa
Baba-Ahmed ya kuma fayyace cewa hasashen da ya yi a baya kan damar Tinubu na samun nasara a zaɓen 2027 ya shafi dukkan Najeriya, ba Arewa maso Yamma ko Arewa maso Gabas kaɗai ba.
“Na ce idan zaɓen 2027 ya kasance sahihi, cikin ’yanci da adalci, da wuya Shugaba Tinubu ya lashe fiye da jihohi biyu.

Kara karanta wannan
An hango abin da zai faru idan aka yi wa 'yan Najeriya karfa karfa kan Tinubu a 2027
“Ban ma ambaci Arewa maso Yamma ba. Na ce a faɗin ƙasar nan.” In ji shi.

Source: Facebook
APGA ta amince da tazarcen Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya miƙa tutar jam’iyyar APGA ga Shugaba Bola Tinubu a hukumance.
akan ya nuna cewa APGA ta amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin dan takarar da za ta marawa baya a zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2027.
Asali: Legit.ng
