Duk da Rikicin PDP, Tsagin Turaki Ya ba Jonathan Tikitin Takarar Shugaban Kasa

Duk da Rikicin PDP, Tsagin Turaki Ya ba Jonathan Tikitin Takarar Shugaban Kasa

  • Duk da rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam’iyyar PDP, an ayyana tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa
  • An tabbatar da takarar Jonathan ne a taron musamman da aka gudanar a Abuja, inda Fred Agbedi ya karbi takardar shaidar nasara a madadinsa
  • Bayan jami’an tsaro sun hana shiga wurin taro na farko, shugabannin bangaren PDP sun sauya wuri tare da alkawarin sanar da ranar mika tuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Bangaren jam’iyyar PDP karkashin jagorancin Kabiru Turaki ya sanar da wanda zai tsaya mata takaraa zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Tsagin ya tsayar da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar domin zaben shekarar 2027.

Tsagin PDP ya ba Jonathan tikitin takarar shugaban kasa
Tsohon shugaban Najeriya kuma jigon PDP, Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Getty Images

An tabbatar da takarar Jonathan ne yayin wani taron kasa na musamman da aka gudanar a ofishin jam’iyyar da ke Area 10 a yankin Garki na Abuja, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Atiku ya girma, ya samu tikitin takarar shugaban kasa a zaben 2027

Jonathan ya samu takarar shugaban kasa

Ko da yake Jonathan bai halarci taron ba, an karbi takardar shaidar nasararsa a madadinsa ta hannun Fred Agbedi, dan majalisar wakilai daga Bayelsa.

Tun farko bangaren Turaki ya shirya gudanar da taron ne a cibiyar wuraren tarurruka, amma daga baya aka samu sauyin shiri domin sake samun wani wuri daban.

Hukumar kula da babban birnin tarayya ta FCTA ta umarci masu otal-otal da cibiyoyin taruka su yi mu’amala ne kawai da shugabannin jam’iyyun da INEC ta amince da su.

Bangaren PDP da Ministan Abuja, Nyesom Wike, ke marawa baya shi ne hukumar zabe ta kasa ta amince da jagorancinsa a hukumance.

Tsagin PDP ta ba Jonathan tikitin takarar shugaban kasa
Shugaban tsagin PDP, Kabiru Tanimu Turaki a Abuja. Hoto: Kabiru Tanimu Turaki.
Source: Twitter

Yadda ƴan sanda suka toshe hanyoyin wurin taron PDP

Da safiyar Asabar 30 ga watan Mayun 2026, jami’an ‘yan sanda sun toshe hanyoyin da ke kaiwa cibiyar A-Class Park and wuraren tarurrukare, lamarin da ya tilasta sauya wurin taron.

Daga baya jami’an jam’iyyar sun sanar da cewa an mayar da taron zuwa wani wuri daban a Area 10 domin ci gaba da gudanar da ayyukan taron.

Kara karanta wannan

Peter Obi ko Kwankwaso: NDC ta shirya tsaida 'dan takarar shugaban kasa a zaben 2027

Rahotanni sun nuna cewa bangaren PDP zai sanar nan gaba ranar da za a mika tutar jam’iyyar ga Goodluck Jonathan a hukumance.

Wannan ya biyo bayan rikicin cikin gida da PDP ke fuskanta wanda ya kara rage karfin da jam'iyyar adawa ke da shi a fadin kasar yayin da ake shirin zaben 2027.

Sule Lamido ya shawarci Jonathan kan shiga takara

A wani labarin, an ji cewa tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya yi fatali da kiraye-kirayen da ake yi wa Goodluck Jonathan kan ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027.

Sule Lamido, wanda jigo ne a PDP da ake ganin Jonathan zai iya neman takara a cikinta ya ce kiran ya samo asali ne daga takaicin halin da siyasar Najeriya ke ciki.

Tsohon gwamnan ya gargadi Jonathan da kada ya bari yabon mutane ko neman faranta masa rai ya sa ya koma siyasar jam’iyya yanzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.