Zargin Badakalar Gbajabiamila: NDC Ta Mika Bukata ga Tinubu da EFCC
- Jam'iyyar NDC ta bukaci tofa albarkin bakinta a kan badakalar da ake zargin shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, Femi Gbajabiamila da aikata wa
- Daga cikin abubuwan da NDC ta bukata akwai sauke Femi Gbajabiamila daga mukaminsa domin ba da damar gudanar da bincike mai zaman kansa
- Haka kuma jam'iyyar ta ce zarge-zargen da Prince Mathew Adeniyi Adeyemi ya yi sun tayar da tambayoyi kan kasafin kuɗi, asusun CBN da daukar ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. FCT Abuja – Jam'iyyar NDC ta bukaci a gaggauta sauke Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, daga mukaminsa.
Jam'iyyar ta bayyana cewa hakan zai bayar ba da damar gudanar da bincike mai zaman kansa kan zarge-zargen da suka shafi zargin samar da hukumar PFIPC.

Kara karanta wannan
"Bai shafi shari'armu ba": Nafi'u Bala ya yi magana kan hukuncin halasta David Mark

Source: Twitter
Wannan na kunshe a cikin wata sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 3 ga Yulin 2026 wacce Sakataren Yaɗa Labarai na ƙasa na jam'iyyar, Osa Director, ya sanya wa hannu, kuma aka wallafa a shafin X.
NDC ta yi magana a kan PFIPC
A cikin sanarwar, NDC ta ce ta damu matuƙa da zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka haɗa sunan Gbajabiamila da Prince Mathew Adeniyi Adeyemi, wanda ke ikirarin shi ne Darakta Janar na hukumar PFIPC.
Jam'iyyar ta yi zargin cewa an yi amfani da hukumar bogin wajen karkatar da kuɗin jama'a, tare da zargin cewa hakan ya faru ne da haɗin gwiwa da taimakon Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa.
NDC ta ce zarge-zargen Adeyemi sun nuna cewa PFIPC ta samu kasafi a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, sannan ta buɗe asusun har uku a Babban Bankin Najeriya (CBN) da sunanta.
Jam'iyyar ta ce abin mamaki ne yadda wata hukuma da Fadar Shugaban Ƙasa ta ce babu ita za ta iya buɗe irin waɗannan manyan asusu a CBN, inda ta tambayi ko Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya sarrafa wasu takardu na bogi wajen aiwatar da hakan.
NDC ta mika bukata ga EFCC ICPC
Har ila yau, NDC ta nuna damuwa kan zargin cewa Shugaban Ma'aikatan Gwamnatin Tarayya ya amince da samar da guraben aiki 314 ga hukumar PFIPC, duk da cewa gwamnati ta musanta samuwarta.

Source: Twitter
Jam'iyyar ta kuma yi nuni da zargin da Adeyemi ya yi cewa Gbajabiamila ya nemi kaso 48 cikin 100 na kuɗin fara aikin hukumar, wanda ya kai N27,395,510,136 duk da an musanta zargin.
NDC ta ce Adeyemi ya yi ikirarin cewa ya samu naɗinsa ne bayan ya biya Naira miliyan 600, daga ciki har da Naira miliyan 400 da aka ce an biya ta hannun wasu mutane, yayin da ragowar Naira miliyan 200 ba a kammala biya ba.
Jam'iyyar ta bukaci hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa na EFCC da ICPC da rundunar yan sanda da su zurfafa bincike a kan zargin.
Ana rade-radin Ganduje zai hada kai da NDC

Kara karanta wannan
Yadda gwamnatin Tinubu ta amince a dauki ma'aikata 300 a hukumar da ake cece kuce
A baya, kun samu labarin cewa an fara yada jita-jita marasa tushe da ke bayyana cewa akwai yiwuwar tsohon shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya fice daga jam'iyyar APC.
Abin da ya fi ban mamakin shi ne rade-radin cewa tsohon gwamnan zai hadu da Rabiu Musa Kwankwaso a NDC, kamar yadda wani tsohon kwamishina a jihar Kano ya bayyana cewa an hango.
Tsohon kwamishinan wanda ya yi aiki a gwamnatin Ganduje, Muaz Magaji yana cikin wadanda suke kara yada wannan jita-jita, kuma ya kara da cewa idan hakan ta tabbata, karshen siyasar tsohonshugaban APC ya zo.
Asali: Legit.ng
