An Turo Tallafin Sama da Fan Miliyan 2 daga Nahiyar Turai zuwa Najeriya da Wasu Kasashe 3
- Kungiyar Tarayyar Turai ta ware €2.3m domin tallafa wa Najeriya, Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Chadi wajen yaƙi da annobar kwalara
- Najeriya za ta samu €1.5m domin ƙara yawan ƙungiyoyin ba da agaji, samar da kayayyakin yaƙi da kwalara da inganta tsaftar ruwa
- WHO ta ce an samu fiye da mutane 61,000 da suka kamu da kwalara a Afirka cikin watanni biyar na farko na 2026
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kungiyar Tarayyar Turai ta ware €2.3m a matsayin tallafin gaggawa ga Najeriya, Kamaru, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da Chadi domin tunkarar annobar kwalara da ke ci gaba da yaɗuwa.
Wakilan kungiyar EU a Najeriya da Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ne suka bayyana hakan a wata sanarwa da suka fitar ranar Litinin.

Source: Twitter
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), an samu rahoton sama da mutane 61,000 da suka kamu da kwalara a yankin Afirka cikin watanni biyar na farkon 2026, kamar yadda The Cable ta ruwaito.
Tallafin da Najeirya za ta samu
Tarayyar Turai ta ce za ta ware €1.5m ga Najeriya domin ƙara yawan ƙungiyoyin da ke ba da agajin gaggawa, samar da muhimman kayayyaki kamar kayan yaƙi da kwalara, da kuma tallafa wa ayyukan samar da ruwa, tsafta da kiwon lafiya.
Tallafin zai kuma taimaka wajen kula da wuraren samar da ruwan sha na jama’a da na gidaje.
Sanarwar ta ce kuɗin zai taimaka wajen ƙara sa ido kan yaɗuwar cutar a wuraren da ba a iya isa gare su cikin sauƙi, da ƙarfafa kula da masu fama da cutar, yaɗa bayanai kan haɗarin cutar da wayar da kan al’umma.
Tallafin tarayyar Turai ga Kamaru
Sanarwar ta ce za a ware €100,000 ga Kamaru domin taimakawa wajen dakile barkewar cutar da kuma kula da marasa lafiya.
Tallafin zai haɗa da samar da ƙarin ma’aikata ga abokan hulɗar jin ƙai da ke aiki a ƙasar, magunguna masu muhimmanci, ƙarin cibiyoyin kula da masu fama da kwalara da wuraren ba da ruwan maganin bushewar jiki a ƙauyukan da cutar ta fi shafa.
A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kuwa, za a ware €500,000 domin faɗaɗa ayyukan kula da marasa lafiya da yin allurar rigakafi, da kuma ayyukan samar da ruwa, tsafta da kiwon lafiya.

Source: Getty Images
Kasar Chadi za ta samu €200,000
A Chadi, Tarayyar Turai za ta ware €200,000 domin taimakawa wajen katse yaɗuwar kwalara ta hanyar inganta samun ruwa, tsafta da kiwon lafiya.
Tallafin zai kuma ƙarfafa taimakon al’umma wajen sa ido kan cutar da kula da masu fama da ita, kamar yadda tashar Channels tv ta ruwaito.
China za ta ba Najeriya N40bn
Kun ji cewa gwamnatin China ta yi alkawarin bai wa Najeriya tallafin yuan miliyan 200, wanda ya haura Naira biliyan 40 domin taimakawa kasar wajen aiwatar da wasu ayyukan ci gaba ga jama'arta.
An bayyana hakan ne yayin da Jakadan China a Najeriya, Yu Dunhai, ya gana dabBabban Sakataren Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, Dr Ahmed Dunoma a Abuja.
Asali: Legit.ng

