Yadda aka Dukufa da Addu'a har aka Kifar da APC a Zaben Gwamnan Osun

Yadda aka Dukufa da Addu'a har aka Kifar da APC a Zaben Gwamnan Osun

  • Mahaifin fitaccen mawakin Najeriya, Davido, Deji Adeleke, ya ce ya yi addu’ar masu zaɓe a Osun su karɓi kuɗin da ake zargin APC ta raba, amma su zaɓi ɗan’uwansa
  • Deji ya ce ya koma ga addu’a ne bayan ya ji rahotannin makudan kuɗin da ake zargin jam’iyyar APC ta kashe domin samun kuri’u a zaɓen gwamnan Osun
  • Deji Adeleke Ya yi ikirarin cewa jam'iyyar APC ta kashe kusan Naira biliyan 60, inda ya ce an rika ba wasu masu zaɓe har N50,000 domin sayen kuri’arsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Osogbo, Jihar Osun – Mahaifin mawaki Davido, Deji Adeleke ya bayyana yadda ya dogara da addu’a domin ganin ɗan’uwansa, Gwamna Ademola Adeleke, ya sake lashe zaɓen gwamnan jihar Osun.

Ademola Adeleke, ɗan takarar jam’iyyar Accord, ya samu kuri’u 511,067, inda ya doke ɗan takarar APC, Bola Oyebamiji, wanda ya samu kuri’u 444,815.

Kara karanta wannan

Shugaban APC zai hada mutum miliyan 1 su zabi Tinubu a Ondo a 2027

Deji Adeleke a wajen taro
Mahaifin Davido, Deji Adeleke. Hoto: Davido
Source: Instagram

The Cable ta wallafa cewa Deji ya ce maimakon ƙoƙarin yin gogayya da APC wajen kashe kuɗi, ya koma ga Allah ya roƙe shi ya ba ɗan’uwansa nasara.

Addu’ar da Deji Adeleke ya yi

Deji ya ce a ranar zaɓen, bayan ya ji irin makudan kuɗin da ake zargin ana kashewa, ya shiga ɗakinsa ya yi addu’a.

Punch ta wallafa cewa ya ce:

“Ranar zaɓen, lokacin da na ji irin kuɗin da suke kashewa, sai na koma ƙaramin wurina a ɗakina, na durƙusa na yi wa Allah Maɗaukaki addu’a, na ce: ‘Allah Maɗaukaki, ka bar mutane su karɓi kuɗinsu amma su zaɓi Ademola Adeleke.’”

Deji ya yi ikirarin cewa an kashe kusan Naira biliyan 60, yana mai cewa a wasu wuraren an kai kuɗin sayen kuri’a har N50,000 kan kuri’a ɗaya.

Ya ce nasarar Ademola ba ta samu ne saboda suna da kuɗi ko wata babbar hanyar siyasa fiye da APC ba, sai dai saboda imaninsu da Allah.

Kara karanta wannan

Dalilai 5 da suka sa Adeleke ya tumurmusa APC a zaben Osun

“Dalilin da ya sa muka doke Oyetola ba wai don mun fi shi girma ba ne ko kuma mun kashe kuɗi fiye da shi,”

In ji shi.

Nasarar Ademola Adeleke ta zama karo na biyu a jere da APC ta sha kaye a zaɓen gwamnan Osun.

Gwamna Ademola Adeleke
Gwamnan Osun da ya lashe zabe karo na 2. Hoto: Osun State Government
Source: Facebook

A zaɓen 2022, Ademola ya doke tsohon Gwamnan Osun, Gboyega Oyetola, wanda yanzu yake matsayin Ministan Harkokin Ruwa da Tattalin Arzikin Teku.

Darasin da APC za ta koya a Osun

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel, ya ce APC ta gaza samun nasara a zaɓen Osun ne saboda ta kasa fahimtar yadda za ta haɗu da masu zaɓe.

Rahoto ya nuna cewa Dayo Israel ya ce jam’iyyar ta raina tasirin Ademola Adeleke, wanda wasu ‘yan siyasa ke yi wa ba’a da laƙabin “Gwamnan Rawa”.

Ya bayyana cewa rawar Adeleke, wadda wasu manyan ‘yan siyasa ke yi wa ba’a, ta taimaka masa wajen kulla alaƙa ta musamman da jama’ar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng