MURIC Ta Zargi INEC da Tilastawa Mata Tube Hijabi a Zaben Osun

MURIC Ta Zargi INEC da Tilastawa Mata Tube Hijabi a Zaben Osun

  • Kungiyar MURIC ta zargi INEC da hana dubban mata Musulmi masu sanye da hijabi kada kuri’a a zaben gwamnan Osun da aka gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026
  • Kungiyar ta nemi a cire Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, daga mukaminsa, tana zarginsa da gazawa wajen tabbatar da ’yancin addini a lokacin zabe
  • MURIC ta gargadi gwamnatin tarayya kan yiwuwar sake tauye hakkin masu zabe Musulmi a babban zaben 2027 idan ba a dauki mataki kan lamarin ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun - Kungiya mai fafutukar kare hakkin Musulmi ta MURIC ta zargi Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da hana dubban mata Musulmi masu sanye da hijabi kada kuri’a a zaben gwamnan Jihar Osun.

Kara karanta wannan

'Ina N4tr suka shiga"? Atiku ya kalubalanci Tinubu kan farfado da matatun mai

Daraktan kungiyar na kasa, Farfesa Ishaq Akintola, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 16 ga Agusta, 2026.

INEC ta fusata MURIC
Shugaban hukumar INEC ta kasa, Joas Amupitan a Ofis Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

BBC Hausa ta kawo labarin cewa da ya ke bayyana damuwarsa, Akintola ya ce lamarin ya faru a wurare da dama kuma an yi wa matan hakan ne da gangan.

MURIC ta damu da matakin INEC

Sahara Reporters ta kawo labarin cewa Akintola ya zargi INEC da hana matan kada kuri'a saboda kawai su Musulmi ne masu sanye da hijabi

ce:

“An hana dubban mata Musulmi da suka sanya hijabi kada kuri’a a zaben gwamnan Osun da aka gudanar jiya, 15 ga Agusta, 2026. Lamarin ya yadu sosai. An yi hakan ne ta hanyar tilastawa, wulakanci da kuma hana su damar kada kuri’a.”

Ya kuma yi zargin cewa wasu daga cikin matan da ba su da karfin yin adawa da matakin, an bar su suka kada kuri’a ne bayan sun cire hijabinsu.

MURIC ta nemi a cire shugaban INEC

Kungiyar ta mayar da hankali kan Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, inda ta zarge shi da gazawa wajen horas da ma’aikatan zabe da na wucin gadi kan batun ’yancin addini.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Muhimman abubuwa 8 da ya kamata kowane mai katin zabe ya sani

Ana zargin jami'an INEC sun rika tilastawa mata cire hijabi kafin su yi zabe
Taswirar jihar Osun inda aka zabi Ademola Adeleke Hoto: Legit.ng
Source: Original

MURIC ta sake jaddada bukatarta ta a cire Amupitan daga shugabancin INEC, tana mai cewa abin da ta kira tsoratarwa da wulakanta mata masu hijabi a zaben Osun ya yi tasiri kai tsaye kan sakamakon zaben.

A kalaman shugaban:

“MURIC ta sake jaddada kiranta na a cire Farfesa Joash Amupitan daga shugabancin INEC. Muna da ra’ayin cewa tsoratar da mata Musulmi masu hijabi a zaben jiya a Jihar Osun ya yi tasiri kai tsaye kan sakamakon zaben."

Kungiyar ta kuma ce tana da hoton bidiyo na akalla wata mace mai hijabi da ta dauki lokacin da aka hana ta kada kuri’a saboda irin tufafin da ta saka.

Zargin MURIC kan gwamnatin Sokoto

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kare hakkin Musulmin Najeriya, MURIC ta yi zargin cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu na shirin tsige Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III.

Shugaban MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi wannan zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, 24 ga watan Yunin 2024 inda ya gargaɗi gwamnan da ya guji wargi da kujerar Sarkin Musulmin.

Kungiyar MURIC na shawartar gwamnan da ya yi taka tsan-tsan. Kujerar Sarkin Musulmi ba kawai ta gargajiya ba ce. Kujera ce ta addini saboda haka ta guji duk wani da zai jawo sabani a kan batun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng