Tinubu Ya Tsallake Kansa, Buhari da Yar'adua, Ya Fadi Shugaban da Ya Fi Amfanar Najeriya

Tinubu Ya Tsallake Kansa, Buhari da Yar'adua, Ya Fadi Shugaban da Ya Fi Amfanar Najeriya

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), murnar cika shekaru 85
  • Tinubu ya ce Babangida ya yi wa Najeriya ayyuka masu matukar tasiri ta hanyoyin da babu wani shugaba da ya taɓa yin hakan
  • Shugaban ya bayyana tsohon shugaban sojan a matsayin fitaccen jagora wanda ya bayar da gagarumar gudunmawa ga ci gaban ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya dattijon ƙasa kuma tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), murnar cika shekaru 85 da haihuwa.

Shugaba Tinubu ya bayyana tsohon shugaban a matsayin wanda ya yi wa Najeriya ayyuka masu tasiri ta hanyoyin da babu wani shugaban kasa da ya taɓa yi.

Tinubu da Babangida.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu tare da Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya) Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaban ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai da dabaru, ya fitar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto .

Kara karanta wannan

IBB ya fadi wadanda ke taimakawa juyin mulki ke yin nasara a Najeriya

Sakon da Tinubu ya aika wa IBB

Tinubu ya kuma bayyana Janar Babangida a matsayin fitaccen shugaba wanda ƙwarewarsa a aikin soja ta kai ga zama shugaban ƙasar bayan juyin mulkin da aka yi a shekarar 1985.

Shugaban ya ce:

“Ko kuna son sa ko ba ku son sa, tsohon Shugaba Babangida ya yi wa Najeriya tasiri ta hanyoyin da babu wani shugaba da ya taɓa yi. Mulkinsa na tsawon shekaru takwas ya bar abubuwa masu dorewa a fannonin siyasa, tattalin arziki da kuma tsarin ƙasa.
“Ya bunƙasa tattalin arzikin ƙasar, ya samar da ababen more rayuwa masu ɗorewa, sannan ya kafa hukumomi da cibiyoyi da dama waɗanda har yanzu suke ci gaba da yi wa muradun ƙasa hidima.
"Ba don hangen nesansa, hikimarsa da kuma fahimtarsa kan daidaito da adalci ba, da akwai yiwuwar wasu jihohin tarayya da dama ba su wanzu a yau.”

Kara karanta wannan

Shugaba Paul Biya na Kamaru ya yi batan dabo, wata 2 ba a gan shi ba

Tinubu ya jinjina wa Babangida

Tinubu ya ce sunan Janar Babangida da gudunmawarsa za su ci gaba da kasancewa a tarihi saboda irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Najeriya.

Shugaban ya ce ko bayan ritayarsa, yayin da yake rayuwa cikin kwanciyar hankali a gidansa da ke Minna Hilltop a Jihar Neja, Janar Babangida na ci gaba da bai wa ƙasa shawarwari masu amfani da jagoranci.

“Shawarwarinsa da hikimarsa na ci gaba da zama abin ƙarfafa wa matasa gwiwa,” in ji Bola Tinubu.
Babangida.
Tsohon shugaban Najeriya karkashin mulkin soja, Jamar Ibrahim Badamasi Babagida Hoto: Muhammed Umaru Bago
Source: Twitter

A rahoton Vanguard, Tinubu ya ƙara da cewa:

“Ina yi maka fatan samun ci gaba da falala, ƙoshin lafiya da sabon ƙarfi. Allah Maɗaukakin Sarki ya bar ka tare da mu na tsawon shekaru masu yawa masu zuwa.”

Tinubu ya taya Gwamna Adeleke murna

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya Gwamna Ademola Adeleke murnar samun nasara a zaben gwamnan jihar Osun na 2026.

Tinubu ya ce sake zaɓar Adeleke wata alama ce da ke nuna cewa dimokuraɗiyya za ta ci gaba da bunƙasa a Najeriya ƙarƙashin mulkin jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262