Kotu na Iya Kawo Cikas ga Shirin NDC na zaɓen 2027 a Jihar Kano
- Wasu daga cikin masu neman takara a NDC sun kai shigar da kara gaban kotu game da zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar a jihar Kano
- Masu ƙarar sun nemi a soke dukkannin zaɓukan fitar dda gwani da aka gudanar a ranar 28 ga Mayu, 2026 saboda wasu dalilai
- Idan kotu ta amince da buƙatunsu, NDC za ta sake gudanar da zaɓen fitar da gwani a wasu mazaɓun Kano kafin zaɓen 2027 da ke tafe
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jam'iyyar NDC na fuskantar ƙalubalen shari'a a jihar Kano bayan wasu masu neman takarar sun nuna rashin gamsuwa da zaɓen fitar da gwani sun garzaya Babbar Kotun Tarayya.
Wadanda suka nemi takarar sun bayyana cewa suna son kotun ta gaggauta soke sakamakon zaɓukan da jam'iyyar ta gudanar kafin babban zaɓen shekarar 2027.

Source: Facebook
Jaridar The Guardian ta kawo labarin cewa waɗanda suka shigar da ƙarar sun haɗa da mai neman takarar gwamna, Mukhtar Muhammad.
An shigar da NDC kara a jihar Kano
A ruwayar Arise News, sauran wadanda suka shigar da ƙaransun haɗa da Shuaib Abubakar Fagge, Mustapha Salisu Musa (Fanandas), Musa Hudu Yusuf da Mahfuz Yahuza.
Masu ƙarar sun ƙalubalanci sahihancin zaɓen fitar da gwani da aka gudanar a ranar 28 ga Mayu, 2026, suna zargin an karya Dokar Zaɓe, kundin tsarin mulkin jam'iyyar da kuma ƙa'idodin gudanar da zaɓenta.
A cikin takardun ƙarar da aka gabatar wa kotu, sun bayyana cewa tsarin da aka bi wajen shirya zaɓen na cike da kura-kurai.
Sun yi zargin cewa an bai wa mutum guda ikon sayarwa da rarraba fom ɗin nuna sha'awa da na tsayawa takara, lamarin da suka ce ya hana sauran ƴan jam'iyyar da suka cancanta samun damar shiga takara cikin adalci.
Masu neman takara sun ƙalubalanci NDC
A cewarsu, wannan tsari ya bai wa mutum guda damar tantance waɗanda za su samu fom ɗin takara da kuma shiga zaɓen fitar da gwani, abin da suka ce ya saɓa wa doka da ƙa'idodin jam'iyyar.
Masu ƙarar sun kuma shaida wa kotu cewa ba a gudanar da ingantaccen zaɓen fitar da gwani ba, suna masu zargin cewa ba a tantance wakilai, kaɗa ƙuri'a, ƙirga ƙuri'u da tattara sakamako yadda doka ta tanada ba.

Source: Facebook
Sun ce duk da kasancewarsu halastattun ƴan jam'iyyar, an hana su samun fom ɗin takara tare da hana su shiga zaɓen fitar da gwani na kujerun gwamna, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jihar Kano a mazaɓun Fagge, Tarauni da Gwale.
Saboda haka, sun roƙi kotu ta ayyana cewa NDC ta take haƙƙoƙinsu ta hanyar hana su damar yin takara cikin adalci da kuma gaza samar da daidaito tsakanin masu neman takara.
Haka kuma, sun nemi a soke takardar shaidar takarar da aka bai wa Aminu Suleiman Goro a matsayin ɗan takarar NDC na mazaɓar Fagge.
Manyan NDC sun gana
A baya mun wallafa cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya karbi bakuncin Sanata Henry Seriake Dickson a gidansa da ke unguwar Maitaima a birnin Abuja inda aka tattauna muhimman batutuwa gabanin zaben 2027.
An yi wannan haduwa ne kwanaki kadab bayan an ga tsohon gwamnan na Kano a gidan Dickson wanda shi ne jagoran NDC na kasa yayin da jam'iyyar ke fuskantar kalubalen shari'a na neman a soke mata rajista.
Sanata Kwankwaso, wanda shi ne 'dan takarar mataimakin shugaban kasa na NDC ya fadi yadda suka yi da jagoran jam'iyyar da kuma yadda aka tabbatar masa cewa an daura sunan shi a shafin hukumar INEC.
Asali: Legit.ng


