Lamuran Siyasa 6 da Ka Iya Tasiri a Zaɓen Najeriya na Shekarar 2027
Zaɓen Najeriya na 2027 na ƙara matsowa, amma har yanzu akwai muhimman batutuwa da ba su da tabbas gabanin zaben da za a gudanar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An shirya gudanar da zaben ne a watan Janairu da kuma Faburairun shekarar 2027 da ya shafi na shugaban kasa, gwamnoni da yan majalisun jihohi da na tarayya.
Rikice-rikicen jam'iyyu da shari'o'i na ci gaba da haifar da rashin tabbas wanda ka iya sauya akalar zaben 2027 da za a gudanar.

Source: Facebook
Abubuwan da ka iya sauya alakar zaben 2027
Masana na ganin cewa dole ne a warware waɗannan matsaloli kafin fara babban zaɓen da aka tsara gudanarwa daga watan Janairun shekarar 2027, cewar rahoton BBC Hausa.
Legit Hausa ta duba wasu daga cikin abubuwan da za su iya sauya alakar zaben kafin shiga shekarar 2027.

Kara karanta wannan
2027: Malami ya gana da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam'iyyar ADC a Abuja
1. Makomar jam'iyyar ADC
Jam'iyyar ADC na fuskantar ƙalubalen shari'a da rikicin shugabanci, lamarin da ya sa har yanzu ba a tabbatar da makomarta gaba ɗaya ba.
A baya wata kotu ta umarci INEC ta soke rijistar ADC da wasu jam'iyyu, tana mai cewa sun gaza cika wasu tanade-tanaden doka.
Sai dai INEC ta ƙalubalanci hukuncin, kuma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta dakatar da aiwatar da shi har sai an kammala shari'ar.
Haka kuma ADC na fama da rikicin shugabanci tsakanin ɓangaren David Mark da na Nafi'u Bala Gombe kan wanda ya dace ya jagoranci jam'iyyar.
Daga baya INEC ta mayar da shugabannin ƙarƙashin David Mark bayan wani hukuncin Kotun Ƙoli, amma ana ci gaba da sauraron asalin ƙarar.
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi hukunci a shari'ar da ke kalubalantar shugabancin jam'iyyar ADC.
Kotun ta tabbatar da shugabancin Sanata David Mark a jam'iyyar ADC mai adawa duk da cewa Nafiu Bala a ce shari'ar ba ta shafe su ba.

Source: Twitter
2. Shari'ar INEC da wasu jam'iyyu
INEC ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da ya soke ikonta na sanya wa'adin gabatar da jerin sunayen mambobi da 'yan takarar jam'iyyu.
Tun farko hukumar ta umarci jam'iyyu su miƙa rajistar mambobinsu kafin watan Mayun 2026 tare da kammala zaɓen fidda gwani cikin wa'adi.
Jam'iyyar Youth Party ta ƙalubalanci wannan mataki a kotu, tana cewa doka ta ba jam'iyyu damar gabatar da bayanansu har watan Satumba.
Kotun ta yanke hukunci a madadin jam'iyyar, amma INEC ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara domin neman a soke hukuncin.
Masana sun yi gargadin cewa idan ba a warware wannan shari'a cikin lokaci ba, za ta iya shafar shirye-shiryen babban zaɓen 2027.

Source: Facebook
3. Fitar da sunayen 'yan takara
Jam'iyyu da dama na fama da ƙalubalen kammala fitar da sunayen 'yan takararsu da kuma miƙa su ga INEC cikin wa'adin da aka tanada.
A APC, wasu da suka yi nasara a zaɓen fitar da gwani sun koka cewa har yanzu ba a ba su takardun shaidar nasara ba.
Shugaba Bola Tinubu ne kaɗai aka tabbatar an ba takardar shaidar lashe zaɓen fitar da gwani kafin daga baya a ba yan majalisun tarayya da wasu gwamnoni.
Jam'iyyar APC ta ce jinkirin ya samo asali ne daga ƙoƙarin warware korafe-korafe domin tabbatar da an yi wa kowa adalci.
Ita ma NDC da sauran jam'iyyun adawa na fuskantar irin wannan ƙalubale sakamakon rashin gamsuwar wasu 'yan takara da sakamakon zaɓe.
4. Haɗewar 'yan adawa
Masu sharhi na ganin akwai yiwuwar jam'iyyun adawa su sake haɗuwa idan suna son ƙalubalantar APC a zaɓen shugaban ƙasa.
Tun farko fitattun 'yan siyasa irin su Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Kwankwaso, Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai sun haɗa kai.
Sai dai rikicin shugabanci da rashin jituwa ya sa haɗakar ta fara fuskantar tangarɗa, lamarin da ya haifar da rabuwar kawuna.
Wasu na ganin rarrabuwar wata dabara ce ta siyasa, yayin da wasu ke ganin har yanzu akwai yiwuwar su sake haɗewa.
An yi wani taro a Ibadan da ya nuna 'yan adawa za su tsaida 'dan takara guda a 2027.
5. Takarar Goodluck Jonathan
Wani ɓangaren PDP ƙarƙashin Tanimu Turaki ya bayyana Goodluck Jonathan a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar.
Sai dai wani ɓangaren PDP mai goyon bayan Nyesom Wike ya tsayar da Sandy Onor a matsayin ɗan takararsa.
Har yanzu babu tabbacin ko INEC za ta amince da takarar Jonathan saboda rikicin shugabanci da ke cikin jam'iyyar PDP.
Kotun Ƙolin Najeriya ta bayyana cewa Jonathan na da damar sake tsayawa takarar shugaban ƙasa idan ya cika sharuddan doka.

Source: Twitter
6. Makomar jam'iyyar NDC
Jam'iyyar NDC ma na fuskantar ƙalubalen shari'a bayan da aka nemi kotu ta soke rijistarta saboda zargin rashin cika sharuddan doka.
Dr. Umar Ardo ne ya shigar da ƙarar, yana mai cewa jam'iyyar ba ta bi duk matakan da kundin tsarin mulki ya tanada ba.
Tun farko wata kotu ce ta umarci INEC ta yi wa NDC rijista bayan hukumar ta ƙi amincewa da buƙatarta.
Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Lokoja, jihar Kogi, ta soke hukuncin da ta yanke a baya a game da rajistar jam'iyyar NDC.
Kotun dai ta soke hukuncin wanda ta yanke a ranar 10 ga watan Disamba, 2025, wanda ya umarci hukumar zaɓe ta INEC da ta yi rajistar jam'iyyar NDC.
Mark: Nafiu Bala ya magantu kan hukuncin kotu
An ji cewa Hon. Nafi'u Bala Gombe ya ce hukuncin kotun da ya amince da jagorancin David Mark bai shafi ƙarar da tsaginsu ya shigar ba.
Ya bayyana dalilin da 'dan majalisa, Leke Abejide, ya gaza samun nasara a karar da ya shigar wanda ake ta magana a kai.
Nafi'u Bala Gombe, wanda ke takaddama da halaccin su Davida Mark ya kuma 'karyata cewa an dora sunayen su Atiku Abubakar a manhajar INEC.
Asali: Legit.ng



