NDC: Jam'iyyar Su Kwankwaso Ta Shirya Hadaka da Sauran 'Yan Adawa
- Babban jagoran NDC a Najeriya, Sanata Seriake Dickson, ya ce jam'iyyar a shirye take ta tattauna da sauran jam'iyyun adawa game da hadaka
- Dickson ya ce NDC na maraba da haɗakar da za a yi d za ta kai ga goyon bayan 'yan takararta, amma ya jaddada cewa ba a fara tattaunawa ba
- Jigon jam'iyyar ya yi tir neman soke rajistar NDC da aka yi, yana cewa jam'iyyar ta cika dukkan sharuɗan da hukumar INEC ke bukata a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Jigon jam'iyyar NDC, Sanata Seriake Dickson, ya sake jaddada cewa jam'iyyar a shirye take ta shiga tattaunawar haɗaka da sauran jam'iyyun adawa gabanin babban zaɓen 2027.
Ya yi magana yana mai bayyana fata cewa irin wannan tattaunawa za ta haifar da haɗin kai wajen mara wa 'yan takarar NDC baya.

Source: Facebook
NDC ta shirya hadaka a 2027
Dickson ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Sunday Politics na tashar Channels Television, lokacin da yake amsa tambayoyi.
An masa tambaya ne kan ko NDC za ta yi aiki tare da sauran shugabannin jam'iyyun adawa, ciki har da jam'iyyar ADC da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
A cewarsa, NDC na ci gaba da jajircewa wajen tattaunawa da jam'iyyun siyasa masu irin wannan manufa, amma ya jaddada cewa bai kamata a yi hasashe kan sakamakon tattaunawar ba kafin ta fara a hukumance.
The Sun ta rahoto ya ce:
“A matsayinmu na shugabannin adawa, jam'iyyarmu za ta ci gaba da kasancewa a buɗe ga tattaunawa a wannan fanni.
"Ba ni ba ne ko wani da zai iya yanke hukunci tun kafin a fara waɗannan tattaunawar. Muna fatan duk wata tattaunawa da za a yi za ta kai ga goyon bayan 'yan takarar NDC saboda mun san ingancin mutanen da muka tsayar,”

Source: Twitter
'NDC ba ta fi kowa ba,' Dickson
Dickson Ya ƙara da cewa jam'iyyar NDC ba ta ɗauki kanta a matsayin wadda ta fi sauran ba, yana mai cewa ana sa ran za a fara tattaunawa mai zurfi bayan dukkan jam'iyyu sun kammala zaɓen 'yan takararsu.
“Ba ma cewa mun fi kowa. Da zarar an kammala zaɓen 'yan takara, za a shiga wani sabon mataki na tattaunawa. Ko tattaunawar za ta kai ga cimma yarjejeniya, lokaci ne zai nuna, amma kofar mu a buɗe take,”
In ji Dickson.
Kalaman nasa na zuwa ne yayin da jam'iyyun adawa ke ci gaba da ƙoƙarin ƙulla ƙawance mai ƙarfi kafin zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
NDC ta ce Tinubu zai fadi
A wani labarin, mun kawo muku cewa jagoran NDC a Najeriya, Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu zai fadi a 2027.
A wata hira da ya yi game da siyasar 2027, dan siyasar ya sanar da cewa 'yan Najeriya sun kosa da irin salon mulkin Tinubu saboda haka za su kifar da shi.
Ya kara da cewa babban abin da ake bukata wajen kifar da Bola Tinubu a 2027 shi ne gudanar da zabe na gaskiya da adalci a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng

