Tsaro: An Gano Biliyoyin Naira da Jihohi 31 Suka Kashe a Watanni 6 Kacal

Tsaro: An Gano Biliyoyin Naira da Jihohi 31 Suka Kashe a Watanni 6 Kacal

  • Jihohi 31 sun kashe akalla N252.26bn wajen tabbatar da yaki da yan bindiga da tabbatar da tsaro a farkon watanni shida na farkon 2026
  • An gano cewa akwai jihohin da suka kashe kudi mafi yawa, kuma sun hada da Kogi da ta ce ta kashe akalla N34.67bn, sai Plateau da N23.69bn
  • Tuni aka fara neman bibiyar yadda aka kashe wadannan kudi musamman idan aka duba matsalolin tsaro da suka addabi jihohin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Jihohi 31 a Najeriya sun kashe kimanin N252.26bn wajen yaki da laifuka da magance matsalar rashin tsaro a cikin watanni shida na farkon shekarar 2026.

Sai dai wannan kashe kudi mai yawa ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun kashe-kashe, garkuwa da mutane, ta'addanci da hare-haren 'yan bindiga a sassa daban-daban na kasar.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Muhimman abubuwa 8 da ya kamata kowane mai katin zabe ya sani

Gwamnoni sun kashe makudan kudi a kan rashin tsaro
Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya a wurin taro Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Jaridar Punch ta tattaro alkaluma daga bayanan kasafin kudi daga Janairu zuwa Yuni 2026, ya nuna cewa jihar Kogi ce ta fi kashe kudi, inda ta kashe N34.67bn. Wannan ya kai kashi 13.74 na kudaden da aka tattara a bayanan.

Tsaro: Abin da jihohin Najeriya suka kashe

Jihar Plateau ta zo ta biyu da N23.69bn, yayin da Bauchi ta kashe N22.35bn. Jihohin uku gaba daya sun kashe kusan N80.70bn, wato kashi 32 na jimillar kudaden tsaron da aka samu a bayanan.

Bayelsa ta kasance ta hudu da N17.49bn, sai Ekiti da N14.83bn da Anambra da N13.40bn. Sokoto ta kashe N11.27bn, yayin da Ondo da Kaduna suka kashe N10.54bn da N10.37bn.

Sai jiar Kebbi ta kashe N10.14bn, Adamawa N9.95bn, Zamfara N9.07bn, Borno N8.29bn, Kano N8.26bn, sannan Katsina N7.21bn.

An samu karin kashe kudin tsaro

Bayanan sun nuna cewa kudaden tsaro sun karu sosai idan aka kwatanta da shekarar 2025. Jimillar kudaden jihohin da aka samu bayanansu ta karu daga N75.84bn zuwa N252.26bn.

Kara karanta wannan

Hankalin Tinubu ya koma kan matatun mai bayan karɓar tawagar NUPENG

Kudaden tsaro na musamman da sauran abubuwan da suka shafi tsaron cikin gida sun karu daga N47.67bn zuwa N135.61bn. Haka kuma, kudaden ma'aikatun tsaro da masu ba gwamnati shawara kan tsaro sun karu zuwa N42.15bn.

Jihar Kogi ce a kan gaba wajen kashe kudi don tabbatar da tsaro
Taswirar jihar Kogi a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sai dai wasu masana sun ce bai kamata gwamnoni su ware makudan kudade kan tsaro ba tare da tsayayyen tsari da hanyar auna sakamakon kashe kudin ba.

Tsohon Mataimakin Sufeto-Janar na ’Yan Sanda, Wilson Inalegwu, ya bukaci gwamnonin su samar da tsarin aikin ’yan sanda na shekara, wanda zai bayyana matsalolin tsaro, kudaden da ake bukata da kuma sakamakon da ake sa ran samu.

An tattauna tsaron Najeriya a Amurka

A baya, mun ruwaito cewa tawagar kasashen Najeriya da Amurka sun fara sabon zagaye na tattaunawa kan batun tsaro da yaki da ta’addanci wanda Donald Trump ke ganin ya fi shafar Kiristocin kasar.

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tsaro, Nuhu Ribadu ya jagoranci tawagar Najeriya yayin da Allison Houker ta jagoranci tawagar Amurka domin a sake lalubo hanyoyin kawar da taaddanci.

Kasashen biyu za su tattauna hanyoyin karfafa hadin gwiwar tsaro da yaki da ta’addanci a wannan taro a Washington DC, kuma wannan ba shi ne karon farko na irin wannan ganawa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng