'Hanya 1 Tilo da Za a Iya Yin Magudin Zabe a Shekarar 2027'
- Osita Chidoka ya ce zai yi wuya a tafka magudi a zaben 2027 idan INEC ta gudanar da shi kamar zaben gwamnan Osun
- Tsohon ministan sufurin jiragen sama ya bayyana cewa ya kamata 'yan siyasa su daina magudin zabe domin ya zama tsohon yayi
- Chidoka ya yaba da yadda fasahar zamani da AI suka taimaka wajen bibiyar sakamakon zaben Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Osita Chidoka, ya ce zai yi wuya a tafka magudi a babban zaben 2027 idan Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar da shi kamar yadda aka gudanar da zaben gwamnan jihar Osun da aka kammala.
Chidoka, wanda shi ne shugaba na cibiyar Athena Centre mai zaman kanta da ba ta da alaka da wata jam’iyyar siyasa, ya ce hanya daya tilo da za a iya yin magudi a zaben 2027 ita ce rashin gudanar da zaben.

Source: Facebook
Chidoka ya magantu kan zaben 2027
Chidoka ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels Tv ranar Litinin, 17 ga watan Agustan 2026.
“Hanya daya tilo ta yin magudi a zaben 2027 ita ce kada a gudanar da zaben."
“Idan aka gudanar da shi da wannan tsarin na Osun, da karfe bakwai mu a Athena Centre za mu rika ba ku sakamako daga jiha zuwa jiha, adadin wadanda aka dora da kuma maki da aka samu. Za mu gaya muku hakan."
“Ko da sun ce babu wata fasaha da za ta yi aiki a wannan rana, za mu yi amfani da tsarin hannu. Za mu sanya mutane sama da 5,000 a gundumomi 8,000 na Najeriya, mu rika sauke sakamakon, saboda abin da Najeriya ke bukata shi ne ta matsa gaba.” In jo shi.
Ya ce yin magudin zabe ya zama tsohon tsari, yana kira ga shugabannin Najeriya da su yi watsi da wannan dabi’a.

Kara karanta wannan
Bayan shan kashi a Osun, shugaban matasan APC ya ba jam'iyyar mafita kan zaben 2027
Ya ce an daina yayin magudin zabe
“Ya kamata mu fita daga wannan, ya kamata mu dakatar da wannan. Magudin zabe ya tsufa, ba abu ne da wani shugaba ya kamata ya yi ba. Shin ba sa jin kunya idan suka hadu da sauran shugabannin duniya, su zo da wa’adin mulki da aka samu ta hanya mara kyau? A’a, an daina yayin wannan." In ji shi
Chidoka ya tuna yadda kungiyoyin sa ido kan zabe suka iya tattara sakamakon zaben gwamnan Osun, yana mai cewa za a iya yin irin hakan a 2027 idan INEC ta bar shafin IReV ya yi aiki kamar yadda ya yi yayin zaben. Ya ce wadanda ke shirin tafka magudi ba su san cewa duniya ta ci gaba ba.
“Su (wadanda suke son yin magudi) suna zaune suna jira, ba su san cewa duniya ta ci gaba ba. YIAGA ta riga ta fara tattara sakamakon, Athena Centre ta riga ta fara tattara sakamakon, Dataphyte ma ta riga ta fara tattara sakamakon."
“Saboda haka, mun san alkaluman kowace gunduma da kowace rumfar zabe. Kuma ku san me? Za mu yi hakan a zaben 2027.” In ji shi.

Source: Facebook
Adeleke ya lashe zaben gwamnan Osun
A wani labarin kuma, kun ji cewa Hukumar INEC ta sanar da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na shekarar 2026.
Gwamna Adeleke ya samu nasarar ne bayan lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Bola Oyebamiji, da tazarar fiye da kuri'u 60,000.
Asali: Legit.ng

